SHAFI NA BIYU

631 73 4
                                    

            *GINI DA YAƁE*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                      (E.W.F)
     
       *BILLY GALADANCHI*

SHAFI NA BIYU

02.

Yusrah rai a ɓace ta isa gidan, duk irin gaisuwar da Zuwairah ta yi mata bata amsa ko ɗaya ba saboda ta ɗauka da zafi. Zuwairah sosai ta shiga hankali hakan ya sanya ta sameta a ɗakin dayake mallakin ta acikin gidan, zama tayi kuda da ita amma bata ko kalle ta ba, Zuwairah cikin tsoro ta shagwaɓa da sanya kuka mai taɓa zuciya abinda nan da nan ya tashi hankalin Yusrah ta yi kanta da sauri tare da riƙe hannayen ta duka biyu, "Zuzu zaki fara ko? Meye abin kuka anan to? Idan sabida ina fushi ne ya wuce kinji, me kikeso yanzun nan in miki" Hannun ta ta zare daga cikin na yayar ta a hankali takai bayan hannun nata ta share ƙwalla sannan ta ce cikin muryar kuka,

"Sanda bakya nan Haidar shine ya tsayamun agarin nan, bance haidar bashida laifi ba tabbas ya barmin tabon da har in komawa Allah bazai goge a raina ba, amma karki manta kana tuna alkhairin mutum so dubu sannan ka kawo sharrin sa ɗaya, idan haka ta kasance yafiya akeso yaa Yusrah" Jinjina kai Yusrah ta yi dukda bazata taɓa fita harkar Haidar ba amma a sarari sai ta ce, "Shikenan ma Zuzu tunda har hakan kike ganin ya dace bazan ƙara komawa ta kanshi ba, mu manta kawai" Rungume yayarta ta yi sannan a hankali ta furta,

"Yaa Yusrah ada Haidar  yana matuƙar sona, yanzu baya sona, nikuwa shekaru takwas da rabuwa da Hidar har gobe ina sonshi, Yaa Yusrah dan Allah ki nemomin shi ya soni" A hankali Yusrah take shafa bayanta cikin ƙunan rai, ita 'yar duniya ce taga jiya takuma ga yau ta, Haidar bai cancanci 'Yar uwarta ba ko kaɗan amma a hankali sai ta furta,

"Zuzu my love, inshaa Allah zai dawo gareki kinji, aishima yana sonki days ganni ya zata ke ce yace kamar ya sanni saboda muna kamanni kinga bai manta dake ba ko?  Murmushi ta yi sannan ta ce, "Allah ko Yaa Yurah? Idan ya dawo gareni zanyi farin ciki, bazaki ƙara gani ina kuka ba" Rungumarta sosai ta yi dukkanin su babu wanda ya kuma magana.

****************
   Shiru dukkansu na wani ɗan lokaci, ko wannensu da abinda zuciyar sa take saƙa masa akan abinda ya samesu, Hafizu abokine awurin Ali Haidar tun suna yara, shi bashida ƙarfi kuma baiyi wani karatu mai zurfi ba kamar Ali, shiyasa ya janyoshi ajikinsa ya mayar dashi babban yaronsa kuma ya bashi damar komawa makaranta harya samu damar kammala digirinsa na farko a fannin Education Economics, kafin daga bisani ya bashi matsayin manager a kampaninsa na sarrafa takalmin silipas da kuma harkokin shige da fice na tafarnuwa da citta zuwa ƙasashen ƙetare inda suke kawo masa riba sosai. Ali ya aminta da adalcin Hafizu fiye da ƙima wannan ne dalilin dayasa komai nashi Hafizu ya sani. Nannauyar ajiyar zuciya Ali ya sauke sannan a hankali ya furta,

"Wannan asaran ba komai bace ba idan mukayi la'akari da yanda mafarin dukiyar yazo, Allah shine ya yi mun wannan buɗin a lokacin da banyi tsammanin samuwar sa ba, yanzu kuma danya amshi ajiyarsa bazan butulce masa ba a hakan ma alhamdulillah da ni da duk wani wanda ya raɓeni yaci daga taskar ubangiji daya bani aro, Alhamdulillah ina godiya mai ɗimbin yawa daya jarabceni da abinda zuciya da ruhi zasu ɗauka, lafiyar ita ce jarina kuma tunda inada ita zanyi amfani da lafiyar wurin jajircewa neman na halak daga yanzu har abada." Hafizu kafeshi da ido ya yi na wani lokaci sannan a hankali ya ɗauke dubanshi daga kanshi ya mayar zuwa wani ɓangaren daban, Cikin jinjina ya ce,

"Haƙiƙa acikin mutanen dana taɓa tarayya dasu ban taɓa cin karo da nagartacce irinka ba Aliyu Haidar, gaba ɗaya ka shallake inda nake tunani, ina yawan jinjinawa imaninka Ali, kanada addini sosai da yawan riƙo da addini kana yawan son yin sallah a jam'i akan kari kai mutum ne dake yawo da azumi a baki kowane lokaci, ka jarabtu da abinda yake raunana imanin wasu amma kai sai naga gaba ɗayanka imanin naka ƙara ninkuwa yayi, wlh juya ban runtsa ba inama nine kai? Wlh dana more abina" Murmushi mai ƙarawa fuskarsa kyau ya yi sannan ya ce,

GINI DA YAƁETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang