SHAFI NA ƊAYA

2.1K 179 6
                                    

   *GINI DA YAƁE*

*BILLY GALADANCHI*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
     *EWF*
  

*Wattpad@ 68billygaladanchi*

*Da sunan Allah mai Rahama mai jinƙai. Ina roƙon Allah ya sanya alkhairi da albarka acikin alƙalamin  dukkanin marubutan mu. Allah kasa mu rubuta dai-dai abinda yake kuskure ne Allah ka tsaremu da rubuta shi Ameen*

*Saƙon gaisuwa da fatan alkhairi agareku mutanen kirki, ina muku fatan Alkhairi. Ayusher Muh'd, Safiyya Huguma da aunty na Maijidda musa.Alkhairin Allah ya riskesu cikin amincin Allah aduk inda kuke.*

*Bazan Manta dake ba ƙawa kuma ƙanwata Hassana Ɗan Larabawa. Yanda kike ƙoƙari akan mu da wannan rubutun don ganin ci gabanmu, Allah ya saka da Alkhairi ina miki fata da nagari.*

*Gaisuwar ban girma agareki babbar ƙawata kuma mai yawan gayamun gaskia wato Ramlat R manga(Mai dambu) yanda kike ƙoƙari wurin ciyar da ƙungiya gaba Allah ya ciyar da zuri'arki agaba*

*Da taimakonki wannan ƙungiyar ta tsaya tsaf da wadataccin ƙafafu @ Mrs Jmoon Allah ya ƙara girma shugaba mai hikima.*

*Da yawa daga cikinku kun cancanci ambato a wannan ɗan ƙaramin shafin saidai tabbas banida ishashen wurin dazan aikata hakan, da wannan nake miƙo saƙon gaisuwa ga ɗaukacin members na ƙungiyar Exquisite writers forum, Allah ya ƙara haɗe kanmu.*

*Wannan shafin kacokam sadaukar wa ne gareki Oum Nass tawaje na. Alkhairin Allah ya baibaye rayuwar ki ya miki sarƙa.*
    
     *SHAFI NA ƊAYA*

           01.
Isashen kallo ya ke mata wanda yake ƙunshe da abubuwa masu yawa. Tabbas idan har yaci gaba da kallon zahida yanda yakeji ajikinsa komai zai iya faruwa! Tsigar jikin sa ce ta miƙe lokaci ɗaya yaji wani gumi yana karyo masa da har yake sauka yana ɗiga tamkar an watsa masa ruwa a jiki yayi tsammanin an daɗe sosai da wuce wurin, yayi tunanin tun shekarun baya wannan cutar dayake ɗauke da ita ta kau, ashe ƙarya ya keyi rabon sa daya yi irin wannan abun tun shekaru takwas da suka shuɗe shin anya shine kuwa! Zahida yamutsa fuska ta yi sannan a kasale ta ce,

"Amma zan iya zuwa na dawo gobe" Saida ya haɗiyi wasu yawun wahala sannan ya ce yana kallon ta har lokacin,

"Amma dazaki iya dakin ɗan jirashi,banaji zai ƙara mintuna sama da biyar nan gaba bai ƙaraso ba." Ɗan resting bayan ta tayi akan kujerar data ke kai zaune sannan a hankali ta furta,

"Mintuna biyar ɗin dai idan har ta cika bai ƙaraso ba gaskiya zamma iya haƙura ni, a rayuwa na tsani rashin tsari tun kafin aje ko ina na fahimci baku shirya wannan aikin damu ba" Lumshe idon sa yayi cikin jin zafin kalaman ta amma tabbas Zahida ta gama kashe masa baki, dan haka cikin wayancewa ya ce,

"Kiyi haƙuri ba haka muke ba wannan ma babban kuskure muka samu" kallonshi ma bata samu yiba ta lumshe ido kawai shi kuwa ya kafe ta da ido baya ko ƙiftawa har zuwa sanda aka shigo office ɗin nashi da sallama. Kallon Hafiz yayi sannan cikin dakakkiyar murya ya ce,

"Amma Hafizu wannan wace irin shiririta ce? Kana kallo wannan baƙuwar fa daga yamai tazo, sannan ta sanar dani komawa take so ta yi yau, amma gaba ɗaya ka ɓata mata rai da lokaci" Sunkuyawa ya yi sannan a hankali ya furta,

"Kayimun afawa ranka ya daɗe wani uzuri ne ya tsare ni a hanya, ga kuma mugun labarin danazo dashi, dazaka bani mintuna goma damun fara ganawa irinta sirri kafin komai" Tsaki gajere Ali yaja sannan ya ce,

"Look Hafizu we have a client here, so dik wani mugun labari ajiye a gefe zata samu tafarnuwar da kuma citta? Share gumi Hafizu ya yi sannan ya kuma cewa,

"Saidai ko zata ƙara mana lokaci nanda sati ɗaya yallaɓai amma gaba ɗaya bako ɗaya a ƙasa" Yamutsa fuska zahida ta yi a hankali sannan ta ce, "Ba damuwa zanyi tafiya yau amma inshaa Allahu nan da sati biyu zan dawo. Inna dawo saimuyi wannan harkar" Tana kaiwa nan ta miƙe zata bar ofishin shima a hanzarce ys miƙe yabi bayan ta, saida ta isa kusa da motarta sannan taja ta tsaya shima yaɗanja tunga tare da cewa,
"Hajiya Zaheedah lambar wayarki fa? Kinga kayan suna samuwa sai kawai na miki waya ko? Watsatsen kallo ta cilla masa sannan a zafafe ta ce,

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now