SHAFI NA UKU

498 66 3
                                    

*GINI DA YAƁE*    FREE BOOK

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
      Et4dtsswɗwtssɗDsɗdeèƊdwwɗde                (E.W.F)
     
 

     *BILLY GALADANCHI*

SHAFI NA UKU. 3

    Zufa ce ta karyowa  Hafizu sanda yake saurarar Ali akan zancen ƙin samun wayar baturen kwata kwata, jikinsa ya shiga karkarwa sannan cikin tashin hankali ya furta, "Nafi tsammanin wata matsalar aka samu yallaɓai, amma Mr Okafor ba yau na saba kai masa kayaba batare dama ka sani ba, kawai manyan kaya ne kawai bai taɓa saya a guna ba amma tabbas mun saba harkar cinikayya sama da shekaru biyu da suka wuce" Ɗage gira ɗaya Ali ya yi sannan ya furta, "Hafizu kanada saurin mantuwa, gaba ɗaya ka manta da cewar Mariri ma mun saba hurɗar kasuwanci dashi, kawai fa ɗaga mana ƙafa suke saimun zurma saisu zanje, gaba ɗaya duk yanda naso in lissafa abubuwan da suka faru suɓucemun sukeyi gaba ɗaya,sama da shekara goma ina wannan harkar ko daidai da rana ɗaya bamu taɓa samun matsala makamanciyar wannan ba sai wannan lokacin, ina roƙon Allah  sassauci akan waɗannan miyagun ƙaddarorin dake bibiyar rayuwata" Hannu Hafiz yakai ya share gumin fuskar sa sannan a hankali ya furta,

"Innalillahi wa inna ilahirraji'una" Shiru dukkansu sukayi na wuccin gadi sannan daga bisani Ali ya ce,

"Asara dakake ganinta Hafizu idan batado ranko zuwanta mai sauƙi ne, babbar fitinar baifi zuwan asara inda za'a biyoka bashin da baka hanyar biyanshi ba, lokaci yayi dazan sayar da kadarorin dukda na mallaka in biya banki kuɗaɗensu danni harga Allah tozarci kiwane irine bana buƙatar sa a rayuwata" Hafizu shiru ya yi bashida bakin magana sama da mintuna bakwai sannan ya ce, "Ali nima zan sayar da nawa mu biyasu, wannan faɗuwar tare muka yita dakai bawai kai kaɗai ba, bance nine sliar shiga wannan halin ba amma tabbas na zama wani yanki daga jikinka danake ga lokaci yana gab da ƙarasowa da zamu gudu tare mu kuma tsira a tare"  Shiru shima Ali yayi na wasu daƙiƙu a halin yanzu idan ya ce baya buƙatar taimako ƙarya yakeyi, taimakon gaggawa yake buƙata wanda zai sallama wannan sana'ar ya nemi wata duk abinda za'a shiga baza'a fitaba gwanda ya haƙura dashi.

"Hafizu bawai naƙi ta taka bane amma banaji saka hannunka da dukiyarka shawara ce mai kyau, ka bari kawai da kaina zan sayard a wasu kadarorin na biya rabin kuɗin rabin kuɗin sainaja wata harkar munata addu'a inshaa Allahu Allah zai saka mana hannu" Cikeda damuwa Hafizu ya musanta masa amma gaba ɗaya bai sauraresa ba. "Ina gargaɗinka akan hakan, ka adana abinda yake mallakinka banaci gauraya acikin ƙaddarata daidai ne a wannan lokacin" Shiru Hafizu ya yi bai kuma magana ba amma acen ƙarƙashin zuciyarsa yaji daɗi sosai da Ali yaketa rejecting offer ɗinsa (Ƙin karɓar tayinsa), saboda shishi kaɗai abinda yake ransa akan wannan dukiyar dayake da wacce ko rabinta bai gayawa Ali yanada, dan tabbas ya fahimci Ali kariyar arziki ce tazo masa wadda babu wanda ya san ranar da zata tsaya dukda haka yana nan tare dashi iya wuya!

    Yanda Ali ya faɗa haka ya yi kaso biyu acikin dukiyarshi ya saida aciki hadda wasu manƴa manyan motocin sa guda biyu ya zamu ya baiwa banki rabi da kwatar abinda ya karɓa a hannun su, dukda sunso mayar masa akan ya biya a hankali amma haka ya kafe saboda bayason fitina yana fatan ƴa samu warwarewar al'amura kafin nan zuwa wani lokaci ya ƙarasa biyansu kuɗaɗensu asirinsa a rufe. Sauran kuɗin dake hannun sa ya shiga harkar dazata fishsheshi.
  Amirah tunda taga ana sayarda kayan dasuka shafi gidansu take ƙunci, daidai da Ma'ma da kuma Abdallah masifa suke faman sha a wurinta. Yauma kamar kullum  bayan Ali ya tashi daga wurin aiki kaiɓtsaye gidansa ya nufa, saidai bata sauya zani ba fuskar Amirah tamau ta kwaɓa ado iya ado zinari ne ajikinta tun daga kan kunnenta wuya har zuwa ƙafarta, murmushi ya yi sannan  ya ware mata hannayen sa alamun ta shiga ƙirjinsa, wani taɓe baki ta yi sannan a hankali ta gangara kusa dashi ta faɗa ƙirjinsa a wulaƙance, zame jikinta ta yi sannan ta ce,

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now