WACECE NI??? CHAPTER TWENTY BY CUTYFANTASIA

225 11 0
                                    

Futowar Sadik daga dakin shi kenan da yammacin asabar cikin shigar Armani trouser da Valentino shirt fara mai bakin rubutu, kafarsa sanye da slippers din "Hermes" blue black sai qamshin signature turaren shi yake yi mai suna
"Kalemat".......
Iskar damunar da take kadawa yake zuka yana fesarwa cikin wani irin nishadin da ya tsinci kansa a ciki kwanan nan, jin shi yake yi kamar a saman gajimare, kamar an mi shi albishir! duk kuma ba wani dalilin ne ya janyo haka ba sai kusanci da shakuwar da ta sake kulluwa a tsakanin shi da Ihman wadda ta ninka ta da a kwanakin nan da ya dawo, for sure ya sani Ihman ba zata taba kin shi a matsayin mijin aure ba, he is ready for Aunty da duka tantrums din ta, kawai abinda yake jin tsoro ya kasa samun mafita akai shi ne yanda Ihman zata dauki maganar da kuma abinda sanin Abba ba mahaifinta bane zai haifar ga lafiya da kwanciyar hankalinta......
Ya san kome zata ji akan tsakaninta da Inna ba zai girgiza ta ba domin babu wata mu'amala mai dadi a tsakanin su idan ba yanzu ba so knowing itama Innan ba..........ya zuqi numfashi ya fesar yana shafa kai
Idan ba don haka ba, da tuni an wuce wajen amma duk da haka yana nan yana kokari kuma yana shirya komai a tsanaki, abinda yake so yanzu shine ya fara winning din zuciyar Ihman, ya saka mata soyayyar shi irin wadda zata runtse idanu ga kowanne irin kalubalen da zai mata katanga da auren shi. By then sai yayi tunanin taking next move din shi.

Da wannan tunanin ya isa cikin gida inda ya samu Inna a kitchen suna aikin abincin dare, sama sama suka gaisa duk da Innan tana hankalce da wani ladabin babu gaira babu dalili da ya tsuro mata da shi, tun can basa shiri da Sadik saboda Ihman kuma bakar zuciyar sa ta sa baya shiga sabgar ta amma kwanakin nan tun bayan dawowar shi ta ga ya sauya mata completely amma bilhaqqi tunaninta abinda ya kawo sauyin shi ne shiryawarta da Ihman da kusancin da suka samu tunda daman dalilin rashin jituwar tasu da shi kenan.

"Inna Ihman ta shirya?"

Ba tare da ta dago kanta daga kan shinkafar da take soyawa ba tace

"Lokacin da na sauko dai ta shiga wanka! Tura wani ya duba maka"

Sai ya shige cikin falon yana dialing number ta a wayarsa, ringing biyu ta dauka

"Are you ready?"

Cikin sanyin muryar ta tace

"Tun yaushe, kai nake jira"

"Will you do me a favour yau kada ki saka wannan dogon abun naki?"

Cikin yar dariya tace

"Wai me Jilbab dina yayi maka? Haka kawai ka saka musu karan tsana bayan kasan bani da kayan da ya wuce su?".

"Suna tuna mun abubuwan da bana son tunawa ne, kema kuma haka don dai kawai bakya son rabuwa da su ne"

"Ya Sadik idan na rabu da su nasa me"

"Akwai kaya masu yawa that are modest, ba sai lallai wadannan dogayen hijaban ba"

"Allah ko?"

"Idan mun futa zan nuna miki! Just try and and change what you wear I promise kema zaki ji chanjin a cikin zuciyarki"

Kamar fadar Allah take bin maganar Sadik domin bayan shi din babu wanda ya isa yayi comment akan suturarta ba'aji kansu ba, kowa yana da abinda yake kunno fushin sa, duk hakurin Ihman bata yarda kayi comment akan suturarta ko surar jikinta sau biyu ba, either positively or negatively ita bata so, she believes cewa kyawu guda daya ne kuma a hali da dabi'a yake, dukkan halittar Allah daga gare shi suke kuma Allah bai taba halittar mummuna ba, duk wata halitta da ka gani ra'ayin shi da hikimar shi da ganin damar shi ne ya sanya ya haliice ta a haka, ba wai don ya gaza ko ya kasa ba, hasalima Shi Allah bai duban halitta ko yare ko al'ada wannan inner halayyar da tsarkin zuciya yake kallo, ya kuma fada cewa wanda yafi kusanci da shi shine wanda yafi tsoron shi toh don haka ita a ganinta rashin tauhidi da kalubalantar mahalicci ne kaga wata halitta kace bata da kyau ko bata yi dai dai ba, tunda komai munin ta wani dan'adan bai isa ta kera ya busa mata numfashi ba. Ubangijin nan dai da yayi masu kyau shi yayi munana kuma bai fifita wani akan wani ba sai wanda yafi kusanta kan shi da Shi.

wacece ni?Where stories live. Discover now