SHAFI NA ASHIRIN

392 87 9
                                    

   *GINI DA YAƁE* FREE BOOK

   *EXQUISITE WRITER'S FORUM*
                     (EWF)

         *BILLY GALADANCHI*

           20.
Miƙewa tsaye ya yi ya na sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin tsananin farin ciki ya kamo hannayen ta duka biyu sannan a hankali ya furta,

"Zuzu One more chance dan Allah, bazan kuma aikata wani kuskure ba har abada, bazan taɓa bari ki sake shiga wata damuwa akaina ba, ki yarda dani Zuwairah" Kakkafeshi da ido ta yi sannan cikin damuwa ta ce,

"Bakada lafiya ne Yaa Ali? Naga duk kayi rama, kayi fayau da kai anya ma kana cin abinci kuwa?" Sauke ƙwayar idon shi ya yi a ƙasa, muryar shi tana rawa ya ce,

"Har ila yau dai bazaki gajiya ba Zuwairah, sam ban cancanci wannan kulawar daga gareki ba, ni mai laifi ne daya cancanci ƙwaƙwaran hukunci ba kulawa ba" Hannyen ta ta zare daga cikin na shi sannan ta ce,
"Idan wani abu ya sameka bazan taɓa gafarta kaina ba Yaa Ali, saboda haka kama daina zancen da kake, yanzu inaso insan meke ta fe da kai?"

"Neman aure, bazaki ƙara suɓuce mun ba zuwairah, bazan kuma wasa da damar dana ke da ita ba akan auren ki, don Allah badan ni ba Zuwairah ki daure ki tallafa ki aureni, wlh soyayyar danake miki zata iya sanya in rasa raina" Anty Yussy ce ta shigo cikin falon da sallamar ta, duk suka mayar da hankali a kanta tare da gaishe ta cikin isa ta ce,

"Bamuda uwa bamuda uba bamuda madadin su, sai ƙanin mahaifin mu daya zalunce mu, banida wata dabara dazan tinkare shi saita kuɗi kuma na saye shi da abinda ya fi girmamawa wato kuɗi, ya tabbatar zai ɗaura aurena da Alhaji ranar juma'a, idan har ka shirya zan shigar da maganar ku kuma duniya ta shaida aurenku ranar juma'ar" Amaimakon ya bata amsa saiya zaro wayar sa a aljihun sa ya soma neman wata lamba kafin daga bisani ya kai wayar a kunnen sa, cikin girmamawa ya gayar da wanda ya kira ɗin sannan ya ce,

"Kawu dan Allah kazo kano ranar litinin zaka nema mun aure, sannan kuma munaso ka tsaya har zuwa  juma'a idan Allah ya sa an ɗaura auren inyaso ka koma" Cikin raha kawu ya ce,

"Kai Yaro da wuri haka? Inace zaka bari saika gama angwanci da Boɗɗo" Ɗan murmusawa ya yi cikin ya ƙe sannan ya ce, "Buƙatar hakance ta taso kawu, ita wannan tare  da yayar ta  ake so a ɗaura musu aure, shiya sanya." Jinjina kai kawun sa ya yi sannan ya ce,

"Babu damuwa inshaa Allah zan sanar da Hajiya da kuma kawu Gajam, duk tare zamuzo saika shirya mana masauki" Godiya ya yi sannan ya kashe wayar cikin washe baki ya na kallon Zuwairah ya ce,

"Amarya muje kasuwa haɗin lefe zamu fara" Ɓata fuska ta yi sannan ta ce, "Bance ina buƙatar wannan ba ai ko?" Yussy ce ta ce,

"Zuwairah ki sassauta masa mana, kin taɓa gani namiji ya yiwa mace gata irin wanan da ya miki, banaji akwai laifi dan kaso masoyin ka, matsayina na babba ina nema masa alfarma yafiya agunki, mun tuba bazamu ƙara ba" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Ya wuce inshaa Allah" Cike da jin nauyi ya na sosa kansa ya ce,

"Anty Yussy Baby fa?" Murmushi ta yi sannan ta ce Bacci ta ke, bata jima da kwanciyar ba ma" Gyaran zaman sa ya yi,

"Zan jira ta tashi in ganta, araina tana bani wahala sosai"  Dariya dukkansu sukayi sannan Yussy ta basu wuri inda zaman ya dawo wani kallon kallo, kowa ya kasa yiwa wani magana.

**************
   Tana zaune acikin ƙaramin garden da aka ƙawata bayan gidan da shi, yasha armashin furanni da shuke shuke masu ƙamshi, wanda daɗin ƙamshin su ya tilastawa wurin dawwamammen ƙamshin dabaya gushewa koda yaushe, koda yake shekarun ta ashirin bata ma ƙarasa cikawa ba amma tana mamakin irin wannan auren da aka ƙulla a tsakanin ta da mutumin da aka kira yayanta kuma ɗan uwanta na jini, koda sau ɗaya ne bakinsa da nata bai taɓa haɗuwa ba, takan rasa dalilin dayasa gaba ɗaya Alin baya shiga shirgin ta, koda wane lokaci saidai Hajjo ta zo ta bata abu ta ce daga wurin mjinta shin wannan mijin nata wane iri ne? Babu shakka bazata taɓa neman sa da wani abun ba, rayuwar kaɗaici rayuwa ce data saba da ita. Nazarin yanayin ta yake ya harɗe hannayensa duka biyu a bayansa, 'me akeso yaja ra'ayin sa a tattare da Boɗɗo? Kyau? Diri? Kokuma a'a idanuwan mayyar da take da shi?' ya tambayi kanshi a zuci, gajeran tsaki ya ja, sannan ya juya batare da ya yi magana ba ya juya, dukda batasan da mutum ba a bayanta amma tabbas inuwarsa ta mata rumfa, sunada tazarar da ba lallai bane ta jiyo sautin fitar tsakin sa amma kash ƙamshin jikinsa daya gauraye ilahirin wurin ya gama tona masa asiri, murmushi ne ya suɓuce mata ta wurgar da karan dake hannun ta takai hannu ta soma wasa da jelar gashin ta tare da lumshe ido.

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now