SHAFI NA GOMA SHA HUƊU

387 64 10
                                    

       *GINI DA YAƁE*  FREE BOOK

                        EWF
        
           *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA HUƊU 14*
  
         Hausar ma bawai ya gama zama a bakinta bane, bata kuma fahimci manufarsa ba, cikin ruɗu ta ce, "Nashe waye ne, mena maki dan Allah karki shutar dani" Runtse idon sa ya yi amma zuciyar sa batajin kira ƙoƙari yakeyi ya hana zuciyar sa aikata wannan mummunan aikin amma ya gagara hanawar, cikin tsoro ya ce,
"Banida niyyar cutar dake, taimakona kawai zakiyi kinji" Bata famice shiba harya shiga kici kicin ɗebe mata suturin jikinta, nan da nan ta fahimce shi, jikinta ya soma rawa, ta shiga kici kicin ƙwatar kanta amma ta kasa, kuka take tana masa magiya amma gaba ɗaya bai saurare ta ba, ihu kuwa babu kalar wanda batayi ba amma babu wanda yazo cetonta har Ali ya gama biyan buƙatar sa, a razane kuma ya dawo hankalin sa, binta ya yi da kallo ita ɗinma fuskarsa take kallo dukda bata gani ta daina kukan sai ajiyan zuciya! Sai a sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya soma tuhumar anya kuwa ma yanada hankali kuwa? Kansa ɗaya ya aikata wannan mummunan ɗanyan aikin? Yasan me yake kuwa? Kallon jikin yarinyar yayi da hanzari saiya tashi ya zuge zip ɗin wandon sa ya gyara jikinda yabi wurin da kallo, hannu takai ta soma gyaran zanin ta harta samu ta kimtsa jikinta, yunƙurawa ta yi ta tashi zaune  da ƙyar sannan a hankali ta furta, "Bana gani amma bazan taɓa manta muryar ka ba har abada, ban maka komai ba ban taɓa niyyan aikata irin zunubin ba kazo ka zalince ni Allah yanaji kuma yana gani sannan kuma na barka da Allah shine zai mana sakayya, wannan abin dakamun bazan rama ba bakuma zan gayawa kowa ba amma na barka da fitowar rana da kuma faɗuwarta, wlh bazaka mutuba saikaga sakayyar abinda kamun, daga yanzu har zuwa sanda zan ajiye numfashi na na ƙarshe zan tabbatar da cewar ina tsaye ba dare ba rana ina haɗaka da Allah" Jikinsa ne ya ɗauki ya ɗauki dukda da fulatanci take magana amma ba shakka ya fahimci cewar faɗa takeyi kuma tanajan Allah ya isane, da gudu  yabar ɗakin yabar cikin gidan gaba ɗaya. Kwanan sa biyu da abin a ransa yana jiran yaji an tashi maganar yaga har aka kammala bikin babu wanda ya tashi zancen anwa wata mace fyaɗe sai kawai ya watsar, dayake zuciyar zunubi baƙa ce sai gaba ɗaya Ali ya manta da wannan lamarin tunda ya cafki amaryar sa a hannu sai gaba ɗaya ya dawo wani kala ya shiga nutsuwa da shiryuw. Baya barin gari saida Amira saboda saiyayi watanni uku bai buƙaci mace ba amma duk sanda abin ya motsa masa sai gaba ɗaya ya birkice saiya sauke.

    Daga lokacin da abun ya faru Ali yakai shekara 2 duk sanda ya tuna abinda yayiwa yarinyar dabaimasan sunanta ba sai ya shiga  damuwa amma daga baya sai gaba ɗaya ya watsar yama fita maganar saboda Ali ya samu duniya, wannan sirrin sa ɗaya da bai taɓa gayawa kowa ba a rayuwa sai zuciyarsa. Har ya samu ƙaruwa Amira ta haihu hsr so biyu kawo wannan lokacin da matsalar nan ta sameshi da Boɗɗo da Zuwairah bai kums neman kowa ba a cikinsu, Khamis yasha tambayar sa labarin zuwairah amma saiya ce masa ammata auren dole ne, dole ya haƙura.

*Dawowa cikin labari*

 
   Jijjigar da Mamah keyi keyi ne ya dawo da Ali cikin hayyacin sa, firgigit ya farka tamkar mai mafarki, katatar da aka saka mata yabi da kallo nan da nan ƙirjinsa ya doka jini ne yake zuba tamkar da baƙin ƙwarya har katatar ta cika ma yana zubowa a ƙasa, kafin yayi wani tunani ba abinda ya faɗo masa sai yanayin yanda ya fitar da budurcin mata uku ba tare da haƙƙi ba musamman wannan bafilatanar mai tsananin kamannu da Hajiya Umma!!! Zabura yayi yaje kiran likita amma me koda suka dawo gaba ɗaya bata motsi ta sanƙare! Alamu nan take suka bayyana mutuwar Mahma, tashin hankali wanda Ali ya shiga a wannan ranar ba'a magana yayi kuka harya gaji!

    Zuwaira tana zaune tana tsefewa Aisha kanta yusrah ta shigo, murmushi ne mai nuni da tsantsar farin ciki ɗauke a fuskarta, wuri ta nema ta zauna kusa dasu sannan taja Aisha jikinta cikin ƙauna ta ce,"Baby na yaya dai, fushi ake tayi dani akak tsifar zan kaiki yawo ne fa" Ƙaramar yarinyar 'yar shekara takwas turo baki ta yi sannan ta ce,

"Anty Zuzu ne bata iya tsifa ba, da zafi sosai
takemun" Dariya sukayi a tare sannan tace, "Tunda an kammala jeki kiyi wanka zan kaiki salon a wanke gashin inyaso gobe saimuje kitso ko?" Da gudu ta ruga yarinya kyakyawa sosai kana ganinta indai kasan Ali tabbas zaka shaida cewar wannan 'Yar jininsa ce, bama ƙaramin kamanni taƙe da Mamah ba. Yussy tattare nutsuwar ta ta yi akan Zuzu sannan ta ce,

"Saboda bakida zuciya zuwaira ba lallai bane kiji daɗin labarin danazo miki dashi amma ki sani ni wannan shine labari mafi girman daɗi agareni aduniyar nan, Nayi nasarar Raba Ali da dukiyarsa gaba ɗaya ban bar masa komai ba sai motar hawa, gida ma na bar masa ne saboda kawai yanada yara, nayi ƙawance da matarsa kuma zugata sun rabu, yayi rashin sa'a anwa 'yarsa fyaɗe, tama mutu a daren jiya yarinyar aka ce, to dama nibawai talauci nakeso ya shiga ba yanda ya barki da ciki baikuma waiwayarki ba ya kunyatar damu haka nakeso ya kunyata a idon duniya, dukiyar Ali duk wacce na ƙwace banci ko ƙwandala ba suna nan ajiye zan kai gidan marayu, tun farko dabaki ɓoyemun gaskia ba da tuni yaci ubansa a hannuna amma sai kikace ya mutu saida kika gagara mantashi kika gayamun. Abinda dai nakeso in sanar miki shine na kira Amirah a waya matarsa, na gaya mata Ali yayiwa 'yarta fyaɗe da kansa kuma yarinyar ta mutu, yanzu lokaci ne dazaiji kunya fiye da kunyar damukaji, duniya zata juya masa baya bawai dukiya kaɗai ba har mutanen daya sani" Da sauri ta miƙe tsaye jikinta yana rawa ta furta, "Aunty you are crossing the line, wannan wane irin mummunan ƙazafi ne? Ai idan haƙƙina zaki ƙwatar mun 'yarshi zaki kai masa ki gayawa duniya abinda yamun amma tayaya zaki laƙaba masa wannan sharrin? Murmushi ta yi mai zafi sannan ta ce,
"Wannan dalilin ne ya sanya ta kwasoki mukazo Uk, wata uku zamuyi kafin mu koma ya gama shiga uku dan ubansa, kiyi tunanin ki yanda duk kikaso dama ya barki da ciwon hauka ai" Nan da nan ta shiga ihu da koke koke amma antyn tata bata saurare ta ba, tayi shigewar ta gida ta ɗaki ta barta anan!!

    Ali yana zaune rungume da Zaid acikin palon gidansa yana nazarin abubuwa da yawa ta 'inama ace ba'a haliccesa ba? Inama ace bai taɓa zuwa duniya ba, inama ace mafarki yake tun farkon rayuwar sa har ƙarshe, soma yake ya fita yaje yin wlcm back ya jefar da wayarsa wurin jana'iza amma ba hali Zaid bayajin daɗi kansa yana masa ciwo har yanzu, bayaso su fita rana ta ƙarawa yaron ciwon kai. Knocking yaji a hankali ya ɗaura zaid akan kafaɗarshi ya fita waje, mutanen daya ganine suka tayarmai da hankali dan kuwa police ne, gaisawa sukayi sannan ɗaya daga ciki ya ce,

"Kaine Aliyu Haidar?" Saida ya gayarwa Zaid zama akan kafaɗarshi sannan ya ce, "A nine yalaɓai wani abinne?"  Duƙar da kai yayi sannan ya ce,

"Munzone mu tafi dakai, ana zarginka ne da yiwa 'yar cikinka fyaɗe harta mutu kuma uwar yarinyar ce ta yi ƙarar ka, ka kama bakinka dan duk wani dakayi koka faɗa zai zama hujja agareka a kotu" Wani irin jiri ne ya ɗebesa jikinsa yana rawa harya kusa tuntsirewa, gaba ɗaya ya gagara fahimtar komai, ga yaro mara lafiya a hannun sa, lumshe idonsa ya yi sannan a hankali ya buɗesu ya zube akan ɗan sandan nan dake maganar nan, cikin ssrƙaƙƙiyar murya ya ce, " 'Yata mamah, danake cikin jimamin mutuwar ta wasu sun mata fyaɗe sun kashemun ita, itace kukazo nan ku tafi dani saboda kuna zargin nine na mata fyaɗen akan wace hujja?" Cikin tsawa ɗan sandan nan ya ce,

"Koma wace irin hujja ce damu zaka amsa tambayoyi agaban hukuma" Janyo gidansa ya yi ya rufe sannan yabi bayansu ɗauke da Zaid har cikin mota. A station ya tarar da Amira  tanata kuka, nan aka soma mayarda magana Amira ta ce zargin sa take dan halinsa ne, bayaga haka yanada wata cuta idan ta motsa saiya kusanci mace, yanzu baida mata shiyasa takeda yaƙinin shine, aka ƙwace Zaid aka baiwa Amirah sannan aka shirya ranar shiga kotu nanda kwana 2 shikuma aka garƙame shi!!!

Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now