SHAFI NA SHIDA

398 67 3
                                    

    *GINI DA YAƁE*  FREE BOOK

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                    (EWF)

      *BILLY GALADANCHI*

SHAFI NA SHIDA. 6

     Sanda abubuwa suka lafa sannan Ali ya fahimci gaba ɗaya gidansa ya ƙone ƙurmus sannan bayaga kayan ciki da aka fitar bai tsira da komai ba na daga abubuwan rayuwar sa, suturun sa ma babu abinda ya fita saina jikin sa, a sashinsa dai bai tsira da komai ba domin ko daga nan wutar ta tashi. Kuma a kayan da aka fitar ma na yara sn musu sata da sunan ceto. "Alhamdulillah" yake ta nanata wa saboda an tsira da rai. A wannan ranar ya tabbatar rufin asiri ma Rahama ne babba! Hsr dare suna harabar adana motoci da wuta baikai ba akan tabarma suna karɓar sauran maƙota 'yan jaje, labarin wutar har gidan TV da radio saboda layi ɗaya wutar ta sauke kuma anrasa tushen wutar, sai dare sannan Amirah da yaranta suka tafi gidansu shikuwa ya zauna nan har gotawar ƙarfe tara na dare. Ganin hakan bazata fiddashi ba ya ɗaga wayar sa ya kira wani abokin sa Shehu, bayan sun gaisa ya sanar masa labarin gobarar da halin da ake ciki, jajanta masa ya yi sannan ya ce,

"Haidar harna kwanta ka kirani da safe zan nemeka" kafin ya yi wata maganar harya kashe wayar. Bin allon wayar ya yi da kallo anan ya zauna ya dinga kiran abokanan sa dayasan sunada hali yana mai tunanin samun aron gidan zama amma saidai su masa jaje su ce zasu kirashi da safe. Ali a wannan daren shagon sa ya tafi ya yi parking motar a agefe ya shiga daga ciki ya yi alwala ya yi sallah ya watsa ruwa dake a kwai ban ɗaki a ciki. sai da ya kwanta sannan ya fashe da kuka!

*****************
   Hajiya Umma tunda ta isa Yamai ake zuwa gaidata tare da kawo mata cima iri iri, ta yi matuƙar jin daɗin kasancewar ta acikin dangin ta, yau duk saitaji inama tun mutuwar mijinta gida ta dawo? Mahaifin Ali ba wani dangi ne dashi ba ko a kanon, mahaifiyarshi ce 'yar kano amma mahaifin sa jan buzu ne  a ƙasar Niger cikin agadez. Zama kawai ya kawoshi kano ya dasa bishiya taja reshe ɗaya jal shine mahaifin Ali.  Yammaci ya tsala ga yanayi irin na damina yau kuma sai aka ta shi da iska mai sanyi har yamma, garin ya yiwa Umma matuƙar daɗi saita soma tunawa tana tariyo lokacin ƙuruwa, Murmushi ta yi tare da Boɗɗo da kallo, cikin kulawa ta ce,

"Boɗɗo am, ki tashi ki shiga ciki mana, bakya tsoron sanyi ya kamaki bama kallabi a kanki" Yarinyar da shekarun ta bazasu haura ashirin da biyu ba kyakyawar budurwa ajin farko 'yar fulani sirkin jan buzu mai taƙama da diri na usul, ta raba sumar kanta gida biyu ko wanne jelar ta kitse shi ya sakko mata gefen kafaɗun ta. Ata gaban goshin ta, gashine ya yi kwance har yana shirin haɗewa dana girar ta dayake a cike baƙi wuluk, Yanayin sakkowsr sumar  kan nata saiya rufawa tsinin goshinta asiri. A hankali ta waigo inda sautin muryan ya ratsa dodon kunnen ta idon ta ta shigar acikin na Hajiya Umma suka kalli juna, a hankali ta yi murmushi sai kuma ta ce acikin hausan da baiko gama nuna a bakinta ba, "Inason wannan yanayin ne, idan na shiga ashiki bazan ji daɗi ba" jinjina kai Hajiya Umma ta yi sannan taci gaba da bin idon yarinyar da kallo, tunda take arayuwa bata taɓa ganin halittar ido masu kyau irin na Boɗɗo ba, acikin zagayen baƙin idon ta zaiba ne, acikin gefe gefen farin idonta tamkar tangaram, duk ta kalli haske zakaga wani hasken annuri acikin idon tamkar tangaram sabon ɗauka mai asalin kyau, tunawa da Hajiya Umma tayi cewar Boɗɗo fa bata gani ya sanya a hankali ta furta "Ikon Allah" Murmushi Boɗɗo ta yi dan dama ta kafe ta da idone ta kuma kasa kunne tana sauraron ta ji Gwagwon nata ta tilasta mata zuwa ciki, amma jin kalmar data faɗa saita ɗauke dubanta daga idon Gwagwo Umma ta mayar akan abinda take kallo tun ɗazu shine turken dabbobin dake gaban ta. Hajiya Umma kums kallon ta ta yi ta ce,

"Boɗɗo ance kinsan kasuwa sosai ko?" Murmushi ta yi sannan a hankali ta ce, "Ko ina ma na sani" Murmushi Hajiya Umma ta yi tana ƙara tuna labarin Boɗɗo da aka bata akan cewar tana gane komai kuma duk inda taje so ɗaya tare dakai bata buƙatar maimaici zata gane hanya wannan ya sanya take kiwo sosai dukda kasancewar su a cikin babban birnin Niger wato Niami.

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now