WA CECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE 3

403 24 2
                                    

Gabaďaya yaran gidan  kansu a haďe yake idan aka cire Adda Asma wadda suka soma futar da ita daga cikin su a dalilin rashin zamanta tare da su. Rashin kirkin Anty bai saka ýaýan Inna sun raina ta ko ýaýanta sun raina Inna ba, zumunci ne mai karfi a tsakanin su da kaunar juna don haka da wuya kaji tashin hankali a tsakanin yaran sai dai idan masifar Anty ta motsa tayi bala'in ta kan wanda tsautsayi ya faďa ma.

A cikin haka suka soma shirin bikin Ya Wasila, da Kamal ďan gidan Alhaji Almu abokin Abba da suka yi aiki a GT bank tare a garin Abuja. Su Abban ne suka haďa auren kuma aka yi sa'a basu yi gardama ba suka amince da juna, farin cikin hakan ya sanya iyayen yi wa bikin wani irin shiri musamman da yake shi ne karo na farko da zasu soma aurar da ýaýa duk su biyun.
Abba ya so Adda Asma ta kawo nata mijin a haďa su ta tubure ita bata shirya yin aure ba kamar yanda Anty ta tsara mata domin su burin su ta auri ďan gidan Hajiya Zaituna da ke zaune a America. Sai Abba ya shafawa kansa lafiya ya kyale su.

Hamma ne ya turo wa ýan kannen na shi kuďi suyi shirye shiryen buki, shima yaso halartar bukin kamar yanda Inna take tayi masa naci amma exams ta rike shi bai samu tahowa ba sai ďumbin hidimar sa da alkhairin sa ne suka ratsa account ďin kowa don haka kowa ya bi shi da addu'ar fatan alkhairi.

Yau ne ranar kamun Amarya wanda aka shirya a harabar gidan su, musamman aka dauko kwararru suka gyare tafkekiyar farfajiyar gidan aka jera kujeru da tebura kamar yanda akewa filin taron biki a manyan event centers, daga aljihun babban Yaya. Shi aka yi wa list din komai na biki ya turo kudi, tsinke Abba bai saya ba, toh daman da wani abu ne da shi mai yawa ba, ma'aikacin banki ne, sai dai duk abinda ya mallaka akan karatun yaran shi suka kare, yace bai damu ya mutu ya bar musu kadara ba, amma zai yi iya kokarinsa ya basu ilmi mai inganci wanda zasu rike kansu da shi ko bayan ran shi, don haka bayan yayi ritaya bai tsira da komai ba sai katon gidan da ya gina a federal low cost, sai bakery da ke Jeka da Fari. Tunda Hamma ya kama kasa ya dauke nauyin komai na gidansu on his shoulders, kowanne wata sai Abba yaji isashshen alert din da zai wadatar da su harkar gida, kuma duk abinda ya taso shi za'a gayawa kuma bai taba gazawa ko gajiyawa ba, he serve them cikin farin ciki da ladabtawa don haka yayi winning zuciyarsu gabadaya.

Karfe biyar dai dai alarm ckock ďakin Ihman ya kada, ta ďaga ido daga kwancen da take akan gadonta hawayen da ke malala akan kuncinta tayi  kokarin  gogewa sannan ta mike.A ranta ta gaza gane dalilin da yasa Inna take mata wannan yankan kauna. Abinda ya faru shine dakin Farida ta shiga ta sameta tana bude wasu takalma haďaďďu da purses da wasu saitin fashion na azurfa Ihman cikin murna tace
"ferry a ina kika samu wannan kayan?"

Farida ta amsa da cewa
"Inna ce mana kema kinsani...ke bata baki ba?"
Ihman tace
"noo ni banma shiga dakinta ba"

farida tace
"zata baki ne ai don cin biki ta siya mana"
daga nan Ihman ďakin Inna ta wuce ta sameta tana  haďawa su khalid kayan sawarsu da hula da takalmi waje daya a sanyaye ta nemi waje ta zauna sannan tace

"Inna naga kayan Farida masu kyau ina nawa?"

A nutse Inna ta kalleta face "ita kadai na siyawa ke ba kina da sabbi da yayanku ya aiko muku ba?"

A tunanin Ihman wasa Inna take don haka tai murmushi tace
"Inna kenan ai itama Farida tana da sabbin kaman nawa"

a faďace Inna ta shiga magana

"toh ita kadai na siyewa ya zanyi asarar kudi na siye miki bayan nasan kina  da shi? Ita Farida ba itace karama ba"

Wannan karon kasa daurewa Ihman tayi domin wani gululun bacin rai ne ya tokare zuciyarta ta soma zafi sai ta mike a hasale ta futa ta banko kofar ta koma ďakinta sai dai ko zama batai ba Inna ta shigo batai aune ba taji wani irin mari "tass" a gefen fuskarta na dama.
A sukwane ta zaro idanu tana dafe da kuncin muryarta na rawa tace

wacece ni?Where stories live. Discover now