WACECE NI??? CHAPTER TWENTY-THREE BY CUTYFANTASIA

195 16 6
                                    

Duk wata dauriya da kokarin da Ihman take da su sai da tattaro su waje ďaya ta qara da wasu ma kafin ta iya masking ďin fuskarta da fuskar da su Inna suka tafi suka bar ta da ita, duk da haka bata yarda ta zauna cikin su ba tace kanta ciwo yake yi zata je ta kwanta. Inna ta dube ta tace

"Gobe fa zamu je Kano Ihman, kuma da Hamman ku zamu tafi kinsan kuma shi ďan sammako ne baya son jira don haka kada ki koma bacci"

A nutse Ihman tace

"Inna bazan je ba! Zamu yi sallama da su daga baya, ko a waya ne"

Inna tace

"Da Hajiyan za ki yi sallama a waya Ihman?"

Cikin bacin rai tace

"Inna I hate anything that has to do with Kano (Inna na tsani duk wani abinda ya shafi Kano)

Inna zata yi magana kenan Hamman ya shigo da ledoji a hannunsa. Farida da Ihman suka tashi suka karbe shi suna yi masa sannu da zuwa.......

Waje ya samu ya zauna sannan ya dubi Inna yace

"Inna tunda bata son zuwa ki rabu da ita! taje wajen Zainab kafin mu dawo, ko a waya ai zasu iya sallama"

Wani sanyi ne ya ratsa Ihman domin ta tsani Kano kamar yanda ta tsani mutuwarta, duk wani tashin hankali da qaddarar da ke bibiyarta idan tayi tracing daga Kano yake, sannan ko sunan Kano taji sai ya tuna mata da Faris!
Mutum guda ďaya wanda ya mamaye birnin zuciyar ta bai bar space ko qanqani ba, bata taba yin so ba sai a kansa kuma ta tabbatar ba zata sake samun wanda zata so ko rabin soyayyar da take masa ba.
Tana son Faris so mai tsanani, irin soyayyar da take jin zata iya zama da shi a kowanne hali a kowanne yanayi na rayuwa komai wuya komai runtsi kuma zata iya fuskantar kowanne irin qalubale akan auren shi. Abinda ya faru a tsakanin su ya bata mata rai, amma har yau ta kasa yarda cewa Faris yana sane ya guje ta ya karya alkawarin da yayi mata ya fasa aurenta, ta tabbatar akwai wani abu wanda ya shigo masa mai matukar girman da ya shanye mi shi kai! She truly believes soyayyar da yake mata ta gaskiya ce, kuma wani dalili wanda zai futo daga gare ta ba zai sa ya sauya ra'ayin shi ba.
Duk tsayin wannan lokacin bata taba addu'a bata sa sunan shi ba, bata taba yin awa ďaya bata tuna shi ba, bata taba kwana ba da begen shi ba. Wani lokacin ta kan ji kamar ta futo da zuciyar ta ta cire sashen da soyayyarsa take ta cillar ko ta samu sassaucin abinda take ji.
Wani lokacin ta kan kwana tana kuka, ko kuma playing call recordings ďin su wanda tayi saving a cikin wayarta.
It's not easy at all, ita shaida ce babu abinda ya kai soyayya cin rai da hana sukuni da gallazawa zuciya, ko abinda ya faru da ita bai kai Faris zama a cikin ran ta ba, soyayyar shi a jininta take, kuma tayi ihmani da ita zata koma ga Allah.

Bayan ta kammala komai na rayuwarta ne ta saka mukulli ta kulle kofarta domin kar wani ya shigo mata! Ta haye saman gado da littafin da take jin kamar yafi komai muhimmanci a rayuwarta a wannan halin ta zauna, jikinta gabaďaya rawa yake yi saboda tsoro da fargabar abinda zata karanto, bata sani ba ko ta haďu da heartbreak ďin da yafi wanda ta gani. Sai da ta haďo dukkan courage ďin da take da shi sannan ta buďe littafin ta soma karantawa dalla dalla, line by line, page by page.

Tun daga shafi na biyu idanunta suka soma kwaranyar da ruwan ruwa, hawaye na ambaliya akan fuskarta domin labarin Innan yayi matukar shammatar ta, ko kusa bai zo dai dai da yanda take hasashe ba, ji take yi kamar almara, kamar hikaya take karantawa ba abinda ya faru a gaske ba.........
A lokacin da tazo tsakiyar wani page ne ta saki littafin akan gado zuciyarta tayi wani irin zillo ta buga da karfin gaske, abinda taji a wannan lokacin yafi karfin kwatantawa domin ta ďauka zuciyarta ce za ta tarwatse ta buga ta kwanta ta mutu, cikin ďimuwa da wani irin tashin hankali kwakwalwarta take rewinding abinda ta karanta ďin kowacce kalma tana rigging a kwanyarta kamar ana kaďa kararrawa

wacece ni?Where stories live. Discover now