SHAFI NA TA DA TAKWAS

386 75 6
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                    EWF
 
     *BILLY GALAFLDANCHI*

           38.

Da sauri Baraka ta ɗagata ta re da soma jijjigata amma ina ba numfashi a tare da ita, cikin azama ta yi waje ta fara neman ceto, yaa Ali ya fita, direba ta kira haka suka kamata itada Hajjo sai mota, Zuwairah ta dasƙare a tsaye tana tunanin me zuciya ya ingizata ta aikata haka? Mekenan ta yi? Koda cikin ne ai rarrashi ake ba faɗa ba haka daga sama!  Jikinta a mace ta bi bayansu batare datasan aaibitin dasuka nufa ba, dukda dai tasan baya wuce asibitin Mai rawani, saboda cen yafi zuwa kowama ya sani, a gaggauce aka karɓe ta inda aka soma bata taimakon gaggawa, Baraka ita ce ta kira Ali ta faɗa masa komai da asibtin da suke, kusan lokaci guda ya iso shida Zuwairah amma a wannan lokacin ko kallon kirki bai mata ba ita ɗinma bata ce masa komai ba sai tsayuwa har aka fito da ita daga Emergency ɗin! Likita ya masa bayani abin da sauƙi hadda firgici da fargaba saidai suna buƙatar ta huta dukda ba ba abinda suka mata amma ta farfaɗo! Bacci take yanzu, har yamma Ali bai kula Zuwairah ba ita ma tana zaune ne a asibitin har akayi magrib, saida taga Baraka taje ta kawo abincin sannan ta ce, "Honey wlh bada gangan bane ba, kuskure aka samu, nifa jan rigarta kawai nayi  sai santsin tile ya jata ta faɗi mama ba ina nufi in cutar da ita bane ba" Lumsassun idanshi ya zube mata sannan ya ce, "Akan me zaki ja mata rigar, duk irin kawar da kai da nann nann danake da ke saida kika ɓatan raina, kin matsa akan tana ɗauke da ciki tunda kikaga bance miki komai ba ai kinsan da dalili ko?"  Cikin mamaki ta ce, "Yarinya zatayi ciki ba aure yaa Ali ka ce kuma kanada dalilin yin shiru wane dalili ne haka?" Miƙewa ya yi tsaye sannan ya ce, "Fatima matata ce kuma nine uban cikin dake jikinta" Wani dumm ta ji zuciyarta ta soma harbawa cikin sauri, dafe kanta tayi sannan ta kalleshi a hankali ta ce, "Baban Baby saboda kawai ka kareta zaka furta hakan?" Juya mata baya ya yi sannan ya soma magana... "Saboda yanayin lalurar dakike ɗauke da ita ya tilastamun yin shiru da bakina akan gaya miki wacece Fatima awurina bayan sanin da kika mata na ƙanwata. Gaba ɗaya a tsayen dayake bai rage mata komai ba tun farkon fyaɗen da yayiwa fatima, auren da aka masa da ita sannan kuma da labarin azabar data bashi ta sha, ya ƙara da cewar "Ya zamemun dole in gaya miki gaskiya wata rana, na zaɓi wannan ranar ne saboda ita ce ranar datafi zuwa da ruɗu sosai, na san ban kyauta ba dana ɓoye miki wannan amma Allah ya sani banyi da wata manufa ba face gudun taɓa lafiyar ki, bansan zan saki jiki da ita da wuri haka ba, kiyi haƙuri bansan zamana da fatima zai yi tsawo haka ba shiyasa, Yanda nake sonki a matsayin matata haka nakeson Fatima, ita fatar zakimun uzuri zakuma ki fahimci manufata, na tabbatar kinsan labarin fyaɗen dana bayar nayi wata tana da ƙananun shekaru a kotu" Batai magana ba sai sheshekan kukanta data cika ɗakin, takowa ya yi a hankali kusa da ita ya sauketa a ƙirjinsa ya yi mamakin yanda ta kwanto babu musu sannan ta ce, "Allah sarki Fatima, a wannan shekarun ta haɗu da wanan jarabtar, harda hihuwa ita kaɗai, harda binne yaronya da hannunta, meyasa mutanen ƙauye sukeda ƙarancin ilimi, meyasa suka aikata mata haka? Ashe ni gata na samu, ashe ni baiwa ce dani, wlh naji mata zafi, meyasa zaka ɓoyemun irin wannan maganar, kasan iyakar haƙƙinta da muka ɗauka, yarinya da mijinta agaban idonta muka riƙe tauye mata kwananta, kasan haramcin aikata hakan kuwa yaa Ali? Yanzu da wanne idon ma zan kalleta" Runtse idonshi ya yi cikin jin tsananin kunyar Zuwairah dama zata fahimceshi haka ya ɓata lokaci wurin taimakon ta? Dama zata fahimce shi haka ya damu kanshi yanayin dazata shiga inta sani, ashe tafishi hangen nesa, cikin damuwa ya ce, "Ki gafarceni Zuwairah ke ɗinma na cutar dake matuƙa, ki yafemun badan halina ba ke ɗinba ban miki adalci ba"

