SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS

356 72 8
                                    

*GINI DA YAƁE* FREE BOOK

EWF

*BILLY GALADANCHI*

28.
Tsaye kawai ya ganta ajikin ƙofar kitchen ɗin, ita kuwa margewa ta yi, sanan ta yi hanyar dazata sadata da ɗakin ta, kasa haƙuri ya yi a hankali ya ce, "Fatima" Tsayawa ta yi sannan a hankali ta waigo, murmushi ya sakaya a fuskarsa sannann ya ce, "Fatima babu gaisuwa a tsakanina danke ne kuma?" Murmushi ta sakar masa sannan ta ce, "Kayi haƙuri dama na bari ne sai idan na samu zama in tambayi anty Zuwairah izinin gayar da kai" Gyaran tsayuwar sa ya yi sannan ya harɗe hannayen sa wuri ɗaya, "Ban fahimci abinda kike nufi ba sam" Zuwairah data fito daga part ɗinsu tana jiyo abinda Fatima ke faɗa ta ce, "A ban aminta ki riƙa gayar da mijina ba, kamar yanda ban aminta ki zaunamun agida ba, ki tattara yanaki ya naki ki koma ƙasarku tunda kin samu lafiya dama ita kika zo nema." So ta yi tay shiru amma saita kasa haƙuri ganin Ali baice komai ba ta ce, "Banaji da sisin kwabonki aka gina gidannan, bakuma naji akwai wuƙar dakike da ita duk duniya da zaki saka ki yanka zumuntar dake tsakani na dashi, ki sani koshi dayake mallaki da iko da gidansa bai isa ya koreni ba nan ɗin gidana ne, bare ke da kika zo, idan kuma ya isa gashinan ya koreni koya maimaita kalaman da kika furta yanzu." Cikeda mamaki Ali ya ke kallon Boɗɗo wai dama fatima batada kunya ashe? Kafin ma wani ya samu damar cewa wani qbu acikinsu Boɗɗo ta yi gaba, da sauri ta rufo ƙofar palon tare da manna mata key ta dafe ƙirji bayan ta jingina a jikin ƙofar, a ranta ta ce, 'Anya zan iya wannan rashin ta idon da Baraka ke so nayi, wlh fa ina tsoron Yaa Alin nan karya mazgeni a banza.' gaba tayi zuwa toilet dama ta idar ne ta fito ta yi wanka saboda tsaro! Zuwairah zuwa ta yi suka fuskanci juna da Ali sannan ta ce, "Honey kana tsaye fa? Kanaji kana gani yarinyar nan ta gaggaya mun magana ta wuce ciki, ni wlh yauyau ɗin nan saika koreta inba haka ba zanbar gidan." Ta ƙarashe maganar da alamun shagwaɓa, Riƙo hannun ta ya yi suka shiga falon su zannan ya zauna ya ɗaura ta akan cinyar sa ya fara magana da harshe mai taushin gaske. "Honey Boɗɗo da kikaga tana wannan iya shegen dama ce a hannun ta, wato yarinyar marainiya ce, kuma Hajiya Umma ita ce mariƙiyar Boɗɗo, amanar ta ta bar mini tare da roƙona akan in riƙe ta, kinga saɓawa iyaye ba daɗi, ki tambayi Boɗɗon har cewa na mata idan muka dawo zan maidata Niger, amma Hajiya Umma kuka ta sakamun a waya dole na haƙura, yanzu kiyi haƙuri akan wannan rashin kunyar da ta miki zan mata horo mai tsanani, ke kuma ki daina biyewa shirmenta kinga abinsa nakewa gudu nan, ta zo a banza ta nemi raina miki wayau bayan ba sa'arki ba ce, ki sani ni Ali babu wata mace agaba na face ke, shin kinsan idan kina nuna mata ta isa in dube ta shiyasa zatake kallon kafaɗarku ɗaya? Ki nuna mata mijinki yafi karfinta shikenan fa anwuce wurin" Nisawa ta yi sannan ta ce, "Naji amma ni ka raba mana wurin zama in daina ganin ta kwata kwata" Saida ya yi jim sanman ya ce, shikenan zan barki kike amfani da kitchen na part ɗin nan da ƙofar nan ita kuwa saimu rufe ƙofar lubbyn dake sadamu kawai ma sukeyin abincin su mu kuwa muci karen mu ba babba ka anan me kika ce?" Rungumeshi ta yi cikeda so sannan ta ce, "Nagode My love." Shi ɗinma rungumarta ya yi amma ilahirin hankalinahi yana gun Fatima, yanaso ya san meke kan yarinyar ne? Bayan haka ta ina zai fara ne! Saida ta nemi izinin zuwa ta shirya sabosa tanaso ta je kotu sannan ya sake ta, har Allah Allah ya ke ta fita, aikuwa fitar ta ke da wuya ya nufi part ɗin Boɗɗo.

Tunda ta fito wanka take zaune akan dressing chair tana saƙawa da kuncewa har lokacin da yazo jikin ƙofar falon data ɗame da key yana knocking, ta zata Baraka ce dan haka ta banzatar a zuwan saita kammala tunda yaran datake kulawa dasu sun tafi makaranta, jin knocking ɗin yaƙi sassautuwa ya sanya ta miƙe ta gyarawa towel ɗin jikinta zama a ƙirjinta sannan ta tako ta baro ɗakin ta buɗe key kawai bata buɗe ƙifar ba ta juya abinda tana mita, "Kefa Baraka bakida kirki wani zubin, ina na ce ki barni zanyi bacci zuwa ƙarfe goma shine zaki dame ni da dukan ƙofa." Jin da yayi shi kuwa an ɓalle key ɗin ya sanya shi turo ƙofar ya shigo da sallama saidai kuma bataji sallamar ba saboda masifar datake da Baraka, amma yanayin ƙamshin wurin ya sanya ta yi azamar waigowa ganin shi a tsakiyar falon ya rikitar da ita nan da nan ta nemi hanyar shigewa ɗakinta, shi kuwa da azama yayi taku uku ya riƙita gaba ɗaya, cikin tsananin jin kunyar yanayin daya risketa ya sanya ta soma magiya, "Ba guduwa zanyi ba hijab kawai zan sako dan Allah ka bari in saka in dawo" Bai ce komai ba hakanan kuma bai sake tan ba, shiru tayi tana sauraren hancin sa akan wuyanta yana shinshina saikace wani maye, yafi 1mns a haka sannan ya sake ta amma bai sake hannayen ta ba, kasa kallon idon shi ta yi ta saukar da ƙwayan idon nata a ƙasa. "Ki sako hijabin kizo zamuyi magana." Kallon sa ta ɗanyi tana ayyana a ranta yanda zata juya ta isa ɗakin yana mata wannan kallon, cikin rashin kuzari ta ce, "Am ko zaka fara fita gaba ɗaya zan sako kaya saina sameka part ɗin ka" Ɗage girarsa ɗaya ya yi sannan yaja hannunta zuwa bedroom ɗin, "Muje zan tayaki saka kayan ma." Batace masa komai ba dan batada abin ce masa, abu ɗaya ta sani Baraka ta sanar mata duk sanda irin wannan chance ɗin ya zo karta ɗaga ƙafar ta, amma ta ina zata fara? Har tsakiyar ɗakin yajata akan gadon ya zauna sannan ya direta akan cinyoyin sa, hannunta dayake riƙe da shi ya soma murzawa a hankali, sannan ya zagaye waist nata da ɗayan shi ɗinma bawai hutawa yayi ba sai yawo yake dashi akan tiny waits ɗinta dukda acikin towel ya ke, "Fatima dama na zone muyi magana akan abubuwan dasuke faruwa tsakanin ki da Zuwairah, nasan ke ce babba agidannnan amma kuma a shekaru zuwairah ce gaba da ke, dan Allah ki daina gaya mata magana yanda duk kika so." yanzu kam juyowa da fuskarta ta yi gaba ɗaya ta zuba masa idonta da suke da kamada ɗanyan zinariya nan da nan ƙirjinsa ya soma dokawa, ya soma ƙoƙarin fita hayyacin sa hannunta ta ɗaura akan wuyarsa tana shafawa a hankali tare da sakin murmushi, tanaso yanda ya shafa mata wuya a india abun ya yi tasiri a kanta shima ta fara masa ta nan, "Daga lokacin da ka ɓoyewa matarka wacece ni a wurinka daga lokacin na rage ganin ƙimarka sabosa namiji baya haka, idan tunani kake cewar asirinka zai ci gaba da ruhuwa har abada to kayi kuskure, shirin da kake na sakina a sirrance bazai magance matsalar ka ba dan wata rana babu shakka saita fita koda bayan mun rabu ne kamar yanda kake muradi. Dakatawa ta yi da magana yaci gaba da shafa wuyansa har baya tana wasa da sumar datayi luf a bayan ƙeyarsa, saida ya soma marmaɗi da fatar idon sa sannan ta yi saurin cewa, "Dama nice zan gayawa hajiya Umma na fasa da aurenka to yanzu na fasa gaya mata hakan, kawai ni a duniya babu abinda nakeso sama da auren nan, kuma idan ka ce zaka sakeni akan tilas zan gayawa Hajiya Umma duk abinda ya faru, bance ka soni ba dan babu wannan a tsari na, na baka labarin rayuwa ta banida masoyi ko ɗaya sai Hajiya Umma