WACECE NI ELEVEN

231 14 1
                                    

13-3-21015
Indoor stadium kofar mata,
Kano state.

Rana bata qarya sai dai uwar diya taji kunya, ranar da su Ihman suka dibi watanni suna yi wa shiri da mugun burin gani ta cika, wajen taron ya cika dankam da manyan mutane da iyaye da malamai da dalibai.
Daga bangaren manyan baki da shugabannin taron akwai mai martaba da gwamna da kwamishinoni, chairmans, manyan yan siyasa da ginshaqiman masu kudi na kusa da manyan malamai da shehunai da alarammonin mahaddata da alkalai da alkalan alkalai babu wanda bai hallara ba........

Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali aka soma gudanar da musabaqar tun daga kan yan matakin farko har zuwa kan su Ihman da zasu yi masabaqar izu sittin, ta farko da aka kira yar jihar Sokoto ce, sannan aka kira Ihman, a lokacin da ta soma karatun ta wani irin shiru dakin taron ya dauka, tun daga kan amon sautin ta, zuwa kira'ar ta, tajweed din ta da uwa uba kwarewar karatun na ta sun hadu waje daya sun saukar da wani irin yanayi a gangar jiki da zukatan wadanda suke zaune a wannan waje mai albarka, muryarta mai tsananin taushi ce, mai sanyi, kuma me Maggi da gishiri har da onga, harshenta kar kar kuma tar tar yake  futar da kowanne harafi da wasalin sa da tajweedin sa, ga wata irin ilhama da kamewa a cikin muryar babu nervousness ko shakewar numfashi ko gudun sauti ko kadan, a nutse tayi karatun cikin kwanciyar hankali tiryan tiryan babu kuskunda ba komawa baya...

Babu mahalukin da karatun Ihman bai tafi da imanin shi ba, wasu tsuma suka dinga yi, wasu hawaye, wasu murmushi, wasu kuma kawai ayyanawa suke a ran su inama su zama Ihman ko kuma Ihman ta zama yarsu ko kanwarsu, wasu kuma jadadda irin baiwa da hazakarta suke da kuma uwa uba nutsuwar da ta mallaka da sauti mai matukar tsada.

Idan aka zauna rubuta yanda abubuwa suka wakana cikin wannan lokaci da wannan rana, toh za'a debi lokaci mai matukar yawa, Abinda kawai za'a ce shine anyi taro an gabatar da komai cikin tsari da ilmi kuma a karshe Ihman ta karbe wannan kambun da kowa yake hari yake muradi, wanda basa cikin gasar kuma suke zumudin ganin wanda zai dauka, a lokacin da alkalai da alkalin alkalai suka kammala yanke hukunci aka soma jawabin kiran sakamako da yanda gasar ta kaya, Ihman ko kadan hankalinta bai tashi kamar sauran daliban ba, ita ba burin ta bane wai tazo ta daya ko tafi kowa ba, burgewar ta kawai a datso mata aya a karanta farkonta ace taci gaba, kuma taci gaban ta kai har zuwa matsaya ba tare da kuskure ko inda inda ba, wannan shi yake tabbatar mata da cewa tilawarta tana kyau, kuma karatunta yana kwari. Toh shikenan fa burinta ya cika, babu wani farin cikin da take iya hadawa da wannan.

A dai dai lokacin da aka yi kiran sunan Ihman a matsayin gwazuwar shekara ta kasa, ilahirin yan gidansu a Gombe suna babban parlour a zaune gaban TV inda ake nuna taron musabaqar live a NTA.
Aunty ce kawai ba tayi zaman kallon ba saboda tsabar kiyayya da hassadar Ihman da ta saka a ranta.

Farida hawaye take yi tana yi wa Allah godiya, Inna kuwa kamar an kafe gunki a kan kujera haka ta koma, hannu bata daga ba, ido bata kifta ba sannan ko kalma bata tofa ba tunda suka fara kallon, sai wani zuzzurfan tunani da ta shiga mai matukar zurfi, duk hayaniya da murna da shewa da tsalle-tsallen da yaran suke yi a matsayin murna ga yar'uwarsu Inna bata tanka ba,
Har lokacin da mai martaba sarki ya mike ya soma jawabi, inda da kan shi ya nuna matukar yabawa da sha'awar daliba irin Ihman, yace ya dade bai ji karatun da ya shige shi irin na Ihman ba, yace yana jinjinawa iyayen Ihman da suka tsaya suka bata karfin guiwa da kulawa a fannin karatun ta har ta kawo wannan gaci, sannan yayi alkawarin daukar nauyin karatun Ihman a kowacce jami'a take da burin karatu a fadin duniya, sannan ya bada kujerun umra ga malaman Ihman, sauran daliban musabaqa kowanne ya samu kyautar kudi da tufafi, a karshe ya jawo hankalin iyaye akan su yi koyi da iyayen Ihman, su dinga jajircewa akan lamarin yayansu musamman masu son karatu, su tallafa musu su basu kwarin guiwa don ganin sun cimma burin su, domin ba karamun amfana al'umma zata yi da irin su ba.

Bayan mai martaba ya kammala jawabi ne wakilin gwamnati ya mike yayi na shi a madadin gwamna a dalilin uzurin da ya kama shi ya bar wajen kafin a tashi. Su Ihman sun samu kyaututtuka marasa adadi, kujerun makkah, kudi, suturu, da sauran abubuwa masu yawa.

wacece ni?Where stories live. Discover now