SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU

354 62 7
                                    

    *GINI DA YAƁE* FREE BOOK

                 EWF
   
         *BILLY GALADANCHI*

24.
    Tsoro sosai ya kama Boɗɗo musamman jin an soma kiran sallan magrib, jikinta yana rawa tana mike ta soma tafiya batare datasan inda zata je ba, ƙwal taji ta yi karo da abu har goshinta ya ƙwale, hannu ta kai ta sosa sai kuma ta fashe da kuka, "Hajjo na kizo ki taimakeni,Hajiya Umma zan koma Agadez dan Allah" Ata bayanta ta ji muryar wasu mazan suna magana a kanta,

"Baba kaga wata cika wai? Ta gama haɗuwa wlh, muje muɗan latsa ta." Ƙarawa takunta sauri ta yi ya yinda suka ƙara nasu suka sha gabanta, "ƴan mata ji mana" Jin haka ya sanya ta ruga da gudu abinda yasa ta hau kan titi bata sani ba, sai ƙara oda ta ji tamkar ankara kunnenta anayi, tsayawa ta yi cak tare da dafe kunnayenta duka biyu tana ambatar sunan Allah da ƙarfi ta ji an fizgeta sannan aka ɗagata cak aka ruga, saida ya tsallaka titin sannan ya dire ta, "Ni meyasa wai bakida hankali ne? Waye ya ce ki bar inda na barki? Dakika fito gidan ubanwa zakije? Yanzu idan da wani abun ya sameki ya kikeso inyi?" Jin muryarshi ya sanya ta yi azamar faɗawa jikinsa jikinta yana rawa sosai, hankalin ta ya yi mugun tashi, "ka kaini wurin Hajiya Umma, tsoro na keji, zan gaya mata bana aurenka na fasa kaji, zanyi abinda kake so." Shi ɗinma tausayi ta bashi nan da nan ya kai mata runguma, "Calm down mana Fatima, nifa ba wai na tafi na barki ba ne, kawai rainane ya ɓaci saina fita insha iska in saya wa Zuwairah Shawarma in dawo, Hold off ne akan hanya sosai amma wlh kina raina, hankalina yana wurinki tunda naga wucewar 30mns ban dawo ba nayi tunanin zaki fita ga shi bakisan gari ba kuma bakida lafiya a ido, plss calm down daina wannan tsoron kinji?" Tana ƙara kakkamashi ta ce,

"Na fahimta amma ka kaini gun Hajiya Umma, kaji zan faɗa mata abinda ka faɗamun"  Jannunta ya yi suka je har mota ya zaunar da ita sannan ya zauna, a hankali ya matsa kusa da ita ya rungumota jikinsa mamaki yake yanda ko ina na jikinta yake karkarwa, cikin takaicin yanayin fushin sa akanta ya ce, "Boɗɗo kiyi haƙuri kinji." Ɗagowa ta yi ta nuna masa goshinta duk da duhu ya sauka  ta ce, "Kagani ko, na buga goshi na jikin wani karfi, yanzu fuskana duka zai kumbura, idona zaimun zafi sosai kalar na ranar" Wayarsa ya haska ya duba wurin sannan yakai hannunya shafa, akwai magani da likita ya gayamun da zaran kinsha zai tafi, bara mu tsaya mu saya sannu kinji" batace komai ba harya gama siya wannan siya wancen suka je gida, a wannan daren Ali gaba ɗaya bai runtsa ba tunani ya ke wane irin mugun zuciya ya ke akan yarinyar nan? Anya babu wani abu kuwa kodai zai saka amasa addu'a ne, bazai yiyu ace akanta kaɗai yake saurin fusata ba, bama yanda za'ayi ace fushinsa yana ƙarewa ne akanta kawai.