na, ita kaɗai ta ke sona sai kuwa Hajjo da Baraka a yanzu, bazanyi butulci ba Zaid da Baby ma suna sona, koda yake Marwa da Arwa ma suna ji da ni, ashe kaga kuwa masoya na suna Nigeria ni ina Niger acikin ƙunci shekara da shekaru yanzu maizai mayar dani? Waɗannan kaɗai sun isheni zaman rayuwa." Ta shi tayi daga kan cinyarsa ta ranƙwafo tare da tallafo fuskarsa da hannayen ta duka biyu, "Yaa Ali idan so kake inwa matarka biyayya wlh bazanyi ba, koda zaka yankani ne acikin gidannan, bata isa ba, karka riƙa mun kallon mara wayau dan nima inada wayau na, shiru shiru da rashin walwalar da kake gani a fuskata damuwa ce, kaine ka kawo haske a rayuwata na da taimakonka Allah ya bani ikon sake buɗe ido a rayuwa ta, tayaya zan barka? Na jingine duk wata damuwar dake addabata a gefe na rungume ka Yaa Ali na, shikenan ka barni da ita kowa tashi ta fisheshi." Idon sa ya sauke akan jinyoyinta da suke haɗe sabosa yanayin duƙin datayi ɗan mutsilin towel ɗin ta ya buɗe a wurin, hannu ya kai ya shafi shinyoyin ta, abinda ya so ya rikita itama nan da nan ta sake mai haɓa taja baya, riƙo towel ɗin nata ya yi da sauri sai kawai ya zame ya biyo hannunsa, da sauri ta tsuguna a ƙasa tana kakkafe ƙirjinta da hannayenta, ta runtse idonta gagam, Takowa ya yi ya tsuguna kusa danita tare da rufa mata towel ɗin ta a bayanta ta rufe jikinta, miƙewa ya yi ya juya bayan sa, "Ki gyara towel ɗin" ganin ba ita ya ke kallo ba ya sanya ta yi sauri miƙewa ta na ƙoƙarin ɗaurawa, saidai tas ya gama ƙarewa surarta kallo a madubin dayake fuskanta kafin ta gama ɗaura towel ɗin cikin rawar jiki, waigowa ya yi gaba ɗaya ya fizgota ta faɗo jikinsa, nan da nan jikinta ya soma rawa, rashin kunyar data gama hadda awurin Baraka dukta fita a kanta, shi kanshi ya kula da yanda ta ke karkarwa, idonshi sunyi jajir abubuwan suna neman tasowa, abarshi sai tsargi take tana harbawa sauri da sauri, duk harbi ɗaya yana bata damar kara miƙewa tsangam! Idanta ta zuba a nashi cikeda tsoro tana sauraron ta ga me zaiyi kalmomin Baraka suna mata ya wo, "Ke cikakkiyar budurwa ce, kinfi ƙarfin rani daga ranar da kika miƙa masa budurcin ki zakiga martbarki ta ƙaru a idon sa da kimar ki" a ranta ta ce, 'Ina budurci a tattare da ni,ina wata martabar bayan ya gama sanin banida budurci? Ina budurci bayan nayi naƙudar yaro ba kulawa, ina abin yake na nunawa bare karɓar martaba?' Tana wannan tunanin kawai taji hannunsa akan dukiyar fulanin ta ya zare mata towel, runtse idonta ta yi tare da ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ina yanaso yafi ƙarfin ta, da ƙyar ta zare jikinta tare da neman hanyar toilet, bashida kuzarin wani binta dan haka ya tsaya harta shige, nan da nan marar sa ta soma aiki data saba, dafe wurin ya yi tare da ƙoƙarin juyawa amma ina zuciyar sa tabi abinda take kwaɗayi, juyawa ya yi har zuwa ƙofar toilet ɗin yana dafe da marar sa ya ce, "Dan Allah ki taimakeni, banida lafiya ne idan banyi ba zan mutu." Nan da nan ta tuna irin wannan muryar tare sa irin wannan maganar a shekarun baya ƙirjinta ya yi mummunnan dokawa, tana shirin buɗe ƙofar ta kalleshi da kyau ta ji muryar Baraka tana ƙwala mata kira, shi ɗinma ganin Barakar ya sanya a daddafe ya fita sai kallon shi take ta zata wani abu ke damunshi sai jeremai tagwayen sannu ta ke amma bai saurare ta ba ya fita dafe da mara!

Nan da nan idanuwan Boɗɗo suka firfito, hankalinta ya tashi a ranta tana ayyana shin wanene Ali? Bata ƙaunar zarginta ya tabbata akanshi!

Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora