SHAFI NA TALATIN

412 67 5
                                    

   *GINI DA YAƁE* FREE BOOK

                    EWF

         *BILLY GALADANCHI*

  30.

Ganin sa'o'i uku sun shuɗe ba labarin Ali ya sanya Fatima fitowa domin neman adaidaita sahu ta je gida, yunwa takeji saboda ba abinda ta ci, mai rake ta fara cin karo dashi wannan ya sanya tana murmushin jin daɗin ganin gwanar ta ta matsa kusa da shi, "Sannu Malam" Mai raken ya ɗago ya kalle ta adaidai sanda wani matashin yaro yazo wurin mai raken shima ya tsaya, riƙe baki kaɗan mai raken ya yi yana kallon ta saida taɗan tsargu ta ce, "Malam lapia?" Jin muryanta ya sanya saurayin kallon fuskarta abinda ya dasƙarar da shi, mai raken kuwa ya ce, "Yi haƙuri hajiya mamaki nake acewai ba indiya tanajin hausa haka" Dariya ce ta suɓuce mata mai sauti, dan harga Allah dariya ya bata matuƙa, saida ta tsagaita sannan ta ce, "Kaga Malam rake zaka bani na ɗari biyar hanzari zakayi dan sauri nake" Saurayin daya gama ruɗewa ya ce "ka bata na dubu biyu" Ɗagowa ta yi suka haɗa ido, nan da nan ya kuma susucewa wannan idon fa! A hankali ta furta, "bana buƙatar hakan bawan Allah, yanda ka faɗa bawai bazan iya saya a hakan ba ne a yanda na saya ɗin hakan zai isheni, nagode" Mai raken kallon ta ya yi "Haba hajiya ni ina murna naga ciniki ke kuma zakimun haka dan Allah" 

"To idan hakane ka saka zan biya da kaina" Saurayin shiru ya yi mai raken ya ruga ya saya babbar leda ya dawo ya irga mata raken ya miƙa mata, "Hajiya gashi" Ta karɓi ledar tare da miƙa kai dubu biyu, inda saurayin nan ma ya miƙo nashi, kallon su mai raken ya yi sanan ya ce, "Hajiya tunda ammiki kyauta ki karɓa mana dan Allah, ba kyau hakan" Wani kallo ta wurgawa mai raken a masife, "Kaci gaba da karɓar kyauta a hannun koma waye amma nidai bana buƙatar kyautar sa" Murmushi saurayin ya yi "Hajiya niba saceki zanyi ba, sata dai bayan wacce ke kikamun ta zuciyata sukutum meya saura kuma" Ɓata fuska Tayi danta fahimci inda ya dosa, tana shirin juyawa kawai taji saukar naushi afuskar wannnan saurayin, inda ya ƙwalla ƙara tare da dafe kumatun sa, Hafiz ne ya riƙo Ali, "Haba Ali meye haka wai, control ur self mana"

"Uban waye ya baka  izinin yin magana da matar aure? Meyema ruwanka da ita?" Saurayin nan cikin fusata ya soma ƙoƙarin rama naushin daya kumburar masa da kuncinsa nan da nan, "Akan me zaka nausheni, kai mahaukacin wane unguwa ne? Tilas na mata? Ko gani kayi na mata tilas ne" Da sauri mai rake ya ce, "Kai kuma saurayi karkayi ƙulla ƙulla, metace maka ina ana kazo ka sameta tana siyen rakenta a are ka yafe, kawai ka fito ka ce bakasan tamada aureba kayi haƙuri, amma shiashigi kake mata tana tureka" Ali kuwa ya ƙara hawan bambami inda yake shiga batanan yake fita ba, da ƙyar aka raba faɗan, suka faɗa motar Hafiz da dama shine ya kawoshi ɗaukan nata, ita ɗinma tunda suka shiga motar yake mata masifa har suka isa gida.

  Hafiz sanda  suka direta ta sauka kallon Ali yayi, "Babu shakka Ranka ya daɗe kana fama da babban ciwo, inaga a rayuwarka baka taɓa so ba sai akan wannan yarinyar, wannan mummunan kishin aiya shahara" Shiru ya yi yana nazarin maganganun sa gefe ɗaya kuma yana ayyana yanda yakeji a ranshi duk sanda wani ya kalli Boɗɗo, bayasonya gaskata maganganun Hafiz danshi yasan bazai fara ba, yarinyar nan duk idan sukaje zaria gobe babu shakka zai gaya mata gaskiyar koshi waye a rayuwar ta, bazai bari ta cutu ba, kazalika shima bazai cutar da ita ba, runtse idonshi ya yi sannan batare da neman izini ba ya soma baiwa Hafizu labarin abinda ya shiga a tsakanin su Boɗɗo har zuwa labarin da ita kanta ta bashi da kanta, cikin sauke numfashi ya ce, "Hafizu bantaɓa tsammanin akwai ranar dazan fayyacewa wani na wannan maganar ba, amma babu shakka yanda take ɗawainiya dani a tsakankanin waɗannnan watanni idan naci gaba da danne ta mutuwa zanyi, ko da zanso Fatima fiyeda yanda zanso kaina kai kana gani na isa in nunawa duniya da ita kanta, abu ɗaya na sani wannan maganar babu shakka saita san gaskiyarta wata rana koba yanzu, to menene zaisa in ƙara wargaza kaina a gunta ta hanyar ɓoye mata" Jim Hafix yayi yana ayyana abubuwa da yawa sosai akan wannan al'amarin, bayan jan dogon fasali sannan ya ce, "Wannan kuskure bazai taɓa gyaruwa ta hanyar sanar mata gaskiyar komai ba a yanzu, sakinta kuma bazai ƙarawa abun komai ba illa ƙara wargaza komai  da ƙara rura wutar ƙiiyayyar ka a zuciyarta, ka sani Ali koni ne ita bazan yafe maka ba, amma kai kanada dama yanzu a hannunka, ka adana komai a yanzu, pretend as if bakasan komai ba a yanzu ka barka kawai sai sanda ka koya mata sonka, zama da kai da kuma sabo mai tsanani da kai"  kallon sa ya yi da mamaki, "Tayaya duk zan iya aikata wannan nida babu wani kyakyawan mu'amala a tsakanina da ita, bayaga haka kasan Zuwairah har yanzu batasan matata ba ce ba, kuma nifa abu kaɗanne ya fusata ni indai akace maka maganar Fatima ce" Kallon sa Hafiz ya yi sannan ya na murmushi ya ce, "Ina ganinka tamkar  ka waye ashe kaiɗin baƙauye ne, bari kaji yanda zakayi acikin sauƙi, tunda yake tabbas kana tsananin son ta..........

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now