SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR

383 69 11
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                   EWF.
   
     *BILLY GALADANCHI*

  25.

Wayancewa ya yi ta re da azamar kamo hannun Zuwairah, "Yauwa Swt hrt zoki rabani da yarinyar nan, gaba ɗaya wai bazata bari mu tafi mu barta ba tsoron aikin ta keyi, nayi rarrashin duniya sai kuka take tamkar wata ƙaramar yarinya, dan Allah ku bata magana" Ɗan sauke ajiyan zuciya ta yi sannan ta ce, "Shine zakaho ka rungume ta kana wani rarrashi saikace ƴar shekaru 5 Daddy? Idanma rarrashin ta zakayi aiba haka ya dace ka yi ba" Murmushi ya yi sannan ya kalli AnyynYussy ya ce, "Anty kinsan Allah wannan yarinyar komai nata abin rigima ne, yanzu meye abun ɓacin rai anan?" Murmushin yaƙe ita ma antyn ta yi, "Ai gaskia kam, wa take dashi anan kusa da zai rarrashe ta idan ba ku ba, ke bakya kusa ya kike so ta yi" Ta ƙarashe maganar tana janyo Boɗɗo a jikinta ta shiga rarrashin ta da kalamai masu daɗi har ta daina kukan, ita kanta tasha jinin jikinta da yanayin kyau da diri irin na Boɗɗo, Sanda idonsu ya haɗu kuwa ƙaramar hauka ne kawai batayi ba akan kyawun idon ma Boɗɗo, har suka bar wurin da magrib bata daina kallon ta ba.
  Zama sukayi a amota suna fuskantar juna, Yussy ta kamo hannun Zuzu cikin jimami ta ce, "Zuwairah kinada ƙarfin zuciya, ki ce mun a labarin da kika bani na wannan yarinyar nafila ne banga farilla ba"  Sauke numfashi ta yi sannan ta ce, "Anty wallahi Boɗɗo batada matsala ta ada tsananin nutsuwa ga ilimi duk karatun dake kan Baby da Zaid akanta suke kwasa, ni damuwa na kawai mijina ne, amma duk da haka idan muka koma gida zan san yanda zanyi su daina koda ganin juna ne, nima kaina zan zama mai tsananin tsauri akanta, yanda bazata fahimci abinda nake nufi ba, zan mata gata duk wani abu dazan ƙanwata zan mata amma gaskiya ko yawomun acikin gida ba hijabi zan tsawatar musu bazan iya ba wlh" Shiru Yussy ta yi sai cen kuma ta ce,

"Ki san yanda zakiyi ki mayar da ita ɗakunan baya inda suka taso, ki nesanta ta da mijinki ainun, bayaga haka bakince asibiti ta zo ya kaita ba, to dan Allah idan ta warke ya mayar da ita ƙasarsu dan wlh koni bazan so yallaɓai na ya ci karo da wannan ba, kinsna Allah duk yanda ake zuzuta kyawuna dana ganta saida na raina kaina." Murmushi ta yi, "Kai Anty karmu zake sa yawa ƙanwar Ali ce ko bama so, kuma ina laifin kyawunta ba gashi ta samma Baby ba"  Dariya kai sauti ta yi, "Ai idon ne kaɗai ba irin na Baby amma komai nasu iri ɗaya, sai sumar kai nata baƙi wuluk na Baby kuwa kalar na Umammn mu ne da sirkin ja ajiki" Dariya sukayi suna mamakin kansu da kishin wannan halittar.

    Bayan sun koma gida Ali kasa sukuni ya yi saida ya cewa Zuwairah zanje siyan Samosa ta zo suje ta ce masa bazata ba dama yasan bazata je ɗin ba dan sam batada yawo ita, shi kaɗai ya fita inda yana siyan samosar kai tsaye asibitin ya wuce inda ya tarar tana kwance ita kaɗai kanta a sama idonta yana kallon silin saidai kallo ɗaya zaka mata kasan tunani take dan batama san da zuwan sa ba, dama basa bari masu kula da marasa lafiya su kwana musu a asibiti akwai nurses da suke kulawa da marasa lafiya, tausayi ta bashi ga TV a ɗakin ga kuma waya a gefenta amma babu idan kallo bare ta danna wayar tata, gyaran kurya ya yi tare da sallama ta waigo a hankali  ta kalli wurin da maganar ke tashi tare sa amsa sallamar sa. Tashi ta yi zaune a hankali zuwa lokacin ya ƙaraso inda ta ke zaune zama ya yi kusa da ita sannan ya ce, "Fatima ke kaɗai ko?" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Daddy ai na saba, a haka na rayu tamkar wata mujiya, ni zaman kaɗaici sam ba ya damuna" ƙura mata ido ya yi na wani lokaci, "Meyasa zaki ce haka?" Murmushi ta yi a karo na barkatai sannan ta ce,

"Baka taɓa jin labari na ba ko? Inaji babu wanda ya taɓa baka tarihin rayuwa ta, inshaa Allah  idan Allah ya bani lafiya ka dawo,kafin mu rabu in tafi Agadaz zan baka tarihin rayuwa ta, inaso ko bayan mun rabu ya zamana ka san wa ka aura? Menene labari na? Yaya na rayu a baya." Kafe ta ya yi da ido yanajin wani iri a ilahirin jikinshi da baisan me yakeji ba game da ita, shidai ya tabbatar baya sonta india ba soyayyar jinin juna dake yawo acikin jikin su ba, amma yanayin dayake tsintar kansa idan suna tare dabanne ji yake tamkar ya hau gajima re a sararin samaniya yana shawagi cikin nisashaɗi, "Meyasa bazaki bani labarin naki a yanzu ba koda a taƙaice ne, sai kika sanya na zaƙu in sani." Dariya ta yi, "Dukda ba wani shiri a tsakanina da kai amma a ƴan wannan kwanakin idan muka keɓe muna magana dakai nikanji daɗi, sai komai yakemun tamkar ba kai ɗin bane ba mai yawan zafi da faɗa akan komai da ya shafe ni, akan wannan zanyi sauri in baka labari na a yanzu ban saniba ko idan ka dawo zaka koma kamar da, idan kana mun faɗa da saurin fushi ta re da hanta ra bazan taɓa iya baka labari na ba, amma yanzu dakake kulawa da ni zanyi hanzarin baka labari na." Gyaran zaman sa ya yi ya fuskance ta sosai, ita kuwa ta fara magana ....

GINI DA YAƁEHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin