SHAFI NA TALATIN DA SHIDA.

421 78 14
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                  EWF

   *BILLY GALADANCHI*

      36.

Kallon yanayin Fatima ya yi yay dariya ta re da miƙewa, saida ya yi sallah da addu'o'in sa sannan ya miƙe, "Ki shirya anjima da ƙarfe 11 na safe, Awwal zai kaiki wani wurin" kallon sa ta yi, "Yanaga hankalin ka a kwance ne wai?" Ɗauke kansa ya yi ya soma tafiya, "Kwartanci nazo da hankalina zai tashi?" Bata ce masa komai ba harya fita, ta ƙofar falonsa ya koma ya shiga, duk su Baraka wanda ya gayar da shi ba wanda ya amsa sai gyaɗa kai kurun. Zama ya yi a kujerar falo ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana danna wayarsa, da sallama ta shigo falon ta zo ta zauna a kusa dashi sannan ta ce, "Barka da safiya yaa Ali, fatan ka tashi lafiya"

"lafiya lau" ya bata amsa batare da ya kalle ta ba, cikin damuwa ta ce, "Wh bansan sanda ka tasheni ba, na gaya maka aina daina wannan shirmen, gajiya ne kawai a tattare dani jiyan, kuma tun shida da rabi na farka sainaga harka wuce masallaci inata jiran dawowar ka sai yanzu ka shigo" Kallon nutsuwa ya mata yanaso ya gano wani abin ganin bata fahimci komai ba ya sanya ya ce, "Ba damuwa ya gajiya?" Murmushi ta yi "Ai duk kai ne ka ƙara saukar mun da gajiyan" Sauke ƙafarsa ya yi sannan ya gincira bayansa da kujera ya ce, "Go and get me coffee plss mai zafi nakeso amma"  Miƙewa ta yi saboda yanayin sa ya kashe mata jiki shikuwa tana shiga kitchen ya dafe ƙirjin sa tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi, wato dai yayi arziki shida kanshi ya san bai kyauta ba, baije da niyyan kwana ba sam so yayi kawai idan ta yi bacci ya zame jikin sa ya gudo ya rasa ya akayi ya yi bacci awurin shima... Kitcehn ya sameta ya rungumeta ta baya sannan ya ce, "Honey kaina ke ciwo sosai fa" Hannu takai ta shafi sajen sa sannan ta ce, "Shine kaketa ɓata rai sannu kaji? Ciwon kai ba daɗi" Narkewa ya yi, "Kizo to ki kamamin kaina mana" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Wai babu yanda za'ayi muyi tafiyar nan a tare?" Numfashi ya sauke, "Honey kinga ban shirya ba ni, akwai sabgogi a gabana ni ɗan kasuwa ne kinsani, dakin ce kinaso mu tafi tare babu shakka dana rakaki" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Idan kuma ya zamana dole saimun surgery ɗin fa?"

"Babu abinda zai dakatar dani daga zuwa idan har hakan ya kasance dukda bana fata" Murmushi ta sakar masa 1month zamuyi, saboda haka idan ka samu lokaci ka ziyarce ni" Jinjina mata kai ya yi sannaj ya ce, "Yaushe zaku tafi abuja?"  kallon sa ta yi sannan ta ce "Zamu tafi yaa Ali? Ba kaine zaka rakani airport ɗin ba?" Murmushi ya ƙaƙaro sannan ya ce, "A hakane, ina nufi tafiyanku nam da kwana biyu gobe zaku wuce abuja kenan?" "A amma ka mana booking flight na gaji da yawo a mota"

"Ba damuwa zanyi inshaa Allah, akwaima wani abinda zanyi a abuja gwara in tsaya inga fitar kayan kawai"

"Allah ya taimaka, ɗazu naga kamun transfer 2million amma ai akwai kuɗi a hannuna" Murmushi ya yi sannan ya ce, "kuɗinki Daban nawa daban, haƙƙine akaina duk wani abu daya shafi lafiyarki in ɗauki nauyinshi, na tabbatar bazasu isheki yin komai ba, amma kudine yaɗan yanke a hannuna saina business zuwa goben ma zan tura miki miliyan uku inshaa Allah, kawai kumun addu'a yanda harkoki suka buɗe a yanzu suyita bunƙasa shikenan fa" Murmushi ta sakar masa, "Nagode, nagode sosai da kulawarka akaina, nagode sosai da soyayyarka akaina Haoney Allah ya ƙara buɗi".

