WACECE NI??? BY CUTYFANTASIA PAGE 1

1K 37 2
                                    

Kiran sallar Assalatu ne ya farkar da ita daga guntun baccin da ya ďauke ta wajen karfe ukun dare a sakamakon zaman bin tilawar alquranin ta da tayi saboda jiya gabaďaya ba ta samu kanta ba sai lokacin kwanciya bacci.
Sai da ta karanto addu'ar tashi daga bacci sannan ta mike ta shiga toilet tayi alwala ta gabatar da raka'atanil fajr tayi jiran masallaci su tayar da sallah ta  bi jam'i.

Bayan ta idar tayi azkars ďin safen ta sai ta ninke kayan sallar ta cire pyjamas ďin jikinta ta ďaura towel ta shiga banďakin da ke manne a cikin ďakin. Mintina goma ta futo tana kamshin shower gel ďin "lavender"
Da ďan karamin towel a hannunta tana goge ruwan fuskar ta. Cikin nutsuwa ta kammala shafa mai ta saka fararen undies ďinta sannan ta shirya cikin kayan makarantar "Gombe High School" wanda suke ta faman ďaukar idon wanki da guga. Ta feshe jikinta da "floral perfume" (turaruka masu kamshin furanni) sannan ta ďauki ďan siririn agogon hannu na mata tana ďaurawa ta futo daga dakin na ta cikin sauri.

A matakalar bene suka ci karo da Ya Sadik ya dawo daga masallaci, domin yana zama ďaukan karatu bayan sallar asuba. Cikin ladabin da ya kasance na halitta a gareta ta gayar da shi ya amsa cikin jindaďin wannan girma da take ba shi da kuma soyayya irin ta jini mara sirki.

"Ihman sarkin sammako! Karfe 6:45 har kin kammala?"

Cikin murmushi tace

"Ya Sadik zan ta ya Inna aiki a kitchen shiyasa"

"God bless your effort!(Allah ya albarkaci kokarin ki).

Ta amsa da "Ameen"

Sannan ta ba shi hanya ya wuce corridor ďin da za ta sada shi da ďakin Aunty ita kuma ta sauka zuwa kitchen.
Inna tana tsaye gaban "worktop" ďin kitchen ďin tana firar sweet potato(dankalin hausa) kitchen ďin ya gauraye da kamshin sauce ďin cin dankalin.
Cikin ladabi ta durkusa ta gaishe da Inna

"Barka da safiya Inna antashi lafiya?"

Ba tare da ko kallon inda take ba ta amsa a dakile. Babu ko ďigon bacin rai a fuskar Ihman ta nufi shelve ta ďauko Apron ta ďaura akan kayanta ta soma taya Inna haďa karin kumallon safe wanda yafi kowanne aiki wahala a girkin gidan domin sai an fara yi wa yara abincin makaranta sannan ayi wa Abba tuwon laushi wanda yake ci kullum da safe, sannan karin kummalon gida gabaďaya.

Cikin zafin nama suka yi aikin suka kammala kowanne yaro aka shirya masa lunch box ďin sa aka ajiye a gafe.

Farida ce ta shigo kitchen ďin da sauri sanye cikin irin kayan ihman tana cewa "good morning Inna" murmushi innan tayi tace
"Maman Abbanta har kin gama?"

Ta sake murmushi tace na tashi inna jiya nayi bacci late ne na tsaya kallon wani film."
Inna ta iso dinning din ta aje tray din kyan shayi tana cewa " toh maza ga breakfast kuyi ku tafi kar ku makara"

Farida ta amsa da toh sannan ta dubi ihman da ke tsaye jiki a sanyaye tace
"bestie kin tashi lafiya?" Murmushi ta kirkiro tace "fine my dear wato karatun exams dinne ya koma kallon film ko? Zakiyi bayani" dariya farida tayi tana kurban tea sannan tace "am done with that bestie sai fatan nasara"

Nan suka zauna suka soma breakfast sauran yaran suka futo suka zauna tare  suma. Seven dot ya sadik ya futo yana oya oya ku taho. Duka suka yi sallama da Inna suka wuce gate inda bakar ciana ďin da ake kaisu makaranta ke fake.

Bayan sun dawo a kitchen suka sake samun Inna tana haďa salad kowa yayi mata sannu da gida suka haye sama kowacce ta nufi ďakinta ta watsa ruwa tai sallah suka sauya uniform zuwa na islamiyya sannan suka sauko kitchen ďin. Ihman ce take taimakawa Inna sukai serving kowa sannan ta zauna ta soma cin nata abincin. Suna gamawa mallam Ali ya daukesu zuwa islamiyya.
Yau kam farida sai da tasha bulalar rashin kawo hadda. Sai bayan malamin karbar haddar ya futa Ihman ta dubi farida tace
"kallo yayi miki kyau ferry! da kinsan baki yi hadda ba kika zauna kallon film ko?"
Ranta a bace tayi maganar. Farida cikin rashin damuwa tace "tunda dai na iya karatun nan naga haddar ba dole bace abinda ance in kayi ka bari ta zube kana da azaba"

wacece ni?Where stories live. Discover now