SHAFI NA TALATIN DA BIYAR

350 64 3
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

               EWF

     *BILLY GALADANCHI*
35.

Wayarsa dake ringing ya zago daga alhujin sa ya ƙurawa screen ɗin ido, zama ya yi tare da ɗaga wayar cikin murya mai sanyi ya ce, "Honey Mutanen Nijar ya akayi ne?" Cikin shagwaɓa ta ce, kawai tunda mukayi waya nake jina a buƙace saikasan yanda zakayi da ni"  Murmushi yayi sannan ya saci kallon Fatima, cikin hikima ya ce, "Haƙuri zakiyi ina yau saura kwana shida? Kawai ki cire aranki zakiga kamar gobe ne" Gano baya cikin mood na irin wannan hirar ya sanya ta ce, "Babu damuwa" sannan ta kashe kiran a fusace ta wurgar da wayar tare da dafe kanta, meyasa ta kasa nutsuwa da yanayin Ali ne? Takira ne cikin hikima kawai saboda tanaso taji idan bata tayar masa da sha'awa ba, Ali bazaiyi wannan hirar da ita ba ya gagara kira yana gaya mata baida lafiya saiyasha maginsa tUkunna,, tunda ya je India dama ya samu maganin matsalar sa a hankali a hankali abin yana raguwa kuma idan ma ya taso yasha maganin anwuce wurin shiɗinma sai ya gama yi mata rigima a waya! Kalmar da wata mata ta faɗa a daren jiya ce ta faɗo mata, "Wannan shine kishiyar Boɗɗo?" Yare aka sauya abinda ya dulmiyar da ita, juyi ta yi ta yi gyaran kwanciyar ta sannan ta lumshe ido cikeda fargaba, ina zata iya zaman kishi da wannan indiyan Nijar, ai kawai gwanda tabar mata!

    Manne da juna suka kwana dukda tanajin tsananin kunyar sa, asuba nayi ya soma shafa sumar kanta data gama tarwatse wa wuri ɗaya gashi tanada sauran danshi, a hankali ta buɗe idonta saidai bazasu ga juna sosai ba tunda gari ba gama waye wa ba. "ki tashi muyi sallah" Ba musu ta miƙe tare da yin miƙa mai ƙarfi ta soma ƙokarin gyara zaren rigarta da ake ƙullewa da Ali ya ɓalle tuni tana bacci, tare sukayi sallah sannan sukayi addu'a mai tsayi har gari ya waye haske ya bayyana, tambayoyi akan addini tasha su saidai malam Ali ya fahimci kanshi zai ƙule ya sanya ya haƙura ya ƙyale ta..... A hanyar su na zuwa kaduna kuwa karatun alƙurani mai girma sukeyi, idan ta janyo aya ya karasa ko idan ya ɗakko ta ƙarasa, sunayi suna murmushi, ta zata Ali bashida ilimi saitaga saɓanin tunanin ta dan kuwa a ƙarshe ƙarshe ma saidai tabkakare saboda ya zurfafa ya ƙure jaddanta dama arba'in da bakwai ne a kanta shikuwa ya kai hamsin damma ya daina ya manta da yawa, duk wanda ya kakare ɗan uwansa ke tashinsa yana dariya a haka suka isa garin, yanayin garin ya ƙayatar da ita sosai, bin ko ina ta yi da kallo har suka isa wani ƙayataccen gidan cin abinci, saida ya yi parking sannan ya ce, "Baby Muje kici abinci, nasan ma yanzu cikinki ya fara ambatar alhaji ciroma ko? Murmushi ta yi sannan ta ce, "Inada saurin gane abu b yabon kaina nake ba, kaga yanzu acikin watanni uku da buɗewar idona na fara iya karatun hausa, so nake dan Allah ka koyamun na turanci kalli yanzu rubutun gidan abincin nan ya ƙayatar amma inzaka kasheni bazan iya karantawa ba" Murmushi ya yi sannan ya ce, "Bakida matsala yau ɗin na zamu fara ma"  Murmushi ta yi sannan ta ce, "Yau tuwon miyan egusi zanci, ka kaini wurin daba mutane sosai inajin kunya" Kallon nutsuwa ya mata sannan ya ce, "Bazakici abinci acikin mutane ba ma, idan kina chewing abu kinfi kyau" Kallon sa ta ke da tunanin menene ma'anar kalmar chewing sai cen ta ce, "Meye Chewing ɗin?" Laƙuce hancinta ya yi "ƴar ƙauye, na ce idan kina tauna abu kinaci kinfi kyau" Murmushi ta sakar masa, "Tauna abu ko cin abu shine Chawing ɗin?" Ta sake tambayar sa, "A amma chewing zakice ba chawing ba" Bata yi magana ba ta ɓalle murfin motar shima haka suka fito. Saida suka zauna cin abincin sanan ya ta kalli lemon daya buɗe ya kurɓa ta ce "Kaima idan chewing abu kafi kyau, yanzu da kake chewing lemon nan baka kanga ba" Bata ƙarasa maganar ta ba ya wanke wurin da lemon bakinsa saboda yanda ya kasa haɗiye dariyar sa, sororo ta yi tana kallon sa, saida ya tsagaita ya saka tissue ya goge jikinsa dama juyawa yayi gudun bata wurin sannan ya kalle ta har lokacin dariya yake idonshi hadda hawaye ya ce, "Ke ƴar ƙauye ce fa, Kurɓar lemo kawai nayi anace da kurɓa da turanci Sip, act ɗin kuma shine sipping" Ɓata fuska ta yi, "Shine kakemun dariya dan kawai nayi kuskure? Aikuwa ban ƙara koyan turancin ma" Rarrashin ta ya soma yi harta sakko sannan sukaci abincin suka je yawon ganin gari basa wannan pack basa wancen sai shiyoyin 9 suka lodo kaji suka nufi otel.

