SHAFI NA GOM SHA TAKWAS

387 70 3
                                    

    *GINI DA YAƁE*.  FREE BOOK

         *BILLY GALADANCHI*

    *EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                       (EWF)

SHAFI Na GOMA SHA TAKWAS 18.

    Yanda Zuwairah take kallon Anty Yussy kaɗai ya isa ya nuna maka cewar jikinta a sanyaye ya ke, zuwa wani lokaci ta d'auke idonta daga duban ta sannan ta ce,

"Koda hakan yana nufin ranar mutuwa tana kusa kuwa." Cikin takaici Yusrah ta ce,

"Amma kina da tsananin son kai Zuwairah, bakya tab'a duba duniya ta sai taki, idan bakya buk'atar ki rayu ni ina bukatar ki rayu saboda tawa rayuwar da A'isha da bata da uba a kusa" Hawaye ne ya wanke mata fuska a hankali ta furta,

"Alhamdulillah" Sannan ta kuma cewa,

"Yusrah kowa ce rayuwa da tata kalar jarabawa, tawa rayuwar gaba d'aya an d'aura zanen ƙaddarata ne akan bautawa son Ali, zuciya ta tanada wani kusanci na musamman da ta Ali, saidai kuma shi bai damu dani ba, kinaji an tabbatar mun yana sabgogin sa cikin nutsuwa ya murje ya yi k'iba abinsa, acikin wata bakwai ya manta wacece ni, yasamu ci gaba a harkokin kasuwancin sa tunda kika mayar masa da kud'ad'en sa, yaya zan rayu da wannan nauyin? Tayaya zuciya ta bazata bugaba a wannan gaɓar?" Cikin tsawa Yusrah ta ce,

"Amma laifin waye? Ban hanaki nesanta kanki da shi ba? Ya dawo gareki after so many yrs wannan wane irin shiri ne mara tsari? Ke macece sanda ya barki raunin zamtowar ki mace ya haddasa miki ciwon zuciya, shikuma namiji ne Zuwairah yana sabgogin da suka isa ɗauke masa hankali daga ko wace mace a duniya, bayaga haka Ali tsayayyen Namiji ne maiji da kansa, yanada dauriya, ki koma Nigeria tare dani, Alhaji Abubakar ya matsanta mun akan maganar auren nan bazan tabbata ina yawon kasuwan ci ba, dole zanyi aure nima inason inga ƙwai na inda rabo" Saida ta had'iyi wani wahaltaccen yawu sannan ta ce, "Shikenan Anty amma ni bazan neme shi ba" Cikin tausaya wa ta ce,

"Zuwairah wallahi Ali da kanshi zai neme ki, har abada bazaki tab'e ba" Nan suka rarrashi juna sannan suka kwanta akan nanda sati uku tare zasu koma.

***************
     Saida ya gama ta je kansa tsaf sannan ya ɗaura agogon hannunsa tare da sanyawa hannayen rigarsa clips, suit ya d'aura akan shirt d'insa bak'a wuluk sai sheƙi take nan da nan ya fito tamkar wani balaraben afirika, da hanzari ya fito daga part d'insa yana rufe wa k'arewa ko ina kallo ya yi Alhamdulillah acikin watanni bakwai ya mayar da gidansa tamkar ba shi bane ya yi gobara, Zaid ya shiga k'walawa kira inda ya fito da gudu Hajjo tana bayansa tana kwasar dariya,

"Hooni Hajjo, kai Zaidu gaba d'aya ka rikice wanda zaije Nijar ne yake ta wannan iyayin tamkar wanda zaije landas" Dariya ya bushe da ita sannan ya ce,

"Allah Hajjo ke ƴar ƙauye ne, London ɗin ne wani wai Landas,kuma ni ba sunana Zaidu ba sunana Zaid" Taɓe baki ta yi kafin ta ce, "Zaidalo ne ba zaidi ba" Dariya Ali ya yi,

"Hajjo dan Allah ki daina biyewa Zaid ku fito mu tafi banaso mu makara" Juyawa tayi da hanzari, "Bara na d'auko jakar kayanmu Aliyu nafika mazari zanje inga ƙawata" Murmushi kawai ya yi ya juya zuwa mota. A gaba ya zauna bayan sun gaisa da direban har suka fito suka kama hanya..

    Kallon farko daya yiwa yarinyar saida ƙirjinsa ya yi mugun dokawa, idon ta yana kansa har sanda ya rab'a ta gefenta ya shige cikin gidan da wani mutum daya masa iso bayan sunsha baƙar wahala kafin su gane gidan a jamhuriyar Nijar. Koda ya ƙarasa cikin gidan gwiwar sa a sace ta ke. A gaban kawunsa ya zube ya gayar dashi cikin harshen fulatanci wanda abinda yake ji aciki bai wuce hakan ba, nan suka dawo hausa da hirar yaushe rabo har zuwa sanda Hajiya Umma ta zo suka gaisa sai kallon sa ta ke duk da batada labarin sa amma tabbas kallon farko ta tabbatar akwai abinda yake damunsa.

GINI DA YAƁEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora