SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI

367 64 3
                                    

  *GINI DA YAƁE* FREE BOOK

             EWF
  
    *BILLY GALADANCHI*

27.

Saida ya haɗa da gudu sannan ya riƙo hannunta, a hankali ya furta "Honey?" Mamaki yake yanda jikinta ke zuba ƙyarma tamkar an watsa mata kunamu a riga, idonta ya yi jajir, sannan sai lumshewa su keyi, dama Zuwairah tana fama da ciwon zuciya kuma Ali ya san wannan, bayaga haka tanada tsananin zafin kishi, ganin yanayin ta ya tsoratar da shi, a hankali ya ƙara tallafota jikinshi, ita kuwa gaba ɗaya dama ƙafarta ya soma kasa ɗaukar jikinta saita yi lamo ajikinsa, bai ɓata lokaci ba wurin ɗaga ta cak tare da juyawa wurin nurses inda aka bata taimakon gaggawa, saida Ali yaga  ansamo kanta tukunna ya samu nutsuwa, allurar bacci  aka mata saboda yanayin ta sannan aka buƙaci ta huta, likitan ya ƙara jaddada masa sam yanayin cutar da ke zuciyaar ta bata son  damuwa komai ƙanƙantarshi!, Cikin damuwa ya nufi ɗakin da Boɗɗo ta ke ya tabbatar cewar zuwa wannan lokacin fuskarta zata sauya, shikuwa baida maganin ta anan ya barsu a Nigeria, me yasa gaba ɗaya duniyar sa take neman gagarar sa? Sai yanzu ya fahimci ɓoyewa Zuwairah gaskia bazai amfani dukkansu da komai ba, yanzu ya fahimci cewar gaba ɗayansu bai musu adalci ba, har sanda ya isa kuka takeyi, kallon farko da ya yiwa Baraka ta kwashi yara suka fita, takawa ya yi inda ta ke sannan ya zauna kusa da ita ya riƙo hannunta, da sauri ta ƙwace hannun ta,  tana zazzare ido, gefen fuskarta ya kumbura, kanta ya fara ciwo idon ta ne kawai yau bai samu damuwa ba, cikin faɗan dabai taɓa gani a fuskarta ba ta ce, ka daina taɓa ni, tunda na haramta agare ka, kafara janyomun duka, kuma bana bari ake taɓa lafiya ta dan bata wadace ni ba, ba ka bita ba? Ba ka rarrashe ta ba? Ni ai kaga banida kowa ko? Ka tafi wurin matarka kawai." Bai taɓa tsammanin bakinta zai buɗe haka ba, bai sani ba Baraka ta gama tsara mata, ta zugata ta nuna mata itama fa macece kuma da igiyar auren sa akanta. "Fatima ba haka bane ba, dama na je ne in dawo da ita kuma saita fara ciwo." "Tunda ni ban fara ciwo ba ka koma wurin ta mana, cewa kamun idan muka koma Nigeria zamu rabu ko? Ina ai bamu koma ɗin ba? Daga yanzu har zuwa lokacin da zaka sakeni idan har aka ci haƙƙina kuda Allah." Da mamaki ya kalle ta, sannan cikin faɗa ya ce, "Ke ke kike taƙama dashi? Notes na kanki sun kunce ne? Kokuma kina taƙamar isa ne san kinga ina rarrashin ki zaki tsaya ina faɗa kina faɗa." Ɗauke kanta ta yi daga dubanshi kawai bata yi magana ba, shikuwa a fusace ya miƙe tare da barin ɗakin gaba ɗaya.

  Dr. Ne yazo dunata ya ga fuskarta ya tamabyi ba'asi, anan Baraka ta bata amsa sa Boɗɗo batajin turanci, nan da nan ya bata magani, sanan ya sallame su daga asibitin gaba ɗaya, baraka ce ta haddace sunan hotel ɗin da suke dan haka itace ta mayar da su masauki, dan Ali bai kuma waiwayar Fatima ba har lokacin, sai bayan kwana ɗaya Zuwairah ta dawo daga asibiti, inda Ali kacokam ya mayar da hakalinshi akan kula da ita tare da rarrashin ta, kuma ya mayar da au Fatima Nigeria inda su kuma suka wuce Umara akan sai after 2weeks zasu dawo!

***************
   Gaba ɗaya tunda suka dawo Nigeria Boɗɗo a sabuwar duniya take jinta, banda yawo babu abinda take, dama ga Yaa Ali ya basu kudaɗe itada Baraka sun zama ƙawayen gaske, ta ƙara kyau ta yi ƙiba saboda gaba ɗaya ta cire wani batun Ali a ranta, ita dama saboda taga ya damu da ita ne ta damu dashi, amma yanzu daya nuna mata dabbobinsa ma sunfita muhimmanci saiya share babin rayuwarta, taci gaba da rayuwarta tana baiwa idonta abinci takuma ƙudurta a ranta  duk rintsi saita rama wulaƙancin duk da ya mata akan matarsa musamman da Baraka ke nuna mata zahiran ga abinda duniya take ciki.

    Dama sunada labarin dawowar su Nigeria, suda sukace sati 2 zasuyi haka suka dinga yawon duniya har sukayi wata 2, yara tun suna kukan Momy da Daddy har suka haƙura. Wani yammacin ranar laraba sun gama taara girkuna kala kala na gani na faɗa, gidan ya shagyara kowane part sannan kuma sai tashin ƙamshi ya ke tamkar gidan sabuwar amarya a maiduguri! Fatima da zaid da kuma Baby sune iyayen taryar baƙi daga airport dan haka Baraka da idonta ya gama buɗewa a rayuwar abuja ta dannawa ƙawarta kuma uwargijiyar ta kwalliya, Hajjo da tuni ta daɗe sosai da tarewa ganin kyawun da Boɗɗonta ta yi ya sanya ba shiri ta rangaɗa guɗa tare faɗin Uwargida sarautar mata" kallon ta Boɗɗo ta yi sannan ta ce, "Hajjo alƙawarinmu zaki karya tun yanzu? Dan Allah ki riƙe komai a ranki gudun tashin fitina da wuri."  Bakinta ta kama sannan ta ce, "Na yi shiru Faɗimatuzahrah" gaba ta yi riƙe da hannun ya ra, sannan ta ja su suka shiga kotar dazata kaisu airport ɗin inda wata motar tabiyo bayansu kamar yanda Ali ya umarci driver's ɗin.

   Sanye take da doguwar riga kalar sararin samaniya har mayafin ta, asaman rigar ta ƙasan dukiyar fulaninta an ajiye wani zaren ɗaurewa abinda ya baiwa tuma tuman dukiyar fulanin ta daman yin ruɗu ruɗu!, Ta ƙasa kusa ta baje dukda haka sirrin shape ɗin jikinta a bayyane yake. Takalmin ƙafarta baƙaƙe ne masu tudu, ta ɗaura agogo a hannun ta sai, idonta madubi me medicated da aka bata a india saboda dole idonta bazaiyi ƙarfi ba tunda ga yadda suke, ta tufke sumar kanta a tsakiya saidai fa ata gaban goshinta ga suma nan a kwance mai tsananin laushi, wacce bata yawa tana shirin haɗewa da gashin girararta, ta harɗe hannayen ta a ƙirji tare da jingina ajikin mota tana ƙarewa airport ɗin kallo, zaid da Baby gefenta a tsaye, cikeda so da ƙauna suka fito daga hanyar da wanda sukayi landing ko boaders  suke shiga ko fita, kallon su ta keyi amma su basu wani kalle ta ba dan babu wanda ya gane ta acikinsu saboda ta yi ƙiba sosai, Ita d akanta ta nunawa zaid da Baby su ta ce, "Kunga Momy da Daddy sun fito kuje ku musu oyoyo, dukansu suka ruga ita kam ko gezau batayi ba, sanda Zaid ya ce anty Fatima ce sannan suka gane ta, madubinta farine ƙal dna haka kana hango ƙwayar idonta, kallo ɗaya Zuwairah ta mata ƙirjinta ya doka, dama Marwa da Arwa duk sunzo gari amma sun sauka ne a part ɗin da su Boɗɗo suka taso sunzo suga yayansu shekaru kusan biyu basu ganshi ba koma fi.

Bataje inda suke ba har sukazo inda ta ke, ɗan murmushi ta yi sannan tace, "Sannunku da zuwa" Ali gaba ɗaya bai samu damar amsa mata ba saboda ya shagala da kallonta, yana mamakin wannan tsaleliyar ace wai Boɗɗo ce, bayaga haka wannan wayewar daga ina? Ita kuwa Zuwairah ƙamshin wurin takewa zarar ido da tsananin mamakin yanda wannan makauniyar ta musu gaisuwar ƙyare! Basu amsa mata gaisuwar ba dan haka bata dau ba, ganin zasu ɓatawa juna lokaci ya sanya ta ce tana kllllon yaran, "Zaid, Baby kuzo mushiga mota, ku bar Daddy da mommy haka har muje gida ko?" Ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Baby, wani tizge hannunta Zuwairah ta yi, sannan cikin faɗa ta furta, "Ke jahilar wace anguwa ce a ƙauyenku da zaki hanawa yarana gaisawa da ni bayan kusan watanni biyu rabon da mu gana? Wannan shishige ne ai." Murmushi kawai ta yi bata koda kalleta ba ta zaga kawai ta buɗe gidan baya ta zauna sannan ta ce da driver, "Ka kaini gida kaji Ɗan Sule" 

"To hajiya bara in gaisa da oga." Ya ƙarashe maganar yana zare sit belt ɗin sa sannan ya fita daga motar ya je suka gaisa sosai sannan ya dawo yaja motar suka tafi, a ƙufule ta kalli Ali, "Mesa wannan mayyar zata zo taryarmu duk mutanen gidan, ina kace Hajjo tana nan, kakuma sanar da ni Marwa da Arwa duk suna nan, sai wannan mayyar daga dirowa na a ƙasar zaka haddasamun ciwon zuciya! Sauke ajiyar ya yi, "Ban zaɓi wanda zaizo airport ba Honey, hasalima harna manta tana gidan, cewa kawai na  yi azomun da Zaid da Baby shikenan." Hararar sa ta yi "Waka kira agidan ka sanar masa haka?" A takaice ya bata amsa da "Hajjo" sannan ya yi gaba ya shiga mota ya zauna ita kuwa sai kumburi ta ke har suka je gida bata daina fushin ba. A babban falon gidan suka tarar da kowa, har Boɗɗo ta kwaɓe rigar ta ta sama sai wandon palazo ne ajikinta da top, wandon a ƙasanshi ya buɗe sosai saman sa a tsuke sai rigar kuma iya ƙugu, ta zube gashin kanta ko ɗaurashi batayi ba, a tsakiyar parlor sai shan kankana suke suna hira abunsu, shigowar su ne gaba ɗaya suka kaure da ihu, banda Boɗɗo dako motsin kirki batayi ba, Shidai gogan sai kallonta yake tana zaune tanashan kankana abinta duk ihun da ake ko waigawa batayi ba, Zuwairah kuwa hankalinta yana wurin Marwa da Arwa dake tsananin kamannu tamkar an tsaga kara kuma suna kama da Ali da waccen Mayyar, daganan part ɗin su suka wuce a kasale, Marwa ta na kallon Boɗɗo ta ce "Ke lafiyanki kuwa baki ga baƙi sun iso ba?" Murmushi ta sakar mata "Kin manta ni ce na taryosu daga filin jirgi" Dariya suka saka sannan suka zauna sabuwar hira.

   Washe gari tunda safe su Fatima suke kitchen ita da  Baraka suna shirya breakfast, "Baraka Airpeace ne a kunnenta ita kuwa Boɗɗo karatun alƙur'ani take mai girma da zazzaƙar muryarta, hankalinta a kwance, tana sanye da riga da wando na bacci yanzun ma sumar kanta a baje yake saidai ta saka hula mai ɓula a tsakiya hular ta zubo da gashin ta bayan kanta. Fuskarta fayau sai sheƙi takeyi fara sol, gashin girrar ta dake baki dana sumar kanta da ido sunwa farar fatar kyau,Sanda ya dawo daga masallaci saida ya ɓata lokaci wurin sauraren karatun datake rerawa da murya mai asalin daɗi yana lumshe ido, yanzu ma gashi yanaso ya ɗan zaga gidan da sanyin safiya muryarta zata shagaltar dashi, shin ita bata hira ne sai karatun alƙurani gaskia ta huta, ya sani yanzu fushi ta ke dashi, ya tabbatar cewar a ranta gani take tamkar bai damu da ita amma bata sani ba ita ce raunin sa, ya rasa yanda zai ɓullowa lamarin ta, a India ya kula sunyi saurin shaƙuwa tanada saurin sabo, a yanda ya ke kuwa nan da nan zata fara sonshi duk kuwa ranar data gano cewar shine ya mata fyaɗe babu shakka zata ninka tsinuwarta a kansa, hakan ya fi babu shaƙuwa zai sanar mata shine ya yi komai inyaso ta yafe masa su rabu yafi zama alkhairi.

  Mom Nu'aiym

GINI DA YAƁEUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum