SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

422 76 5
                                    

      *GINI DA YAƁE*  FREE BOOK

                          EWF
    
           *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI*
17.

  Idanta ya kaɗa yayi jajir, jikinta amaimakon rawa a mace yake matuƙa, yayi sanyi fiye da tunanin mai tunani, ta kafe Anty Yusrah da ido batako ƙiftawa, duk wanda ya san zuwaurah kallo ɗaya zai mata ya tabbatar ranta a matuƙar ɓace ya ke, cikin sarƙaƙƙiyar murya ta ce da Yusrah,

"Menene haka? Zuciyar tawa da kike tattali shekaru takwas zaki ƙarasa da kanki gaba ɗaya? Ajiye ƙaunar da zuciya ta takewa Ali a gefe wannan mai sauƙi ne wannnan ita ce shekara ta tara rabona dashi ban kuma mutu ba, amma yaya zan rayu da tunanin cewar akan ɗauƙar fansar abinda akamun kinyi kisan kai? Gayamun ta wace hanyar zan rayu da wannan nauyin a zuciya ta" A hankali Yussy ta miƙe ta sauke Baby dake kan cinyarta sannan a hankali ta tako kusa da 'yar uwarta ta ɗaura mata hannu a kafaɗu ta furta,

"Na rantse da wanda rayuwa ta take hannun sa bani na tura a kashe Ali ba, banida zuciyar kisa, da inada wannan zuciyar da akan cikin Baby zan fara, wane magiya ne bakiyi ba akan a zubar miki naƙi? Ki san me zaki gayamun, tunda kikaga na tattaro duk abinda nake na baro ƙasar damukaje na dawo dan farin cikinki la shakka da ƙarfina da dukiya ta zan saka in taimakeki, na tabbatar miki zanje har kotu in sanar nice na zuga matarsa na shinfiɗa masa wannan ƙaryar.  Zancen guba ki tuntuɓi ɗan sandan daya duba abincin tunda kedai a wurin masu kayan fruits kika saya" Sauke nannuyan ajiyan zuciya ta yi sannan ta ce, "Anty waye yake neman ran yaa Ali? Banaji yana daga cikin mutane dasuke da tarin maƙiya gaskiya, mutum ne shi mai tsananin son kyauta da kyautatawa, yanason ibada matuƙa, ire iren su Ali basa samun maƙiya da yawa" Ɗan juyawa Yussy ta yi na wani lokaci kafin ta ce,

"karki nunamun cewar duk abinda nayi na ganin kin zama cikakkiyar lauya dukda ciwon da kike fama da shi ya tashi a banza, ɗan adam kika manta? Gaba ɗaya a talauce ma bazaka taɓa rasa maƙiya ba bare a sarauce, Ali yarone da kuɗi abokin tafiyar manya, wlh acikin abokanan sa tas wani zai iya kasheshi tsabar ƙiyayya, nidai bani ba ce, bazan iya kashe koda kiyashi bane ba, nayi dogon bincike akan halayyar Ali wannan dawowar da nayi na kuma tabbatar halayensa ingantattu ne, nayiwa wani malami tambaya ya kuma nunamun banida wani ikon shiga hurumun Allah ta'ala, saboda haka dukiyarsa ma dana damfara dama ƙwandala banci ba, zan mayar masa idan ya samu kuɓuta" Ragwaf Zuwairah ta zauna tana sauke numfashi a wahale,

"Anty gaba ɗaya kaina ya ƙulle, da ƙyar fa aka samo kanshi a asibiti" Kafin Yusy tayi magana wayar Zuwaurah ta shiga ƙara, da sauri ta ɗaga wayar ganin officer data saka bincike ne akan maganar inda nan take ya ce,

"Hajiya wannan matsalar fa bata Ali ba ce shi kaɗai, jinin sa ne bashi da ƙarfi ya sanya abin ya yi saurin taɓashi, zan gaya miki acikin abincin gidan kurkukun nan aka saka guba, dan yanzu haka hatta wacce ta yi girkin batada rai ita sam, sannan har ma'aikatan dasuka ci abincin nan suna asibiti rayuka goma sha huɗu aka rasa yanzu haka kuma muna kan irge" Da sauri ta miƙe tsaye, "Hasbunallah wane mara imanin ne zaiyi wannan mummunan ɗanyen aikin? Me kuma mutanen kurkukun sukayi masa?" Ɗan ƙasa ya yi da murya sannan ya ce,

"Hajiya akwai wani wanda aka kawo, to matsalarshi ta shafi wani babban ɗan siyasa, ana tuhumar yana tsoron ya tona masa asiri shine yakeso a mutu har liman" Jinjina kai ta yi,

"Tabbas ƙasata babu adalci acikin ta, to Allah ya taƙaita abun"

*BAYAN WATA ƊAYA*

    Wani wahaltaccen yawu Amirah ta haɗiya yanda Zuwairah ke aika mata tambayoyi na ƙurewa, saida ta fita tunanin ta sannan ta kalle ta ta kuma ce wa,

"Mecece hujjarki to ta yanke masa hukunci? Wane irin ganganci ne ya kaiki ɗakin da maxa suke a wannan daren? Meyasa da ya ce ki fita kika je kuma kika dawo?" Shiga ruɗu ta yi dan bataƴi tsammanin wannan tambayar ba sannan ta ce,

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now