SHAFI NA ARBA'IN DA ƊAYA

323 58 3
                                    

*GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                EWF

   *BILLY GALADANCHI*

41.

   Duk iya jan jikin da sukayi Hajiya Umma batace musu kanzil ba har suka fito, musamman Fatima fuska ta mata jajir saboda anci kuka. Wani takaicin su ya ƙara lulluɓe ta da mamakin su ta ɗauke idanta daga kansu, driver Ali ya kira nan da nan aka canja mota zuwa prada jeep baƙa, aka mayarda kayan Hajiya a nan itama Fatima aka saka nata sannan ya wurga ƴar ƙaramar jakar sa shima ya shiga ta re da cewa su shiga, ita dai Hajiya Umma ba abinda ta ce masa saida suka ɗau hanya ta ce, "Tasha zaka kaimu?" Ta manubi ya kalleta sannan ya ce, "Hajiya yarinyar nan fa tanada 'yan matsaloli gaskiya, idan ma baki yaddaba saina kaiki gun likitan ta, idan na baiwa direbobin nan ita su kaita saisu iya janyo wata matsalar ai, gwanda in kaita da kaina inyaso jibi saina dawo" Murmushi tayi ta re da kallon gefe har suka tsaya wani store anan su biyu kadai suka fita, suna jeruwa ya riƙo hannun ta Hajiya ta kama haɓa a ranta ta ce 'yau naga abinda ya fi zare tsawo,yaran nan haka suka dawo? Dukda abin farin cikina ne amma yaushe suka zare ba kunya ko kaɗan' Suna tsayuwa a cikin mall ɗin ya tsaya ta gabanta yakai hannu ya mayar da sumar kanta data fito ata mayafin ta, "Ya kika fito ba hula ba ɗankwali sai zallan mayafi ummm Fateena?" Ƙwallan datake tarewa ne ya silalo mata ta yi hanzarin kawar da kanta,murmushi yayi cikin ƙoƙaarin kawar mata da damuwa sannan ya ce, "Muje karmu bar Hajiya a mota, ki ɗauki duk abinda kike so da abinda kikasan zaki buƙata kinji" Hannu ta kai ta ɗauke hawayen, ita bawai baƙin cikinta rabuwa da Ali kawai ba, garin nasu ne ta tsana da mutanen cikinsa, meyasa za'ace gidan ubanta za'a kaita shin dama tanadanl uba ne? Kokuma dama sai kana moruwa kake na kowa? Duk yanda ma ya so ta ɗebi kayan kasawa ta yi sai shine dole ya ɗauka mata kayan tare da jibgarwa hajiyar sa nata suka koma mota......

   *NIGER REPUBLIC, AGADEZ*

Kwanan su ɗaya Hajiya ta umarce shi akan ya shirya gobe zasuje Tawa inda daganan zasu gangara ainahin ƙauyen su Fatima. Hakan kuwa akayi tun safe suka ɗauki hanyar tafiya ba ƙaƙƙautawa. Tunda suka doshi hanyar ƙauyen hankalin Fatima ya tashi, nan da nan kuwa hakan ya nuna sosai a fuskarta, Ali ma Hankalin sa yana kanta, a yanda ya sani tunda Hajiya Umma ta ɗauke ta daga wannan garin bata dawo ba, kuma tafiya ce ta yi mara daɗi kana dama bawai ta san yanayin garin bane saboda koda ta tafi babu ido a tare da ita. A ƙofar gidan suka yi parking inda Kawu Bala shine ya nuna musu wurin, daganan suka kalli juna ita da shi, Hajiya Umma ce ta fara fitowa sannan suma suka fito, dattijon dake zaune a ƙofar gidan saman dakali ya kalle su sannan yana washe baki ya miƙe ta re da cewa "Ahhh Chatou, Bala yau kune agarin namu" Murmushi Hajiya Umma ta yi suka ɗanyi raha sannan suka isa cikin gidan atare, muryar sa kaɗai ta tabbatar wa Boɗɗo cewar mahaifinta ne amma dai yanda taga idon sa baiko kalle ta ba haba ta kame bakinta har zuwa sanda aka musu shinfiɗa a ƙarƙashin bishiyar suka zauna matan gidan da mahaifiyar ta sukayi dafifi wurin gayar da baƙin inda acikin kaf babu wanda ya gane ta dukda tsananin kamanin da suke da mahaifiyar ta, Mahaifiyar ta kaɗai ce ta gane ta ita ɗin ma ta kasa gaskata zargin ta akan yarinyar dandai ita batada jiki amma wannan dukda ciki ne da ita tanada alamar yin ƙiba kam. Saida suka sha ruwa wanda aka kawo musu Boɗɗo kuwa batace komai ba kana kuma bata damu da shan ruwan ba, Hajiya Umma ce ta kalli wurin da suke sannan ta ce tana kallon mahaifin Boɗɗo,

"Malam Fatima ce dana gaya maka zan mata aure da yarona kwanakin baya na kawo gida saboda ta samu kulawa irin ta al'ada dan kuwa juna biyu ne da ita kuma harya shura ƙa'idar zuwa gida ma" Kallon Hajiya Umma ya yi sannan ya ce "Chatou  phatouma kuma? Ina take phatouman?" Da hannu ta nuna ta sannan ta ce, "Gatanan zaune yanzu har lokacin ya yi tsayin sa zaka kasa gane Fatima a duniyar nan?" Kawar da kanshi ya yi daga dubanta sannan ya ce, "Amma Chatou aina sanar cewar babu ni babu phatouma? Yarinyar data aikata abinda ya ke hanani zuwa wurin abokaina ko fita har gobe sabsda ana zunɗena? Duk faɗin garin nan Phatouma ce kawai ta taɓa yin shege, niko mezanyi da ita?" Hawayen datake ƙoƙarin tarewa ne ya silalo mata, ganin haka b ƙaramin ɓatawa Aliyu rai ya yi ba cikin baƙin ciki ya kalli mahaifin Fatima sannan ya ce, "Ko ma menene ai anawa mutum uzuri Baba, yarinyar nan zuwanta biki kano akai mata fyaɗe bason ranta ba ne ba, meyasa bazakuyi imani ku karɓi tata ƙaddarar a yanda ta zo ba?" Kallon sa ya yi da mamaki aannan ya ce, "Wannan shine yaron da aka aura mata ko?" Hajiya Umma data gama fusata cikin ƙufula ta ce, "A shine, wani abinne?" Mayarda dubanshi ya yi zuwaga Ali sannan ya ce,

"Allah ya yi maka albarka yaro amma shin kasan ta yi shege kuma a haka ka aureta?" Wani baƙin ciki ne ya tarnaƙe Ali cikin takaici ya ce, "Nine uban shegen tun wancan lokacin, kuma ni nasan cewar bawai yin kanta ba ne, nine na mata fyaɗe dan haka ina roƙon alfarmar daku yafe mata dan Allah" Miƙewa Malam ya yi sannan ya ce, "Indai akan maganar phatoum ne na gama magana, idan ta ƙara minti biyar agidannan Allah ya  isa ban yafe mata ba" Kallon tsoro Boɗɗo ta masa sannan da hanzari ta miƙe ta riƙe ƙafarshi tana gunjin kuka, "Baffa dan Allah ka yafemun, Baffa na tuba, Baffa bazan ƙaraba, Baffa ka dubeni da idon rahama  ka yafemun, nasan na maka laifi mafi girman laifi amma ka yafemun, zan yarda laifin duk nawa ne amma dan Allah ka yafemun kaji Baffa na" Tureta ya yi taje ta buga goshi a dutse, nan da nan jini ya wanke mata fuska amma haka ta bishi ta ƙanƙame masa ƙafa tanata famar gunjin kuka tamkar wata zararriya tana magiya, a haka ya soma tafiya yana janta amma taƙi ta sake mai ƙafa har suka fita wajen gidan, ali yana kallo Hajiya Umma ta hanashi zuwa wurin! Ƙarar da suka jiyo ce ta tilasta musu yin waje da gudu inda suka tarar Baffanta yanata dukanta tamkar zai zare mata rai, a wannan lokacin ne Ali ya shiga tsakanin su ya karɓe matarshi, nan da nan fuskarta ta sauya ƙananun ƙuraje duk suka feso,jikinta ma duk inda ya daka sai ƙurajen suka feso yayi jajir da ƙyar kawu Bala ya riƙe Malam, sai huci ya ke tamkar wani mayunwacin zaki! Ali yana miƙar da Fatima tsaye amma ta kasa tsayuwa sai silalewa ta ke, dole ya ɗagata cak zuwa mota da sauri ya sakata a mota ya zaga ya figi motar yabar harabar gidan!

  Mom Nu'aiym.

Saura kaɗan!

GINI DA YAƁETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon