SHAFI NA GOMA SHA TARA

421 70 5
                                    

*GINI DA YAƁE*.  FREE BOOK

         *BILLY GALADANCHI*

    *EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                       (EWF).

     SHAFI NA GOMA SHA TARA 19.

Ficewa yayi daga cikin gidan gaba ɗaya ya fita waje, motar saya buɗa ya zauna agida baya tare da dafe kansa, babu shakka wannan itce yarinyar daya yiwa fyɗen amma shin ba'a kuskure ne a rayuwa? Gaba ɗaya Umma ta sauya masa bata duba irin masifun daya faɗa ta rabashi da auren wannan mayyar, shi tunda yake ganin mutane yaji tsanarsu wannan mai ido a zaren kalar na mayun tafi kowa bashi mugun takaici, yarinyar kuma saikace wata aba taita wasu abubuwan jinkai ita ba ƴar kowa ba rainon shanu! Zuwairah ita kaɗai yaso shi sam ko Ameerah ya duba Allah ne ya aure ta amma babu wani abu mai kamada soyayya a tsakanin sa da ita. Hafix baya nan, bashida number Hafix a yanzu da babu shakka zai sanar masa wannan halin, kai bazaima haƙura ba, zai baiwa yarinyar da kuma Umman sa haƙuri a wuce wurin.

    Zuwairah dukda ta samu labarin Ali yana Niger amma hankalin ta bai kwanta ba akan rashin neman ta a waya, tayi tsammanin Ali zai dawwama yana neman layinta daga sanda ta tafi har abada, amma ina dukda haka ta masa uzuri zuwa sanda zai dawo.

    Zube yake a saman gwiwowin sa tare da riƙo hannun mahaifiyar sa muryar sa tana rawa ya soma magana,

"Umma naji duk abinda kuka tattauna da Hajjo jiya, kuma tabbas haka ta faru ba musu amma wlh sharrin shaiɗan ne, bada sona bane, sanda haka ta faru bana cikin hayyaci na, ina fama da wata Lalura Umma na,bazan taɓa iya zuwa in gaya miki irin wannan lalurar ba har abada, kunya nake ji, cuta ce dani kamar mai aljanu idan har ta tashimun idan ban kusanci mace sai inyita suma ga zabar ciwon mara, nasha suma ni kaɗai har saina farfaɗo, ranar da komai ya faru akan wannan yarinyar wlh bana cikin hayyacina, saboda a wannan ranar nayi tsammanin mutuwa zanyi. Naje neman ki ne saboda ki bani wannan maganin da kika taɓa bani, a wannan lokacin nagama shawarar gaya miki ga damuwa ta, saboda akwai sanda kika tarad dani a wannan yanayin kika bani garin maganin hausa bayan nasha na samu sauƙi, koda na isa ba kowa sai ita kaɗai na tambaye ta ta ce bakya nan" Saikuma ya kasa magana kallon sa ta tsayayi sanan a hankali ta furta,

"Sai kawai tunda babu maganin Hausa ka zaɓi taɓa Allah" Da sauri ya ɗago ya kalle ta sannna ya ce, "Ba haka bane Umma, wlh ba haka bane sharrin shaiɗan ne" kallon yanayin sa ta yi sannan ta ce,

"Kayi kuskuren rashin gayamun matsalar ka dan inada maganin ta Yaro, haka kuma wannan matsalar taka mahaifinka ma ya yi fama da ita, gado kawo jinine yake bibiyar ka, ciwo ne kawai na mara da zaka nemi maganin ciwon marar da babu shakka ka warke tas tun kafin ka hayayyaƙewa ƴar mutane, yanzu me kake so na maka?

"Dama Umma ni so nake a taimaka mun a rabani da auren yarinyar nan dan Allah, zan bata haƙuri, za mata koma meye, amma ni bana sonta, zan bata haƙuri kinji Ummi na" Murmushi  ta yi sannan ta ce,

"Ali na rigada na ɗaura aurenka da Boɗɗo, kuma wlh ko bayan raina ba saki a tsakanin ku, har sai yaushe zakayi hankali? Da shege ka barta tazo ta haife a wahale, tanaji tana gani mahaifinta ya kore ta, ka rabata da farin cikinta ta dawo nan ta rasa uwa, uba da ƴan uwanta duk akanka, Allah yasa ɗan ya mutu ta huta, baka bi ba'asin wane hali ta shiga ba sai a rabaka da aurenta? Ƙafarka da tata zaku taka kubar gidan nan idan kaje da ita dan Allah ka kashe ta, sannan kuma an tabbatar mun idonta zai samu lafiya, saboda haka kayi amfani da dukiyar ka ka kaita ƙasashen turawa a mata aiki" Muryarsa tama sarƙewa ya ce, "Amma Umma" cikin tsawa ta dakatar da shi,

"Amma me! Kana tsammanin ita tanasonka ne da har tamun biyayyah! Ban isaba kake nufi ko me? Banida darajar dazaka bi umarnina ko me kakeso ka ce?" Da sauri ya riƙo hannu ta data warce,

"Ba haka nake nufi ba, kiyi haƙuri Ummina, inshaa Allahu zan riƙeta fiye ta yanda kike tsammani, zan mata adalci fiye da iyawata, ayimun aikin gafara nayi kuskure." Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,

"Yaro baka kyauta ba abind kayi, idan ka samu nutsuwar zama da ita ka nemi yafiyar ta amma ba yanzu ba, sanan kuma ka nemi maganin matsalar ka, tarayya da mata bashi bane, dan bazaka ce duk inda zaka sanya ƙafa saida mace ba" Shiru ya yi harta gama magana sannan ya yi godiya ya tashi ya fita.

***********
    Tunda suka kamo hanya Boɗɗo bakinta bai furta koda kalma ɗaya bane, saidai yana motsi, idanta wuri ɗaya suke kallo saidai gaba ɗaya rayuwar ta bata mata daɗi, har wannan lokacin Batasan cewar Ali bane ya aikata mata wannan aikin sai dai kam tabbas jikinta yana bata hakan, babu abinda take tunawa dashi sai amon sautin muryar sa, tayaya muryar zatazo iri ɗaya? Meyasa Umma take nuna mata shishi kaɗaia ne zai iya riƙe amanar ta, runtse idonta ta yi tana tunawa da haddar ta, shikena ammata asara saura mata izifi nawa alƙuranin daram ta haddace sa? Runtse idon ta ta yi so ɗaya tak wasu zafafam hawaye suka silalo mata, Allah ya tabbatar da abinda yake alkhairi akanta, duk abinda ba alkhairi bane ba Allah ya rabata dashi acikin ruwan sanyi.

    *Bayan kwana biyar*

Tunda sukazo bakinsa dana Boɗɗo bai haɗuba, ba ruwansa da ita, Hajjo ce ta nuna mata ɓangarenta da komai, ita ce take kulawa da ita, shi gaba ɗaya ko nemanta baya yi, ya ƙudurta  a ransa bazai ma kula ta ba bare har ta zame masa cuta, ci sha da suturu saita ture amma bazai iya ba harga Allah. Yau kaɗai yaji a ransa yana sha'awar kiran layin Zuwaira da har gobe bai daina kira ba. Tana zaune a saman kujera tana cin cucumber wayarta ya soma bulayin neman ɗauki sharewa ta yi dan ta gama cire rai akan Ali zai nemeta, shikuwa zabura ya yi jin wayar tana ringing, kira sama da goma amma batako motsa ba, Nan da nan ya shiga neman location na wayar yana gane tana gida bai ɓata lokaci ba ya bazama gidan, a inda take anan ya sameta, yana faɗowa parlon saida ya bata tsoro shikuwa cikin sauke numfashi ya zube a ƙasa, hadda ƙwallan sa ya furta,

"Zuwairah" Itama miƙewa ta yi, cikin basarwa ta ce, "Meye haka?"

Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now