"Ni babu abinda ka mun, ba abinda ka aikata mun fa ce gudun ɓacin raina daya sanya ka bari muka zalunce ta, a hakafa ita ce uwar gidan,ita ce babba wata nawa mukayi muna tauye haƙƙinta, wace mace ce zata yarda arayuwa ayita ɓoyon cikin jikinta saboda gudun ɓacin ran kishiyarta, wace ma ce zata kame bakinta tana zaune gidan mijinta batada kwana, a wannan zamani zama a samu kuwa? Haba Ali duk wannan zagayen da muke fa lahirar mu mukewa, meyasa akan wani selfish interest namu zamu tauye haƙƙin wata?" Nisawa ya yi cikin jimami sannan ya ce, "Gaba ɗaya kunyarki ta gama mamaye rayuwata, ke macece abarso, ke macece da babu irinta, wlh irinku a duniya ƙalilan ne, irinku a wannan duniyar basuda yawa sam, irinku a Wannan duniyar ababen riƙewa ne gagam, ki ƙara gafarta mun kuma ki yafeni" Janye jikinta ta yi ganin Boɗɗo a tsaye bayansu ta ce, "Fatima kin tashi sannu kinji" Ali da sauri shima ya juyo ta re da yi kanta da azama ya riƙo hannunta tare da cewa "Sannu Fatima ya jikin" Da sauri ta ƙwace hannayenta a nasa sannan ta ce cikin tashin hankali, "Karka kuma taɓani, karka kuma Zuwa inda nike, karka kuskura ka kuma nunawa ka sanni, dama kaine? Dama kaine ka jefa rayuwa ta a haɗari kuma ka sani amma ba share, kana sane amma ka nunan ba haka bane ba, kanaji kana kuma gani ka munamun baka sani ba, tsakanina da kai Allah ya isa, cikin nan bazan taɓa haifeshi yanda ka bari Haidar ya mutu haka wannan cikin da kakeso kamar ranka saina hallakar dashi, bana son ganinka na tsane ka!! Zuwairah ce ta yi azamar riƙe ta "Haba Fatima,yanada kyau yin imani da ƙaddara ta alkhairi ko akasin ta" Hannunta ta ƙwace taje ta buga kanta da bango, takai hannayenta duk biyu dama ta tuge kanula ɗin hannunta sai tsiyayar da jini ya ke, ta dinga dukan ruwan cikinta iya ƙarfin ta, Ali da Zuwairah sunyi sunyi amma yanayin borin datake yafi ƙarfin su, in aka tare nan ta tare can duk ta tuge gashin kanta ta zama wata zararriya ba ita ta tsagaita ba saida jini ya ɓalle mata, nan da nan Ali ya ƙara firgicewa kan kace meye ya fara zubar da ƙwalla....Saida ta galabaita sannan ta tsagaita tayi lamo tana sheshekar kuka, wannan wane irin muguwar ƙaddara ce ke bibiyar ta? Tayaya za'a ce Alinta ne ya mata haka? Ta taɓa zata shine amma daga baya ta ce shiba haka ya ke ba, meyasa ƙaddararta zata zo a yanayin da bazata iya jurewa ba??

   Da sauri Ali ya je neman likita, Zuwairah sai rarrashin Boɗɗo ta ke amma bata ce mata komai ba..."

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now