SHAFI NA ASHIRIN DA ABIYU

345 62 3
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

          EWF.

  *BILLY GALADANCHI*

        22.
A hankali a hankali sautin kukanta ya soma raguwa, tun tana da ƙarfi har ƙarfin nata ya soma rinjayar ta, lumshe ido ta yi tare ɗaura hannu ta shafi fuskar ta a karo na barkatai, rabon da adake ta tun komawar ta agadaz, rabon ta da wannan ciwon kuwa tun dukan da akai mata na ƙarshe, zama ta iya cewa ta manta da wannan ciwon, ji take tamkar an watsa mata ruwan attaruhu a idonta, gaba ɗaya kumatunta ya yi suntum yayi jaji tamkar gauta, duk inda shatin hannunsa ya kwanta ƙananun ƙuraje sun feso burjik awurin sunbi shatin hannun, nan da nan kanta ya soma sarawa, idan dukan ajikinta ne bata cika samun matsala irin haka ba, babban matsalar ace a fuska aka dake ta tofa ba zaman lafiya, kwata kwata fita hayyacinta ta ke fatar jikinta sam batason duka, tanada alergy na gaske akan abu ya daki jikinta koda ba hannu bane kuwa.  Har bayan isha tana kwance agun bata ko waigo ba dama kuma fashin sallah take, ganin kanta yana barazar tsage mata ya sanya ta kira Zaid daya shigo ɗakin sannan ta ce da shi,
"Zaid jeka ka kiramun Momyn ku kaji, ka ce wai inji ni dan Allah ta zo." Saida ya kalle ta sosai sannan ya ce, "Anty tun ɗazu kina kwance agu ɗaya bakida lafiya ne?" Bataso ta waigo yaga yanda fuskar ta ta yi zaima iya tsorata dan haka sai ta ce da shi,

"Zaid mana, kaje ka kiratan banason surutu." Bai ƙara magana ba ya juya a bedroom ya samu Zuwairah tana shafa mai a jikinta, saida ya gayar da ita sannan ya ce,
"Momy wai inji Anty Boɗɗo tana kiranki kizo." Murmushi ta yi sannan ta ce, "Kaje ka ce na ce ina zuwa nanda mintuna goma sha biyar." Kaman daga sama sukaga faɗowar shi a ɗakin, yana kallon Zaid dake masa oyoyo ya ce, "kaje ka gaywa antyn ta ka bata isa ba, ita dai ta zo amma momy kam bazata je ba danba sa'arta ba ce ba"  kallon mamaki ta wurga masa sannan a hankali ta furta, "Daddyyyy, wai meke damunka ne? Bakasan uzurin ta ba, Boɗɗo fa yarinya ce mai tsananin biyayya dan Allah badan ni ba ka sassauta mata, ni gana ɗaya ka birkice akan yarinyar nan ko ƴan aikin gidan nan baka tsawwalawa kamar yanda ita kake tsawwala mata."

"Rashin tarbiyar har ya kai ta aiko akiraki? Menene amfanin wannan abu? Yara zata koyawa rashin tarbiya a banza, idan dai har bazata zo ba to wallahi ke ma ba zakije ba, kinga karma ki ƙara tashin mun maganar ta dan Allah!" Nisawa ta yi,gaba ɗaya a dangin miji ba wanda ta sani sai Boɗɗo, Marwa da Arwa sai sunayensu ta sani basa garin kano ga alama kuma basuda zumunci ko kuma wannan fitinar ta yayansu ya sanya basa son raɓarsa, dolenta ta tattali Boɗɗo amma yanzu tunda ya rantse zata haƙura har zuwa safiya.

    Da gudu ya ƙarasa inda ta ke sannan ya dafa bayan ta, "Anty inji Daddaynmu wai saidai ke kije ita bazata zo ba." Murmushi ta yi shi yaro ba ruwan sa ko da maganar tafi haka muni zai faɗa ne kai tsaye, cikin wayancewa ta ce,

"Yanzu kaje ka gayawa Baraka na ce zanyi bacci, kuma kaina kemun ciwo nasha magani kar wanda ya shigomun, ta baku kayan bacci a tabbatar kuma anyi addu'a kafin kwanciya kaji ko?" Langwabar da kanshi ya yi sannan ya ce , "Sannu" kawai ya juya hakan ya bata samar tashi a hankali saboda kumburi idonta ya kusa rufewa ta taka taje ta rufe ƙofar bata saka key ba ta rage hasken fitilar ɗakin sannan ta kwanta, zuciyar ta sam ba bu daɗi ga azababen raɗaɗi da fuskarta ke mata ga ciwon kai.

    Washe gari kam abin yafi muni dan sam bata runtsa ba kwata kwata, shigowar baraka wuraren 7 ya bata damar yin tozali da fuskar Boɗɗo abinda ya yi tsananin tashin mata hankali taja baya da sauri tana salallami, "Anty B meya sameki haka? Wani ƙwaron ne ya cijeki?" Muryan ta yana rawa ta ce, "Baraka ki taimakeni da ruwan ɗimi insha, karkuma ki gayawa kowa halin da nake ciki da kanshi zai tafi" Takowa ta yi ta dafa kafaɗar taannan wane irin ciwo ne? Ko akwai abinda kikaci wanda jikinki bayaso kike eacting, kalli wani ƙananun ƙuraje ko ina kamar shatin yatsu" Sadda kanta ta yi a ƙasa da sauri, harga Allah batason ta sanar da Baraka gaskiyar abinda ya faru da ita, amma ya zatayi? Muryanta yana sarƙewa ta ce shiyas na ce karki gayawa kowa, jiya ne da dare na ɓatawa  Daddy rai shine ya mareni a fuska, nikuwa inada damuwa a fatar nan ta tawa daidai da karo nayi da abu indai fatana ya daku zakiga yamun haka" Cikin tausayawa ta ce "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, lallai tabbaa kina fama da lalura, amma me ake baki idan ya miki haka" Nisawa ta yi ta ce "Bazan iya tuna yaushe yamun yawa haka ba, na manta yaushe rabon da adakeni a fuska, dama idan ajiki ne tokuwa nikan saka  galas (ƙanƙara) a tsumma sai inta gasa wurin a hankali, kwana ɗaya biyu zai washe, na fuska kuwa har ido yake taɓawa shi magani ake bani na gargajiya, amma nafi shekaru 8 banyi na fuskar nan ba, bansan ya zanyi ba gashi ba'a jamhuriyar mu bane ba bare a nemomin da sauri kuma wallhi zafi yakemun tamkar an watsamu ruwan attaruhu a fuska na, idon ma zogi yakemun." Ta ƙarashe maganar tana ƙara ɓata fuska tare da fifita fuskar da tafin hannun ta, Baraka zama ta yi yanzu kam sannan ta ce,

GINI DA YAƁEOnde histórias criam vida. Descubra agora