    Kwanan su huɗu A kd suka soma shirin dawowa gida, ba laifi sunci uwar sabada, an hau gajimare an sakko anyi lilo iya lilo, gaba ɗaya Ali ya gama ɓata Boɗɗo yama zare mata kunyar da aka bashi shawarar ya saka mata, sannan ya mayar da zolayar ta abincin sa, koda wane lokaci acikin zolayar juna suke, kwalin wayar daya ɗaura a cinyarta tabi da kallo sannan ta kalle shi cikin nutsuwa, "Yaa Ali wannan fa?" murmushi ya yi sannan ya ce, "Kukan da kikemun a gado nakeso ko bama ta re kiyita mun irinsa a waya haɗaɗɗiya shiyasa na saya miki" Sauke numfashi ta yi sannan  ta ce, "Amma kuɗin da yawa dubu ɗari takwas da hamsin, haba yaa Ali" Ɗan gajeran tsaki ya ja sannan yayi riverse tare da ɗaura wani case a kusa da wayar ya ce, "Wannan ma nakine, ki kula dashi sosai kuɗinsa zaikai miliyan biyu da ɗari biyar, sarƙar gwal ne"  kallon mamaki ta bishi da shi sannan ta ce, "Duk wannan na meye wai? Kalli booth ɗaya duk cikeda suturu da abubuwan daka sayamun beyi yawa ba kuwa?" Saida ya ɗan nisa sannan ya ce, "Raina ma fansa ne agareki Babyna, ni ɗinma nazama naki bare abinda ya ke mallaki na, inaso ki sani duk abinda na miki saboda akwai ne idan babu saidai mu haƙura" kwantar da kanta ta yi asaman kafaɗar sa yana tuƙin shikuwa ya riƙe sitiyarin motar sa hannu ɗaya ya saƙalo hannun sa ɗaya ya rungumota gaba ɗaya sai godiya ta ke masa.......

*Bayan kwana biyu*

       Gaba ɗaya gyaran gidan ake da girke gike saboda taryar me gidan dake shirin dawowa daga Nijar, uban gayyar ma yau murna ta hanashi sukuni dan kuwa ba shakka yanaso yaga  matarshi, sanda suka iso kuwa ko abinci bata ciba saida ya sakata wankan jiƙa gashi, sannan ranta ya mata sanyi ganin cewar tabbas ya zaƙu akan ya ganta. A ɓangaren Fatima kuwa takaicin da Ali ya bata ba'a magana, saboda agaban kowa ya rungume Zuwairah hadda wani ɗagata, kuma tunda ta dawo bai kuma neman ta ba har dare, zuwa wurin 8 tana kwance riƙe da waya a hannu kiran wayarshi ya shigo mata, ɗagawa ta yi a jagule ta ce, "Assalamu Alaikum" Sauke wai nannauyan numfashi ya yi sannan ya ce, "Kizo ina mota ina jiranki" Ckin takaici ta ce, "Saboda me zanzo? Ba matarka ta zo ba" Numfashi ya sauke, "Ina jiranki" ya datse kiran tare da resting bayansa akan sit na motar. Hijab ta zumbulo ta fito tana ƙunƙuni tamkar wata ƙaramar yarinya, Zaid ne ya tare ta, "Anty ina zakije?" Shafa kanshi ta yi, "Kaje wurin Momy saƙo kawai zan karɓo in dawo" "Momy bacci ta ke ta ce kar wanda ya tashe ta ma" "Kaima kaje ka kwanta kaji" Ba musu ya juya ita kuma ta fito waje, kai tsaye gaban motar ta ɓalle ta zauna sannan ta turo baki, rungumo kafaɗunta ya yi sannan ya ce, "Baby menene kuma?" Janye jikinta ta yi sannan ta ce, "Zuma ta dawo ina ruwan wata baby" Murmushi ya yi sannan ya kuma riƙota nan da nan ya cura kanshi a ƙirjinta ya soma shinshinar ta "Baby na tuba, ki gafarce ni nasan ban kyauta ba" Jan numfashi ta yi dan matsalar ita tana ƙarfin sha'awa indai Ali zai raɓeta babu shakka nan da nan zatayi laushi, dama kuma rigar bacci ce kawai acikin wannan dogon hijabin dan haka baisha wahalar samun access da manya manyan dukiyar fulaninta ta ya soma wasan caɓal dasu da forehead ɗinsa, Janye jikinta ta yi daga nasa sannan ta ce, "Ba laifn dakamun kawai ka tsaneni ne yau" Kamota ya yi gaba ɗaya, "Ban isa ba ranki ya daɗe,idan akwai ranar dazan tsani kaina to akwai ranar da zan tsaneki, kefa jinin jikina ce, gaba ɗaya bugun zuciya ta ke ce shi akan me kike irin wannan furucin" Kawai kuka ta fashe da shi, "Yanzu ya zanyi bacci yau? Tayaya zan iya bacci bayan ka sabamun" Ɗan kallon ta ya yi, "Dame kike saba? Juyar da kai ta yi, "Ba komai zanje na kwanta" Dariya ya kuma yi "Kiyi haƙuri Zuwairah nanda kwana uku zasu wuce ita da yayarta zataje checup kuma wata ɗaya zatayi, idan ta tafi da kwana uku muma abuja zamu tafi musha madara abunmmu, muyita kuka muna lilo" Shiru ta yi zuciyarta yana mata zafi, kenan haka zata dawwama da ɓoyayyen aure, haka zata dawwama dabkewar mijinta a duk sanda kishiyarta ta ke kusa, cikin rashin kuzari ta ce, "Zanje na kwanta kaji" Ya fahimci wannan bazai mata maganin damuwar ta ba ya sanya ya mata sallama kawai ta tafi.

    Wuraren sha ɗaya na daren wannan ranar ya shiga ɗakinta, gaba ɗaya ya rasa sukuni, banda tausayinta ba abinda yake, shida yake namji ya shiga damuwa, ya tabbatar karatuttukan daya zube a kanta dole ta nemi yin bitarsu akan kari, yana tausayin ta akan komai ma, akan gadon ya zauna ita kuwa dama ba bacci ta ke ba nan da nan ta nemi kurma masa ihu, da sauri ya riƙota a hankali ya ce, "Baby Ali ne fa" Sauke numfashi ta yi sannan ta ce, "Amma meya kawo ka?" Bai tsaya ɓata lokaci ba ya haɗe bakinsa da nata.......basu suka farka ba sai ƙarfe bakwai na safe, ba shi ba hatta Boɗɗo ta shiga rikici dan batasan dayaya Ali zai fita waje ba, ga gidan akwai mutane a waje yanzu, bama wannan ba yaya zaiyi da Zuwairah? Dan kuwa tabbas tanacen  yanzu tana jiran dawowar sa!!!

Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon