SHAFI NA GOMA SHA BIYAR

420 66 16
                                    

     *GINI DA YAƁE*  FREE BOOK

                         EWF

         *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA BIYAR 15*

       Dafe kansa yayi acikin cell ɗin duniya tana juya masa, bashida wanda zai masa tsaye a duk faɗin duniyar sa sai Allah, babu shakka abubuwan daya aikata ne suke bibiyarsa a sanda bai taɓa tsammani ba, Allah shiyasan dalilin dayasa ya ɗauke Hafizu, ya ɗauke Umma
5 baya Nigeria babu shakka daya tabbatar khamis zai tsaya masa, yanzu duk ya gama fahimtar abokanan sa na bugi ne, dayawansu kuɗinsa suke so wanda suke abotar dashi badan ya basu wani abu ba kuma suna yine dan ace sunsan wane suna tare dashi, ya sani zuwa wayewar gari labarin sa zai bazu a media, duniyar dayake mafarkin ginawa da yaɓe mai kyau zata lalace saboda rashin ƙarfi da ingancin tubali, ya gina  rayuwar sa da tubalin toka gashinan tun ba aje ko inaba ya soma girbe abinda ya shuka!!

   *BAYAN KWANA BIYU*

Sai da aka kwana biyu sannan aka kai shi kotu zuwa wannan lokacin kuwa gaba ɗaya ya fitar da duniyar a ransa, bashida hanyar samun mahaifiyarsa a waya, bata neman sa kwata kwata itama ya rasa sanin laifin da ya yi mata, idan har bashine ya kirata ba tofa ita bazata kirashi taji ko ya yake ba. Kallon cincirindon mutane dake wurin yake da ɗaɗɗai da ɗaɗɗai yayinda ake karanto tuhumar da ake masa, lokaci guda ɗakin kotun ya ɗauki kabbara! Runtse idonsa  ya yi na wani lokaci kafin ya buɗesu a lumshe ya zube akan Amira dake kallon sa da tsananin ƙiyayya! Alƙali kallon sa ya yi cikin tausayi danshidai ya rasa dalilin daya sanya gaba ɗaya yana kallon mutumin yakeji ajikinsa tamkar bazai aikata hakan ba, mayarda dubansa ya yi zuwaga Amira sannan ya ce,

"Lauyoyi su gabatar da kansu" Ba musu lauyan biyu suka gabatar da kansu akan cewar sune waɗan da suke bayan wadda ta yi ƙara sai kuma wani lauya daya ziyarci Ali a cell daya gabatar da kanshi matsayin lauyan dake kare wanda ake ƙara, mai gabatarwa ya ƙara yin gabatarwa akan ƙarar da aka shigar, sannan alƙali ya ƴi magana kamar haka.

"Aliyu Haidar kaji abinda ake tuhumarka dashi, me zakace game da wannan" Shiru Ali yana kallon lauyan daya ce shine wanda yake kare wanda ake ƙara, to waye ya ɗaukar masa lauya? Shi bai ɗauki lauya ba, bawai bashida kuɗin bane amma ta yaya? Ta inama zai fara? Lumshe idonsa kawai ya yi saida alƙalin ya kuma magana sannan lauyan sa ya yi hanzarin karɓe zancen ta re da neman izinin yiwa Amira tambayoyi nan take kuwa alƙali ya bashi izini inda aka bata izinin fitowa ta tsaya acikin kejin da aka tanada dan irinsu.

  Kallon sosai Br. Yusuf ya yi mata sannan a gyara zaman madubin idonsa cikin hikima ya ce,

"Malama Amira kin shiga da ƙarar tsohon mijinki da kuka rabu watanni babu yawa a baya akan kina zargin shine yayiwa tilon 'yarki mace 'yar shekaru ƙasa da tara fyaɗen gilla harta rasa ranta. Tare kuke zaune dashi a gida ɗaya bayan kun rabu kokuma aa kinganshi ne sanda yake aikata hakan da har kike cewa shine ya yi?" Zubewa lauyan idanuwan ta ta yi kafain ta ce, "Shine mana ya yi mata fyaɗen! Har sai idan ina tare da wancen zan bad shaida akan nummunan halinsa? 'yata ce kuma shine ubanta amma ai koni uwarta fyaɗe yamun da girma na har yaga zan tona masa asiri shiyasa ya lallaɓani ya aureni, kaga kuwa babuko tantama tunda yake rayuwa ba mace a tare da shi kuma ya saba aikata zunubansa bazan taɓa daina cewa shine ya lalata mun 'ya ya kuma yi sanadiyar marinta duniya ba!" Kotun ce gaba ɗaya ta ɗauki kabbara saida alƙali ya tsawatar sannan sukayi tsit, ita kuwa nan da nan tasha ragamar hijabinta zuwa kan fuskarta tare da share hawayen ta! Lauya saida ya ja dogon numfashi jin sabon al'amari sannan ya ce,

"Babu hujja a cewar danya miki fyaɗe shine ya aikatawa 'yar cikinsa, sannan ta yaya zai miki fyaɗe ki rufa masa asiri mecece hujjarki ta rufa masa asiri bayan haka kuma a ina ya miki fyaɗen da girman ki ɗakinsa kika je matsayin ki na budurwar sa ko ya ya?" Lauya mai kare masu ƙara ya yi hanzarin karɓe zancen da ce wa,
"Objection my load! Lauyan dayake kare wanda ake ƙara yana ƙoƙarin sauya wa wannan shari'ar manufa gaba ɗaya, wannan bashi bane abinda ya taramu anan" Alƙali saida ya doki table dinsa da wannan gudumar sannan ya sanya hannu ya gyarawa tabaransa zama daram kana ya ce, "Barista Yusuf a gyara tambayoyi" Ɗan russunawa ya yi tare da gyaran tsayuwar sa shima ɗin ya daidai zaman madubin idonsa akan hancinsa sannan ya mayar da dubansa zuwa fuskantar Amira cikin ƙwarewa da hikima ya ce,

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now