SHAFI NA ARBA'IN DA UKU

338 62 4
                                    

  *GINI DA YAƁE* FREE BOOK

                    EWF
  
      *BILLY GALADANCHI*

43.

   Baffa tunda ya ƙyalla ido ya ga kayan arziki yake zarya a ɗakin su Fatima, yauma kamar ko yaushe da leda ya shigo a hannunsa yana washe baki tamkar gonar auduga, a jikin ƙofar ɗakin ya tsaya ya yi sallama, Fatimace kaɗai a ɗakin ta yi hanzarin ta sowa ta re sa gayar da shi, ledar hannun sa ya miƙa mata sannan ya ce "Bado ne Phatoum na sanki da son bado tun kina ƙarama, shiyasa yanzu ina gani na saya na ce barin rugo in kawo miki masu ciki da son ƙwalama" Murmushi ta yi sannan ta dinga godiya tamkar ya bata duniya harya juya ya tafi, yanaji a ranshi bai kyautawa yarinyar nan abubuwan daya mata tun tasowar ta, an daɗe ana zunɗen sa akan cewar dalilin abinda ta aikata ya sanya ya ke ƙara tsiyacewa kowa yanada wutar lantarki bandashi sai gashi yau ata dalilinta yana ganin wutar da ba ko ƙwandalar sa a ciki, anya ya yiwa yarinyar nan adalci kuwa? Ko da baya morarta yana gani lokaci ya yi dazai sassautawa al'amarin ta. Murmushin fuskarta bai gushe ba har ta zauna ta ware ledar, ta ƙurawa Badon ido tana tunani rayuwar ƙuruciyarta dukda batada wayau sosai, duk sanda zai fita zai kawo mata wani abun marmari, lumshe idonta tayi tana fatan wannan farin cikin datace ciki ya ɗaure har abada.

*Bayan wata biyu*

      Duk wani abu daya dace ayiwa Zuwairah an mata kuma alhamdulillah ta samu lafiya fiye da tunani, ta murmure tamkar ma ba ita ba, wanda ya santa a da yana kallonta yanzu zai tabbatar ta dawo ita ɗin, tana samun tsananin kulawa awurin mijinta gaba da baya. Tunda sukaga kansu a Nigeria bai samu sukuni ba saida ya kimtsa tafiya Niger, dukda yasan ance ba'a bari yaga matarsa amma wanan aganin sa magana ce ta kawai, bashida burin daya wuce ya sanya Fatima a idonsa, a rayuwa yayi tsananin kewarta fiye da tunanin duk wani mai tunani, Tare da Zuwairah suka je har garin nasu Fatima. Durƙushe take tun daren jiya saboda azabar naƙuda an tilasta mata sauka akan gwiwowinta yayin da hannayenta suke akan kujera ƴar tsuguno ta tsuguna! Dukda yanayi irin na damina an samu ruwa a daren jiya laima ta sauka, kuma har wannan lokacin akwai haɗaɗɗen hadari da ya ke shirin sauka sam hakan bai hanata tsiyayar da zufaba, gwiwowinta sun sage ainun ta gaji matuƙar gajiya,idonta har wani lumshewa suke saboda azabar datake sha maƙoshinta ya bushe amma an hanata ruwa tun daren jiya kana wani ƙyallle ne aka toshe bakinta dashi wai kar tayi ihu ajiyota, tayiwa mahaifiyar ta da unguwarzomar wani kallo sannan ta langwaɓar da kanta, ana haka Zuwairah ta shigo da sallamar ta, Inna ta mata kallon wulakanci sannan ta amsa kana ta ɗauke kanta, mamaki ya kama Zuwairah ta ce "Baiwar Allah dan Allah Boɗɗo nake nema ko tana nan?" Kallon ta matar ta yi sannan kamar wacce ke jira ta ce, "Bazaki samu ganinta ba dan kuwa tun daren jiya take gurfani kuma abu yaƙici yaƙi cinyewa haihuwa ta gagara, har yanzu tana kan gwiwa da ɗaurin baki, tana ɗakin uwart, ta nuna ɗakin da hannun ta sannan ta ci gaba, "Kuma Uwar ce acikin abun Kunya da Unguwarzoma" Dukda Zuwairah bata gama fahimtar insa aka dosa ba hakan bai hanata tunanin haihuwa bace sa sauri ta nufi ɗakin ta re da faɗawa lokaci guda  tare da sallama, kareta Unguwar zoma ke ƙoƙarin yi yayinda idon Zuwairah yakai kanta ita kuwa cikin tsananin neman ceto ta soma miƙo mata hannu, wara ido ta yi sannan ta ce, "Kuyi haƙuri ni abokiyar zamanta ce, amma naƙuda take haka, meye wannan dan Allah?" mahaifiyar Fatima najin haka ta miƙe ta re dajan hannun Zuwairah wa je, saida suka isa tsakar gidan sannan ta ce da ita, "Tana yunƙuri ne baiwar Allah, kiyi haƙuri ba'a shiga, ga abin ya zo da ruɗani tun jiya da safe take sama sama zuwa dare ta kasa a haka muka kwana" Da sauri Zuwairah ta juya cikin tashin hankali ta isa wurin Ali, yana jingine jikin mota ta sameshi sannan ta ce, "Munshiga Uku yaa Ali, kaga halin da Fatima take ciki kuwa, tun jiya wai take naƙuda har yanzu bata haihuwa ba, kuma acikin gida....kafin ta ƙarasa ya fece aguje sai bayanshi tabi suka shiga cikin gidan, juyin duniya yayi abashi matarshi aka ƙi saida ya bore tare afkawa ɗakin, kallo ɗaya ya mata ya kasa riƙe hawayenshi! Bai ɓata lokaci ba wurin ɗaukarta duk yanda mahaifiyarta ta so nuna masa basa haka bai saurare ta ba, Zuwairah ma kuka ta keyi saboda tausayinta, Inna ce ta tare mai ƙofa ya kalleta ɗauke da Boɗɗo a hannu cikeda ta takaici ya ce, "Baiwar Allah meye haka?" "Wlh yanda suka saba abun kunya bazasu ƙara lalata mana sunan zuri'armu ba, babu inda zakaje da ita, kafiri kawai" Ƙafarshi ya saka ya banke ta da ƙarfi yayi waje suka afka mota kai tsaye asibiti suka nufa inda likitoci suka tabbatar masa  ruwan da baby yake ciki ya tsiyaye kuma basaji ma zata iya haihuwar da kanta, sannan saidai yaje asibitin galmi saboda su wannan ƙaramar asibiti ce, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana shine ya ziyarce sa, haka ya karɓi transfer letter suka juya ga kuma galmi garin da nisa... Koda suka ƙarasa asibitin ta gama fita hayyacinta gaba ɗaya, dan haka a emergecy suka karɓeta zuwa dubawa sai ambaton Allah takeyi... Basuda zaɓin daya wuce suyi mata CS dan haka akayi hanzarin booking emergency CS, cikin sa'a aka ciro mata yaronta Namiji kyakyawa dashi ƙato sosai. Matsalar ɗaya ce jini yaƙi ya tsaya, anaji ana gani banda zubar jini babu abinda takeyi...

  Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now