SHAFI NA BAKWAI

383 65 0
                                    

  *GINI DA YAƁE*   FREE BOOK

  *EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                       (EWF)
    
          *BILLY GALADANCHI*

SHAFI NA BAKWAI. 7
  
     Bai tsaya ko inaba sai shagon sa, anan ya zaunar da su ya basu wannan ya basu wancen yana musu hira cike da ƙarfin hali har suka saki jikinsu dashi. Mahma cikin damuwa ta ce,

"Daddy wai ni mesa Umman momy mu take cewa dakai mai ƙashin tsiya ne? Cewa naji ta cewa Momƴn mu idan bata ce ka sake ta ba zata tsine mata, Daddy Momy tana ta kuka hadda majina, Uncle Imran ya dinga dukanta, ta ce, "itadai kawai a barta kano tanada harkar yi ga shop ɗinta inyaso zata rabu dakai, suka ce sam saitazo sun tafi" Shiru yana kallon yarinyar saida ta gama magana ya ce, "Mahmana ba ruwanki da wannan maganar kinji, wasa suke mata" Ɗan murmushi ta yi masa "Daddy wasa da duka? Tabb ba wani wasa daddy suda Allah kawai" Bai kuma magana ba, Mahma dududu shekarunta bakwai,ko ina ta san wannan maganar? Bai bi kan maganar ba yana kallonta ya ce,

"Gobe bazaku samu zuws school ba Mamah saimunyi setling a wancen gidan tukunna sannan saimu yi abinda zamuyi ku koma school da islamiyya" Jinjina kanta  tayi sannan ta ce, "Daddy yanzu dawa zamu zauna to?" Wayon yarinyar  yayi yawa tanason magana shikuwa ba yason surutun nan hakan ya sanya bai kula zancenba. A wannan daren dai a shagonsa suka kwana.

****************
    Ali ya rasa yanda zaiyi ya gayawa mahaifiyar sa wannan mummunan ƙalabarin na faruwar komai cikin ƙiftawar ido a rayuwar sa. Gaba ɗaya bazai taɓa iya lissafa tsawon asarar da ya yi ba sannan kuma komai sai yake ganin faruwar sa tamkar a mafarki. Jikinsa a mace ya janyo wayar sa ya danna kiran layin dayake tsammanin zai same ta akai, saidai har ta yi ringin ta yanke ba'a ɗauki kiran nashi ba. Ƙara tura kiran ya yi inda wannan karon ringin biyu ta yi aka ɗaga kira, Boɗɗo dabatasan ko waye ba ta ɗaga akan zata sanar Hajiya Umma sallah take. Jin an ɗaga kiran da sauri ya ce,

"HaJiya Barka da wannan lokacin, ya kwana biyu" Da hanzari Boɗɗo ta janye wayar a kunnen ta, nan take jikinta ya soma rawa, idon ta ya cika fal da ƙwallah cikin lalube ta kashe wayar tare da cillar da ita gefe ɗaya, matsawa ta yi gefe ta dafe ƙirjinta tana sauke numfarfashi sauri da sauri, wannan meke faruwa da ita? Wannan wa ce murya ce mai haifar da tsananin faɗuwar gaba, tare da tarwatsa kai! Ganin kiran ya yanke ya sanyashi sake kiran wayar saidai kuma wannan karon har so biyu ba'a ɗauka ba, wannan ya tilasta masa haƙuri da kiran wayar baki ɗaya.

*************

     Zuzu yau ma abubuwan nata sun motsa mata gaba ɗaya banda tunani dason ganin Ali babu abinda ke ranta. Yussy yanda ta shigo ta sameta zaune a ɗakin ta yi jigum ta tabbatar zan cen kenan dafa kafaɗar ta ta yi sannan a hankali ta ce suna fuskantar juna,

"A wannan halin da kike ciki Zuzu da inada inda zan samo miki Haidar wlg dabazan taɓa bari kisha famar neman sa ba. Nayi iyakar binciken da zan iya  amma tunda ya yi gobara ya daina zama a office ɗin, bai sayar da wurin ba amma bai waiwayar wurin, baya tsohon gidansa daya yi gobara kuma matar tasa ma ba labarin ta, nayi iya yina akan ganin na sama miki farin ciki amma abun ya ci tura, ya faskara ya kuma gagara Zuzu. Kuskurena na farko shine barin damar farko ta suɓuce mana, daban yi hakan ba da babu abinda zai kaiki shiga wannan halin, zuzu ki dubi girman Allah ki ɗaukewa kanki wannan wahalar rayuwar dan Allah." Ko motsawa bata yi ba har yayar ta ta ta miƙe tabar wurin, runtse idon ta ta yi sannan a hankali ta buɗesu ta ce,

"Aunty wlh inaso na ganshi koda hakan yana nufin cewar shine abu na ƙarshe da zanyi a rayuwa ta, Ali ya dasamun cutar ƙaunar sa acikin ɓargona dababu maganin waraka agareta, Ali ya barmun mummunan tabo da bazai taɓa gogewa a rayuwata ba! Ali ya barmun mummunan ciwon da har inkoma ga mahaliccina bazan taɓa daina jin zogi da raɗaɗin wannan ciwon ba, Ali shine gatana a wannaj duniyar, na ƙwallafa raina da Ali, na sskawa raina ƙaunar Ali mai dafin dake illata rayuwa zuwaga kushewa, dan Allah da maraicin dake kaina ki tallafeni Aunty!" Ta ƙarashe maganar cikin kuka mai ban tausayi. Aunty data gagara motsa koda ɗan yatsanta ne ta kafe agu ɗaya tana nazarin wannan rayuwar da ƙanwar ta take ciki, wannan wane mugun so ne? Tunda take bata taɓa ganin soyayyar hauka irin wannan ba, mutumin daya maka irin wannan yaudarar ace zuciyar ka taki warware ta kunce ƙullin amincin dake tsakanin ku koda na daƙiƙa ɗaya ne? Shin anya Ali bai haɗa Zuzu da malamai akai masa aiki a kanta taba kuwa? Sauke gwauron numfashi ta yi kafun ta ce, "Ki kwantar da hankalin ki zaki samu abinda kike so inshaa Allah, namiki alƙawarin nemo miki Haidar nan da ɗan lokaci ƙanƙani, ki bani lokaci ƙanwata kinji?" A hankali ta gyaɗa mata kai alamar gamsuwa da bayanin ta, cikin kuma tausayin kanta ta ce, "Nagode Anty Yussy" Yusrah fita kawai ta yi tabar ɗakin zuciyar ta a raunane.

     Ali bai fasa zama gidan su Mamah da uwarsu ta basu ba, acen ya tare da zama. Tare da nemawa yaranshi makaranta mafi kusa. Duk ya fita hayyacin sa damma dai keke napep da shagon sa suna matuƙar tsimaka masa wurin ciyar da yaran. Abu ɗaya ne ya ke damunsa shine rashin mai tsaya masa da su yaje aiki, wannan dalilin ne ya tilasta masa sanya su islamiyya gaba ɗaya basa dawowa sai 6 insunje.

    Wani yammaci bayan school bus ta ajiye su a bakin gidan sai sukayi rashin sa'a Ali bayan gidan. Shikuwa yana cen motar sa ta tsaya masa a hanya ya kira bakanike hakan ya sanya harya manta da lokacin tafiyar sa gidan don yaransa ya wuce. Haka sukayi ta zama har bayan magrib, suna nan zaune ba kowa sai zaid ya kalli yayarsa cikin damuwa da tsoro ya ce, "Adda Mahma Daddy bai dawo ba har yanzu kuma kashi nake ji, gashi inajin tsoro" Yarinyar ƴar ƙarama miƙewa ta yi tana ƙarewa yanayin unguwar ta su kallo duk wurin filaye ne sai kangaye da ba'a ƙarasa gini ba, gaba ɗaya maƙociyar su ma dasuke shiga gidan wacce gidan nata yana fuskantar na su tayi tafiya, ammata rasuwa, sauran gidajen akwai 'yar tazata tsakani sannan kuma sabuwar unguwa ce. Dukda batada shekaru da yawa amma ta san cewar basuda wurin zuwa ƙanin na ta ya ce zaiyi kashi agidan da ba'a sansu ba. Hannun sa taja suka shiga wani kango data hango ba nisa sosai da gidansu, "Zomuje cen kangon Zaid,maman su jainaba bata gari sunyi tafiya Daddy kuma wani abun ya tsareshi inaga, ka sauran ruwa a water battle ɗina saina ma tsarki dashi" Haka suka isa suka kutsa kai, ta karɓi jakar school ɗinsa da Lunch box ta ce tana kallon sa "Kayi kashin muyi mu tafi" Tsugunawa ya yi ya fara saida ya kammala tamai tsari sannan ya rataya jakar sa suka soma shirin fitowa. Suna isowa ƙofar barin kangon saiga wasu samari ƙarti su uku, kallon Mahma ɗaya daga cikin su ya yi sannan ya ce, "Ke me kuke ana?" Kallon ƙaninta ta fara yi sannan ta ce murya yana rawa "Zaid ne yakejin kashi kuma Daddy baizo ya buɗe mana gida ba shine nace yazo nan kangon ya yi" Bai ɓata lokaci ba ya ɗauke ta da mari,

"Ubanki ne ya gina kangon? Nace ubanki ne ya gina kangon dazaki kawo ƙaininki yamawa mutane kashi dan kin tabbata ƴar iska?" Dur ƙushewa ta yi da sauri dafe da kuncin ta, 

"Dan Allah Baba ka yi haƙuri wlh bansan bakwa so ba, kuyi haƙuri" Baban data ce ya ƙara tunzura Boss ɗin nasu cikin takaici ya finciko ta sannan ya ce waye Baba, ni zaki kalla ki gayawa Baba inba saina fanshe a jikinki ba shegiya nake kai Ɗan kuba maza kuzo kumun banƙarar kaza da ita kuma a tabbatar bakinta ya daina furta kamomi" Ganin anyi ciki da yayarsa ya sanya ya fashe da kuka tare da azamar riƙo hannun Boss ɗin ya maƙale masa, Iya ƙarfinsa ya sanya ya ture yaron kai tsaye ya faɗa akan wani ƙaton dutse ƙara ɗaya ya yi daganan bai kuma ko da motsawa ba!!! Ganin haka ya sanya Mahma kuka nan da nan ya janyo wani ƙarfe ya zaro harshenta ya haɗe da leɓenta na ƙasa ya hudasu ya manne su wuri ɗaya sai dalalar da yawu ta keyi bata kuma iya ɗaga harshe ta yi magana ba har suka nata zigidir sai nuni take da ɗan uwanta.

    A jaka ya tuƙo motar sa tunawa da yaransa, dukda ya san inyayi late sukan shiga gidan maƙotan dake kallon su amma bai taɓa yin late haka ba, yanada yaƙinin Mamah akwai wayo amma shin Zaid fa? Anya zata uya kulawa da shi kuwa? Bashida labarin maƙociyar tasu ma ta yi tafiya.

   *DAN ALLAH KUMUN UZURIN RASHIN TYPING, WLH HIDIMA NE. AMMA INSHAA ALLHU ZAN ƊAUKI CEWA IDAN NAYI YAU GOBE ZAN HUTA, INA FATAN KUNAJIN DAƊIN LITTAFIN NAN. KODA YAKE HAR YAU NASAN BABU WANDA YA FAHIMCI INDA MUKA DOSA, DA IKON ALLAH KUN KUSA FARA FAHIMTAR KOMAI.

MOM NU'AIM.

   

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now