Cikin ikon Allah Ihman ta farfado ta samu kanta, kuma darajar addu'a babu abinda ya faru da ita, bayan kwakwkwaran bincike likitoci sun tabbatar abinda yake cikinta ma yana nan cikin koshin lafiya, shock ne kawai da rudewa suka haifar mata da wannan matsalar. Tunda ta tashi take kuka, ita lallai gida zata tafi kuma a ranar take so a saka ta cikin jirgi a mayar da ita gida ke ba zaki ce ita ta dauko kafafunta ta taho da kanta ba, ganin abun yana neman yawa Aunt Halima ta saka aka yi mata allurar bacci domin ta huta su ma su huta da tension din da suke ciki.
Bayan tayi bacci Aunt Haliman ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kyakykyawar fuskarta, wata irin soyayya da kaunar ta tana tsirgawa cikin zuciyarta. Duk cikin yan'uwanta babu wanda Allah ya hada jininsu kamar Sa'id, da shi suke kashewa su binne tun suna yara, da shi take shawara kuma ita kadai yake zuwa kai tsaye ya bayyanawa sirrin zuciyarsa. Ita ta san farin sa da bakin sa da halayen sa, ita tafi kowa sanin damuwarsa da fadi tashin sa don haka duk wani abinda ya shafe shi yana da matukar muhimmanci a wajen ta.
.....................................................................................
THREE DAYS LEAP
Hamma ne ya je Airport ya dauko Abba, Adda Wasila da Farida a yammacin, duk da cewa ya riga ya kamawa Abba masauki, bai wuce da shi can din ba suka zarto unguwar Diso gidansu Inna. Ba wani abu bane ya tattago shi kuwa illa babbar maganar da ta taso daga bakin jami'an bincike cewa Ihman tana kasar Ghana, Hamma bai tunkari kowa da maganar ba sai Inna, saboda alamu da yawa da suke alakanta tafiyar Ihman da Innan da kuma yanda ita Ihman din ta tafi kasar Ghana kai tsaye wanda ya tabbatar cewa, da niyyar zuwa wajen wani ko wata ta tafi da kuma taimakon wani information da ta samu a bakin wani ko wata take amfani don haka ya koma asibiti wajen Inna ya gurfana a gabanta cikin tsananin rauni ya dinga yi mata magiya ta gaya mi shi waye Ihman zata iya zuwa wajen shi ko wajen ta a kasar Ghana??Shock din da Inna ta shiga kadai ya tabbatar masa da cewa akwai wani boyayyen sirri wanda ko shi bai sani ba, wanda Abba bai sani ba, wanda dukansu basu sani ba, wannan sirrin ne kuma Ihman ta bankado ta samu courage din tafiya Ghana saboda shi kai tsaye. Tunda Inna ta fara kuka bata sarara ba, kuka magigici mai daga hankali, kukan da Hamma zai ce tunda Ya taso bai taba ganin tayi irin sa ba ko lokacin mutuwar mahaifinta.
Babu yanda basu yi da ita ta fadi abinda yake cikin ranta ba taki, babu wanda bai mata magana ba idan aka cire Hajiyar Kano wadda gabadaya jikinta yayi sanyi, ko magana ta kasa, kuma ko hada idanu da Innan bata yi which clearly means itama ta san inda batun ya dosa. Sai Hamma ya dauki waya ya kira Abba for the first time bayan tahowarsu"Hello Abba barka da rana"
"Muhammadul Quraish! Ka huce da Abban ne?"
"Abba ni na isa nayi fushi da kai?"
"Gashi kuwa ka dauki babarka kayi mun yaji ko waya ban samu arziki ba"
"Kayi hakuri Abba, ba fushi nake yi ba! Hanyar da zan bi na gyara alakar da tafi kowacce muhimmanci a rayuwata nake tunani! Zamanku lafiya da Inna shi ne biggest strength dina Abba, tun ranar da ka ambaci ta bar maka gida na rasa duk wani kuzari da karfin guiwar da nake tunanin ina da shi......"
Kawai sai yasa wa Abba kuka, kukan da ya galabaitar da Abban ya saka mi shi wata irin saduda da nadama da tausayin da kullum yake haqa rami cikin zuciyar shi yana binnewa a game da alakar Hamma da Innan! Cikin dauriya yace
"Haba Quraishi! Ba'a san jarumi da kuka ba"
"Abba ni din ba jarumi bane a wannan fannin nafi kowa ragwantaka! Ba zan iya jure ganin iyayena sun raba inuwa ba, bazan jure ganin tarwatsewar ahalina ba! I'm not that strong"
Cikin dishewar murya Abba yace
"Me kake so nayi yanzu Quraishi?"
Kamar wani yaro ya furzo maganar cikin kuka
VOCÊ ESTÁ LENDO
wacece ni?
Ficção GeralWacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban m...