Duk wata kulawar da me irin condition din Ihman take bukata an bata, likitoci biyu ne suka tsaya a kanta sukayi stabilizing na ta, an tsayar da bleeding din kuma sun samu ta dawo hayyacinta sun yi sedating dinta, kafin daga baya ayi binciken gano status din lafiyarta da ta babyn.
Sa'id na kwance idanun shi a rufe yana sauraron radadi da azabar da zuciya da ruhin shi suke masa, wani irin ciwo yake ji irin wanda ba zai iya misaltawa ba, danasanin aikin da ya aikata yana qara baibaye shi, ji yake kamar kowacce gaba a jikinsa la'antar sa take yi tana tsine masa! Gabadaya bai ga amfanin rayuwar sa ta baya ba balle wadda zai yi anan gaba, ya soma yin istigfari a hankali domin sabon da yake shirin barowa, ya dinga kiran sunan Allah cikin tsananin radadi da karyewar zuciya har bacci ya sake yin gaba da shi.
.....................................................................................
Tun da Hamma ya futo daga gidan Hajiya yake gararamba akan titi without knowing ina za shi? Me zai yi? Yaya zai yi? Ba.
He has never been this tensed and helpless in his life, ji yake yi kamar ya rufe idanu ya bude ace masa komai mafarki ne, kamar ya gudu daga wannan kasar ya koma wata duniyar wadda bai san kowa ba.
Shi dai bai dawo Nigeria da sa'a ba, lokacin da yake China hankalinsa a kwance, komai yana tafiya lafiya a gida, iyayensa suna zaune lafiya kamar zasu hadiye junan su, kannensa suna farin ciki da shi, dangi suna shi masa albarka, daga can bangaren sa komai is going smoothly, karatunsa, kasuwancinsa wanda yake gudanarwa acan da wanda yake nan gida Nigeria. He has lived the most comfortable and peaceful life in China, watakila Nigeria ce bata karbe shi ba, watakila kuma qaddarar shi ce haka.
Ba abinda yake karya mi shi zuciya yaji ya fara kukan da yafi komai yi mi shi wahala a rayuwa kamar ya tuna yanda Abba yayi wa Inna cin mutunci da tsantsar rashin tausayi a gaban yayanta, yace ta tattara awanni biyu kawai ya bata ta bar mi shi gida, kuma kada ta dauki ko yaro daya, a satin ya tursasa shi ya kai kannensa maza boarding a Abuja.
Farida da Zainab suna gidan Hamman, gidan dai ya rage daga Anty da iyalanta, sai Sadik wanda bai taba yini a gida ba tun ranar da aka wayi gari babu Ihman, ranar dan karamin hauka yayi musu a gidan don sai da ta kai Abba ya kira likita yayi masa allura kafin a samu a shawo kansa.
Daga wannan ne kuma likitan yake gayawa Abba cewa lallai akai Sadik asibitin kwakwalwa ayi masa cikakken bincike da diagnosis domin yana zargin shi da wani mental disorder da ake kira EID wato "Intermittent Explosive Disorder" a likitance!
Lokacin da yake yi wa Abba bayanin alamomin ciwon da halin da me ciwon yake tsintar kansa idan ciwon ya tashi sai yaji kamar da Sadik din likitan yake, hankalinsa ya tashi sosai, duk da cewa Dr Sha'aban ya kwantar masa hankali kuma jaddada nasa cewa babu matsala da izinin Allah zai samu sauki, kawai dai ya danganta da saurin da akayi wajen kai shi asibiti da nemar mi shi taimakon likita, sannan shi zargi yace yana yi bai tabbar ba, sai an kai shi gaban likita yayi diagonising din shi da ciwon tukunna.
Hamma yana ji yace a bari hankali ya kwanta a gama da maganar Ihman, shi zai dauki Sadik zuwa Germany da kansa kwararren likita ya duba shi ya bashi kulawar da ta dace. Ya kuma jaddadawa Abba cewa kada ya bari Sadik din yaji wannan maganar. Amma da yake Aunty butultacciyar mata ce, daga baya sai ta fara yi wa Inna sharrin tana jifan yayanta da asiri, wai ta gama da Asma'u ta raba ta da Abba, ta hana ta karatu ta hana ta aure, yanzu kuma daga dawowar Sadik din za ta sa mata shi a gaba.A gaban Abba tayi wannan furucin, kafin yayi magana Inna ta juyo tace
"Kowanne irin abu nayi miki komai munin sa na roki Allah ya saka mi ki akan yayana, idan kuma sharri kika yi mun na bar ki da ubangijin da ya halicce mu gabadaya"
Daga nan tayi parking din kayanta ta bar gidan zuciyarta kamar za ta fashe saboda tsananin bakin ciki da tashin hankali, Hamma ne ya dauketa zuwa gidansa da magiya da rarrashi domin itama tayi mugun fushi da Abban, dakyar ta kwana washegari ya saka ta a jirgi suka tafi Kano, sai dai suna zuwa gidan Hajiya wani mugun zazzabi da ciwon kirji ya kamata, ko hutawa basu yi ba suka dauketa zuwa asibiti, kawo wannan lokacin Inna tana kwance rigib cikin tsananin rashin lafiya, Hamma ko sau daya bai waiwayi gida ba, bai kuma kira Abba ba domin shi ma this time, yana bayan Innar shi ya daina zama neutral din da ya saba.
YOU ARE READING
wacece ni?
General FictionWacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban m...