SHAFI NA TALATIN DA TARA

387 64 4
                                    

*GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                     EWF

    *BILLY GALADANCHI*

         39.
Tai makon gaggawa aka bata amma itama gasha wahala, saboda ciwon ciki ne ya murɗe ta tamkar zata sheƙa lahira, haka da ƙyar akayi tattalin cikin da likitoci ma basuda yaƙinin zai tsaya, haka abata allura annan kowa ya kwana ranshi ba daɗi. Zuwairah tunda safe ta dawo asibitin ita da Ali, koda sukazo tanajin sallamar su ta rufe ido har saida ta ji Ali ya fita zuwa wurin likita, sannan ta buɗe ido, dama sunzo ne Hajjo data kwana ta tafi gida itama bata ce mata komai ba, cikin fusata Zuwairah ta far mata, "Boɗɗo akace shekarun ashirin da biyu anya ba'a miki ƙarin shekaru ba kuwa? Banda wowta da rashin hankali a ire iren mutanen da suka faɗa irin ƙaddarar da kika faɗa nawa ne suka samu gatan da kika samu? Nawane suka rayu? Nawane suka auru? Idan har kinsha fama da baƙin ciki ya kamata ki sani yanzu lokaci ne da Allah ya kawo da zaki huta, mijinki yana sonki, yana kulawa da ke tun kafin sanin cewar ke matar sa ce na tabbatar wa kaina Ali yana sonki, ya na miki hidima  ashe bazaki godewa Allah ba? In banda wowta mijinki kike gaggayawa magana, idan ma kinji haushin shi aiba haka akeyi ba, ni kaina munYi haka dashi idan baki sani ba ki sani Baby 'yar Ali ce kuma bada aure muka haifeta ba, hasalima bayan ya gama sheƙe ayarsa dani ban kuma jin labarin sa ba sai bayan shekaru takwas, akan wanan raɗaɗin na kamu da ciwon zuciya amma yanzu ba komai ya wuce ba, yana daga cikin mazaje masu adalci wlh, danshi ba mazinaci bane ba kawai cuta ce ta sameshi ya kasa samun waraka yake tafka shirme a baya, ni a matsayina na abokiyar zamanki kuma yayarki danna girmeki, ina baki shawara maza ki baiwa mijinki haƙuri kuma ki janye wannan Allah ya isan dan idan da cutar sonki kadai aka barshi wlh yaga sakyya, jiya ko bacci baiyiba a tsaye ya kwana, magidanci babba irin Ali saigashi yana kuka, aikuwa ya cancanci yabawa agareki ko Boɗɗo, kuma wlh kiyita istigfari dan wuyar da kika sha abaya kinyiwa Allah izgili na cewar zaki zubda ciki, gani inason haihuwar an hanani ɗaukar cikin saboda ciwon zuciya ni ince me to?" Ido ta sauke ƙasa sannan cikin rauni ta ce "To Anty dan Allah kiyi haƙuri" "Kiban haƙuri ni me kikamun? Shi yayan naki dai idaN ya xo ki bashi haƙurin kuma ki tabbatar kin tubarwa Allah, fushin fari aiba naki ba ne ba" Shiru ta yi aaida anty Zuwairah ta gama mata faɗa sannan ta dawo nasiha aoaai saida ta yi kuka sannan ta sassauta mata, Ali kuwa bai ƙara dawowa ɗakin ba har yamma hasalima ficewa ya yi daga asibitin tunda ya ji halin datake ciki sa sauƙi, daren jiya bai runtsa ba amma ya shaƙa sosai abinda ta masa, ya fi kowa sanin cewar bai kyautawa Boɗɗo ba amma me kenan ita ta aikata? Ashe bazata karɓi ƙaddara ba saita saɓi Allah? Kuma ma yanzu meye amfanin abinda ta yi acikin asibiti? Da wannan kawai ya saka a ransh bazai biye mata ba, san haka har Zuwairah ta koma gida bai dawo asibitin ba sai wuraren ƙarfe tara. Da sallamar sa ya shigo ɗakin inda Hajjo ta soma barkwanci tana masa wasanni ya ɗan biye ta,Baraka ma ta gayar da shi ya amsa Boɗɗo kuwa kunyar sa ta hanata buɗe idonta, shi kuwa daga tsayen ya ce da Hajjo, "Ya jikin ta? Saida ta kalleta sannan ta ce "Da sauƙi sosai, amma har yanzu sun hanata motsawa ma saidai komai a mata, ko me zatayi basa bari ta yi tafiya da ƙafarta ko nan da cen" Shiru ya yi na wasu daƙiƙu kafin ya ce, "Ba damuwa, Allah ya bata lafiya, da wani abinne ko in tafi kawai, ga kayan marmari nan na kawo naku da nata, sannan akwai gashashiyar kaza ita ɗinma biyu ce ku ɗaya ita ɗaya a tabbatar taci abinci sosai"

"Ba komai zaka iya tafiya, amma bakwa buƙatar ganawa mu baku wuri?" Kallon wurin datake ya yi ya tabbatar idonta biyu, bazata buɗi baki ta gayar da shiba ke nan ko ciwon a bakinta ya ke? Tsaki ya ja siriri sannan ya juya ta re da cewa "Hajjo saida safe" Miƙewa ta yi sannan ta ce, "Ba anan zan kwana ba Baraka ce zata kwana anan, dama direba nike jira"
"To muje itace kalmar daya furta sannan ya ƙara gaba.
   Nan da nan Boɗɗo ta shiga ruɗu, hankalinta ya tashi yaa Ali ya ɗauki zafi kenan bazaima kulata ba? Kenan ta mishi laifin dazai kasa budar bakinsa ya tAmbayeta lafiyar jijinta? Haka duk yawan maganar da Baraka ke mata bata kulata ba, sai da sukayi sallan asubahi sannan ta daure ta baiwa Baraka labarin rayuwar ta kaf cikin aminci ta ƙara da cewar "Baraka tunda na ke adai mutanen dana buɗi baki na baiwa labarina ke ce ta uku, daga mahaifiyar Ali sai Alin saikuwa ke, abinda ya faru a asibitin nan wlh zuciya ta ce ta taɓu, meyasa sanda na bashi labari bai sanar da ni gaskiya ba, me yasa zai bari in fara sonshi sannan kuma mema ya sanya ya gagara neman yafiya ta tun a baya?.... Nisawa Baraka ta yi sannan ta ce, "Amma dukda wannan duk wannan abin? Me yayi zafi, akanme zakiyi masa wannan tozarcin agaban ta? Meyasa zaki zubar da ƙimarsa acikin asibiti? Kokinsan da wani namijin ne wlh bazai kuma zuwa nan asibitin ba, ƙoƙarin kashe masa gudan jininsa, Allah ne ya soki ma cikin bai zube ba da inaga saidai ku rabu dan ya ɗauka da zafi sam bashida walwala." Lumshe idon ta ta yi batare datayi magana ba sannan bayan wani lokaci ta ce , "Amma ya zanyi? Ni bazan iya fushi ba? Bazan iya nuna ɓacin raina akan abinda akamin ba ko me?"

GINI DA YAƁETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon