SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA

416 72 7
                                    

*GINI DA YAƁE* FREE BOOK

EWF

*BILLY GALADANCHI*

26.

Koda ya isa masauki baya gani sosai, sannan tunda yake a duniya bai taɓa jin ciwon kai kwatankwacin yanda yakeji a yanzu ba, zuciyar sa tsallen gaske ta keyi tana ƙoƙarin baro ƙirjinsa ta fito waje, saida ya dafa ƙofar sannan ya yi knocking ya jingina ajikin ta saboda jirin dayake gani, Zuwairah data gama fusata da shi banza ta masa yakai 20mns tun yana iya Knocking harya zube awurin cikin azabar ciwon kai da jiri ga zuciyar sa dake barazanar tsallake ƙirjinsa ta tarwatse a waje inda zatafi samun wali. Mutanen dake kai kawo a wurin sune suka yo kanshi suna masa sannu da tambayar meke damun sa, amma ko idonsa baya iya buɗewa ya yi kasake yana sauraren datsewar numfashin sa a hankali! Jin hayaniya ya sanya ta zuro hijar ta leƙo ganin Ali a kwance ammasa rumfa ya sanya ta yi kanshi tana jijjigawa amma me idon shi sun lumshe sannan kuma alamu sun nuna baimasan inda kanshi ya ke ba, da gudu akazo da abulance ta kwashesu sai asibitin da Boɗɗo ta ke kwance, shi ɗinma aka karɓeshi emergency sai kuka Zuwairah ke yi na rashin mafita da ƙyra ta daure ta kira yayarta nanma bata ɗaga ba, a wujen ƙofar ta tsaya dake glass ne kana iya hango duk abinda Ake masa, har oxygen suka sama gaba ɗaya sun rufu akanshi, da gudu ta ruga ɗaki Boɗɗo ta tarar da ita zaune tana karatun alƙur'ani mai girma, da kuka ta isa wurinta abinda ya tilasta mata tsayawa jin muryar Anty, "Subhanallah Anty lafiya?" Riƙo hannun ta ta yi, "Nashiga Uku Fatima, hakanan kawai yayan ki ya koma gida da daren nan ya faɗi, yanzu naga har abin shaƙar numfashi suka saka masa yana asibitin nan" Da sauri ta miƙe, "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, kuma bai saba yin hakan ba? Yanzu yana ina, me akace yana damunshi?" Share hawayen idonta ta yi, "Basu faɗamun ba amma dai naga anata fama da shi"
"To anty maza muje wurinshi kar su nemi ƴan uwanshi basa nan" Tare suka jeru Zuwairah tana riƙe da hannun ta har suka isa wurin, zuwan su yayi daidai da fitowar likitoci inda ɗaya daga cikin su ya tsaya cikin harshen turanci ya ce,

"Are you his relatives?" (Kune ƴan uwan shi?) Da sauri Zuwairah ta matsa tare da cewa, "Yes Dr. Am his wife, (A likita ni matarsa ce.)"

"Ok Follow me, (To ki biyoni.)" Bayansa ta bi tana janye da hannun Boɗɗo da batajin turanci sam sai go, come, sit, stand da sauran ƙananun abubuwa shi ɗinma Baraka da zaid da Baby ne suke koya mata, sunayen su dining, cup, chairs da dai sauran ƙananan abubuwa, Allah ya mata kan ganewa to tana haddacewa bayaga haka ko taho in kasheki kace zataje dna batasan me ake nufi ba. Saida suka zauna a office ɗin likitan sannan ya ce,

"The patient blood pressure is very high did anything happened to him? has he ever been in this condition?" (jinin mara lafiyan ya hau sosai, shin wani abu ya faru da shi ne? Kokuma ya taɓa faɗawa cikin irin wannan yanayin?)" Tana sharar ƙwalla ta bashi amsa akan baitaɓa yi ba, nan ya sanar dasu zai sauka saboda sun bashi kulawa sannan a rage bashi yawan damuwa, da sauransu. Wurinshi suka koma inda suka tarar yana baccin wahala, gashi basa barin patient relatives su kwana dole Zuwairah ta koma masauki, saidai gaba ɗaya Boɗɗo ta kasa zama a ɗakin ta, har ƙarfe ɗayan dare tana zarya gashi bazata iya komawa ɗakin dayake ba, haka ta zauna tana masa addu'a har bacci ɓarawo ya sace ta.

    Washe gari tunda asuba sallah kawai Zuwairah ta idar ta kwaso yara da Baraka suka bazamo asibiti, anan suka tarar har lokacin yana bacci, sun kai kusan 7 sannan wani Dr. Yazo ya dubashi anan yake tabbatar mata jinin nashi ya sauka kuma inshaa Allah zai farko kafin 11: na safe, jin haka ya sanya ta bar Baraka wurin Boɗɗo, sannan ta ce zataje wurin yayarta ta sanar mata tafiyar su ta fasu saboda bashida lafiya, ta kasa samun wayarta. Shiru na wani lokaci tsakanin Boɗɗo da Baraka kafin daga bisani Boɗɗo ta ragewa zaman rashin daɗi da cewar, "Ki kaini wurin Yaa Alin mana Baraka."  Ba musu ta miƙe ta jagorance ta har ɗakin, umarni ta yiwa baraka akan ta kaita wurin gadonshi  ita kuwa har kusa da kanshi ta kaita ta ɗan zauna a rakuɓe tare sa lalubar hannun shi a hankali ta cura nata aciki, sannan ta lalubi kanshi ta riƙe da ɗaya hannunta ta runtse idonta, addu'a sosai ta masa kusan mintuna 25, sanan ta tsagaita, Shikuwa a hankali ya ya buɗe idon shi tuni, batare data sani ba ya kafe ta da ido, Baraka ficewa ta yi daga ɗakin inda baimasan sanda ya fara hawaye ba, bazai ce ga abinda ya faru da shi ba amma babu shakka ya sani ciwone ganin inda yake kwance, hannun ta dake cikin nasa ya motsa tare sa matse nata kaɗan zabura ta yi tare da soma wara ido tamkar zata ganshi, saikuma ta shiga laluben fuskarsa har zuwa saman idon sa da kumatu, "wani abu yana damunka ne yaa Ali? Inane yake maka ciwo kake kuka? Baraka ki je ki kira mana likita"  A hankali ya kai hannunsa ɗaya mai kanula ya janye gashin daya zubo mata zuwa bayan kunnen ta ya saƙala shi, sannan ya shafi fuskar ta,

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now