    Wuraren ƙarfe sha ɗayann kuwa ta shirya tsaf tasha ado sai ƙamshi tabl keyi, Baraka nata zolayarta akan ta faɗa soyayya, bata kulata ba, saida taje ƙofa sannan ta ce, "Wannan hijabin da aka zura na meye?" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Bayason mayafi Baraka, ya zanyi da shi?"
"Amma ai matarsa tana sakawa" Murmushi ta yi sannan ta ce "Can tsakanin su" Tayi gaba Baraka ta dinga dariya saboda ita kanta Fatima masifaffen kishine da ita. A wajen gate ta yi karo da Zuzu inda ta gayar da ita a daƙile ta amsa tana mata wani kallo sannan ta ce, "Ina zakije?" Fatima tamkar zata kurma ihu haka ta juyo ta ce, "Wankin gashi zanje" Gyaran tsayuwar ta ta yi sannan ta ce, "Amma Fatima baki gayamun ba ai ko? Kokuma shi yayan naki kin sanar masa?" Fuskarta ta shafa kaɗan sannan ta ce, "Ba hanyar dazanbi naje part dinki, amma shi na masa waya shiyace ma driver ya kaini" Jinjina kai ta yi sannan ta ce, "Ba damuwa, zoki karɓa to" Takawa tayi kusa da ita sannnan ta ciro 5k ta bata, bata karɓa ba ta ce, "Anty Yaya ya bani kuɗi fa" Ɓata fuska ta yi, "Meye amfanina agidan to? Idan dai har ace kuɗin wankin gashi ma saikun karɓa a hannunsa ai bakumun adalci ba ,duk abinda kukeso ku tambayeni kai  tsaye, idan yafi ƙarfina zan gaya masa ya bayar a baki" Hannu biyu ta sa ta karɓa sanan ta ce, "Kiyi haƙuri anty, zan mayar masa da nasan, Allah saka da alkhairi" Hannun ta Zuwairah ta kalla da mamaki ta mayar da dubanta akan fuskarta, "Wannan wayar fa?" Ita ɗinka kallon wayar hannunta ta yi sannan ta ce, "A nawane yaya ne ya saya mun" Tunano kuɗin wayar ta yi amma anya yaa Ali nada hankali kuwa? Ta ayyana a ranta a sarari saita ƙaƙalo murmushi, "Lallai yayan nan yanaji da ke, wannan zuƙeƙiyar wayar bata miki yawa ba" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Anty zan wuce to" Jinjina kai ta yi, "Allah ya tsare idan kin kammala ki waiwayi gida da wuri" Gyaɗa kai kawai ta yi  ta juya ta faɗa motar da driver ke jiranta. Tana shiga wayarta ta soma ringinga ta ɗaga, "Kun kamo hanya?"
"A yanzu muke barin harabar gida"  Jinjina kai ya yi, "Ok ina jiranki" Murmushinta kife wayar Ali akwai wayau, ina zasuje ne haka to ita kam.... Zuwairah ta yi shiru tana ayyana abubuwa da yawa aranta bayan ta shiga motar, ƙamshin turaren dake jikin yarinyar nan kuɗin sa zai haura dubu hamsin, wai meke faruwa ne? Bata tsawwala ba ta kama hanya kawai....

****************
    Tayi mamakin ganinsu a wani matsakaicin gida mai kyau,  a harabar gidan suka taradda Ali, shine ya mata iso zuwa cikin gidan, kallon juna sukayi sansa suka isa bed room ɗin ya kafeta da ido yana murmushi, "Ina ne nan?" Ta wurgo masa tambaya yana murmushi ya ce, "Nan ɗin gidana ne danake ajiye baƙi" Jinjina kai ta yi sannan ta ce, "Tom na haɗu matarka dazan fito, ta ce ina zani nace gyaran gashi, tanata fada akan ban tambayeta izinin fitaba, kuma meyasa ma na karɓi kuɗi a hannunka bayan tana nan, ta ce inzam fita ita zanke tambaya kuma abin kuɗi in tambayeta sai idan yafi ƙarfinta zata karɓomun awurinka, a taƙaice sai kaga ba'a buƙatar ina doguwar hulɗa dakai" Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ai tafiya zamuyi tare da ita gobe shiyasa na ce kizo nan yau in huta inta kallonki zan dafa miki noodles" murmushinta sakar masa, "Bakace zamuje tare ba nima" Ɗan taɓe baki ya yi, nafasa dake" Shiru kawai tana kallon sa daga bisani ta cire hijab ɗin, riga ne da wando ajikinta sun mata shegen kyau, ta zare ribon na kanta nan da nan dogon sunar kanta ya baje, sannan ta gyara zamanta akan gadon ta ce, "Ina Noodles ɗin ban karya ba" dariya yayi ya ce, "Zo inbaki madara tukunna" Janyewa ta yi tana dariya "Ka kai kasuwa" Janyota yayi suka faɗa kwance akan gadon suna dariya.

*Bayan sati uku*

    An ƙara ɗaura Zuwairah akan magunguna tana shirin dawowa, amma sam zuciyar nan tata wannan ramin sai girma yake ƙarawa, anbata watanni shida ta dawo, idan babu wani ci gaba za'a mata aiki kawai. Ansha angwanci dan kusan kwanakinsunsha bakwai a abuja, saidai sun dawo gida saboda Fatima jiki yaƙi daɗi sam, haka kullum amai ta ke da kasala, ga yawan son ƙamshin jikin Oga Ali,  muddin bashi ta shaƙa ba bata iya bacci, nace wani sabon iskanci, Ali yayi yayi suje asibiti taƙi yarda harya ɗauki fushi da ita....ana wannan budirin Zuwairah ta diro ƙasar!!!

Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now