SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA

418 59 11
                                    

    *GINI DA YAƁE* FREE BOOK

  *EXQUISITE WRITERS FORUM*
                      (EWF)
   
       *BILLY GALADANCHI*
21.

     Baraka ce ta shigo ɗakin da sallama, ɗauke a hannunta tray ne mai ɗauke da plate a rufe da kuma tea cup akai,agaban Boɗɗo ta dire sannan a hankali ta ce, "Anty har ƙarfe biyar na yamma ba abinda kika ci, dan Allah kiyi haƙuri Anty, ga tea mai zafi na kawo miki saina haɗa miki sandwich kici dashi, idan hanjinki ya warware saimu nemi abinda zakici" Nisawa ta yi dan harga Allah tanajin yunwa amma batada ɗanɗano ko kaɗan a bakinta,

"Baraka banajin cin komai ki barni kawai" cikin tausayawa ta ce,

"Anty dukda nasan ba hurumina bane shiga al'amuranki amma ki sani saikin tashi tsaye, nasani babu daɗi ace mijin aurenka ya mayar dakai shara, yana ƙaryata zamtowar ka mata agareshi amma ki sani ke ma macece, Anty na shekaruna bakwai ina aiki a abuja ni bana ganin kinayi kamar matan zamani, tun ina ƴar shekaru tara nake aikatau, a garin aikatau nayi makaranta har matakin sakandire, mutuwar uwargijiyarmu ita da mijinta a haɗarin jirgin sama ita ce ta haifar da dawowata garin kano neman matsuguni danni marainiya ce, inada wayewa ba yabon kai nakeyi ba dukda ban daɗe agidan miji ba Allah yamai rasuwa amma acikin mata uku na zauna kuma shekaruna  huɗu da su, na tabbatar na girmeki kuma nafiki buɗewar ido, ki bani dama anty in jajirce wurin fito da zamtowarki mace kema ki rama, wlh duk macen data bari baƙin cikin ɗa namiji ya hanata sukunu bazata taɓa walwala ba har abada" Nisawa ta yi  sannan ta ce, "Baraka inada damuwa ne tun kafin aurena da Yaa Ali, nayi tsammanin zan samu nutsuwa idan na bar ƙasata na auri ɗan uwana, ban aureshi dan ina sonsa ba, na aureshi ne bisa biyayya meyasa ko gaisuwa na baya amsawa sai a daƙile, nasani duk abinda nake buƙata ana bani ana ajiyemun amma haka ake aure Baraka? Ni kenan tunda nazo duniya a baƙin ciki nake kuma ashi zan dawwama?" Da sauri baraka ta riƙo hannunta tare da furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, haba Anty dan Allah ki bari karki yi saɓo fa, ki kwantar da hankalinki inshaa Allahu zai dawo gareki, yanzu dai yanda ya faɗa keba matarsa ba ce ki zauna akan hakan itama karki nuna mata ai zamansu ya ɓarar dan kowane lokaci zata sani ne" ƙwallan daya silalo mata ta shafe sannan ta ce, "Saboda bana gani ake wulaƙanta ni ko? Ko saboda anga kamar banid gata? Makauta bai na sakawa kaina ita ba Allah ne ya ɗauramun" Daga nan ta kuma fashewa da kuka rarrashi sosai Baraka ta yi sannan ta haƙura da kukan ta zauna a ƙasa ta sha tea ɗin da har ya soma yin sanyi.

  *BAYAN SATI BIYU*

Har kawo wannan lokacin ana zaune ne agidan Ali d sunan cewar Boɗɗo ƴar uwarsa ce tazo tayasu aiki da kula dayara, akwai shaƙuwa mai tsanani a tsakanin Boɗɗo da Baby Aisha da kuma Zaid zaka rantse sun shekara da sanin ta, wannan ya saya suke wasa sosai da ita. Yauma kamar kullum chocolate ta kwaso a plate tazo suka zauna a ƙofar shiga babban parlor ɗin gidan saman corridor, abinda ta koyar dasu na alƙur'ani take musu game dashi idan ta janyo aya duk wanda ya ƙarasa mata shi ake baiwa chocolate da swt, Ƙarasowar sa ke nan a ƙofar gidan bayan ya dire motar ya tsaya ya tako dama nan ne hanyar shigar sa cikin gida da key ɗinshi da wuya ne ya zaga, cak ya tsaya yana kallon yanda take rero karatu acikin suratul muhammad aya ta bakwai muryarta tamkar wata balarabiya, abinda yafi bashi mamaki shine yanda kafin takai ƙarshen ayar yaran duka suka ɗauka atare suka ƙarashe susu biyInu tana wata irin dariya mai cikeda annuri ta ce, "Dukanku  kuka haddace gaskia naji daɗi sosai, tunda haka ne Zaid ka gayawa Daddy dan Allah ya sanya akaimu kalan yawon rannan" Ihu taji sunayi Daddy oyoyo Daddy Oyoyo ya sanya ta yi azamar miƙewa tare da kallon wurin dataji muryoyinsu na tashi, ba shakka ga inuwar sa nan kuma ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar ya kakkafe ta ido, ita ɗinma kai tsaye ta zube masa idonta masu launin Zaiba da ɗigon blue, shine ya fara kawar da kanshi daga dubanta sannan ita kuwa kai taye ta furta "Daddy Sannu da gida" Gyaran murya kawai ya yi ba tare da ya amsa mata ba hakan ya ƙara kashe mata jiki a hankali ta juya da plates ɗin chocolate ɗin da ya saura a hanun ta, kallon takunta ya ke bata kuskure bata ɓace hanya wannan ma acikin makafi nata makautan mai lisence ce. Saida ta wuce sannan ya soma yiwa yaran magana da wasa suka ɗunguma ta ƙofar falon sa. Zuwairah ba tanan dan haka Baraka ta tasata agaba saida ta ɗauki abincin sa ta nufi dining a hankali gudun karta faɗi, dukda ta gama haddace hanyar amma tsaf zata iya yin karo da wani tunda bata ganin abu sosai sai dishi dishi wanda bama kowa ta gayawa hakan ba.  Yana zaune zaman dining yanashan kankanar daya zuba late da cokali mai yatsu, bata ankara da shi ba saidai tabbas ta ji ƙamshin turaren sa, bata kawo yana wurin ba dan bataji motsin kowa ba, ta ɗauka kawai tunda wurin mazaunin sa ne zai iya ɗaukar ƙamshin,cikin nutsuwa da dabara ta dire tray ɗin tare da soma jere warmers data ɗauro akai akan table ɗin tana laluben wurin a hankali, saida ta gama sannan ta juya bayan ta lalubi tray ɗin ta ɗauka zummar barin wurin, Cikin dakkiyar murya ya ce,

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now