*************
  *India New Delhi*

Tunda suka sauka a airport ake ta kuwace kuwace ana murna garin ya burgesu matuƙa, saidai boɗɗo sam bata ganin garin, gashi tana cikin fargabar komawa Nijar idan aka gyara mata idonta, Ali yana takura ta amma zamanta anan yafi mata kwanciyar hankali ta kula ba wanda ya ke gudunta sannan ba'a zaginta ko gulmarta, babu wanda ya ke kira mata mayya kai tsaye, bata shakkar zuwa koma inane, babu wanda ya san labarin ta, tashiga duniyar tunani kawai ta ji saukar hannunshi a nata, "Haba Fatima, kinsa lalurar ki sai kawai kiyita tafiya gaba gaɗi, ki riƙa jeruwa tare da mutane yanzu gashi kina ƙoƙarin hawa kan titi" Murmushi ta yi sannan ta ce, "Ayyah Hankali na ne ya ɗauku nagode Daddy" Zuwairah kallon hannun sa ta yi dake sarƙe a nata nan da nan ta ji wani ɓacin rai ya ziyarce ta, kallon Baraka ta yi sannan ta ce,

"Abiyaki ki kula  da ita sannan kuma aikin da ake biyanki akai ma sai Daddy ya miki, yaya zaki saki hannun mara lafiya ta hau kan titi? Wlh idanda wani abun ya same ta saina makaki bayan kanta kinyi bayani." Cikin ruɗu ta shiga bata haƙuri sannan ta matsa ta na ƙoƙarin riƙo hannun Boɗɗo datayi kasake hannun ta saƙale acikin na Ali tana sauraren su, jin duk anyi tsit ya sanya ta zare hannun ta sannan ta gyara tsayuwar ta ta ce, "Baraka zo muje ko?" 

   A hotel da suka sauka kuwa ɗakunan baccin su suna manne dana juna, shida Zuwairah ɗaki ɗaya Suit ne amma mai ciki da parlor da ɗan ƙaramin kitchen mai ɗauke da gas da abin gashi tare da ain ɗumama abinci, sai tukwane biyu da plates huɗu, akwai culinary set da komai da mutum zai buƙata, ɗakin su Boɗɗo ma komai akwai kamar wancen.

  *Bayan kwana 2*

Tun washe garin ranar da suka zo sukaje asibiti anyi gwajin ido da komai har an saka ranar aiki, kuma yau ce ranar tafiyar su a kwantar da ita asibitin, dan haka suka shirya dukkansu zuwa asibitin, direban daya ɗaukesu a asibiti ya ajiye Ali da Baraka da Boɗɗo, sannan Zuwairah da yara suka wuce masaukin Anty Yusrah datazo garin jiya ita da mijinta. Su biyu ne kaɗai a ɗakin dan Baraka ta basu wuri, ita tana wasa da yatsun hannayen ta shi kuwa ƙoƙari ya ke ya mata magana amma ya ras ame zai ce, da ƙyar ya tattara courage ɗin sa wuri ɗaya sannan ya soma magana,

"Jibi za'a shiga dake aikin da ƙarfe tara na safe, ni da Zuwairah da yara zamuje Dubai, bazamu daɗe ba sati kawai zamuyi gobe da sassafe zamu wuce so banaji zamu biyo ta nan, na barwa Baraka kuɗaɗe duk abinda kikeso zata miki, na karɓo miki sabon layin waya idan kinason wani abu ko magana  dani ki saka ta kirani." Kallon wurin da sautin muryarsa ke fita ta yi a kiɗime, "Amma meya sa zaku tafi duka ku barni? Meyasa bazaku bari idan akayi aiki munl tafi tare ba, yaa Ali ni tsoro nake ji, dan Allah ka tsaya mana." Sauke numfashi ya yi dan babu yanda za'ayi ya tsaya ɗin, "Haƙuri zakiyi kinga ko na tsaya babu abinda zna miki, sannan idan banyi hakan ba bazan samu ishashen lokacin danake so ba, na baro tarin ayyuka agida dole zan waiwaye su."

"Ni dai ka taimaka ka tsaya a gama aikin tukunna, wlh tsoron aikin na ke" Tasowa ya yi daga kan kujerar dayake zuwa kan gadon kusa da ita sosai ya kamo hannunta tare sa cewa,

"Ba rashin kulawa ba ne Fatima, kiyi haƙuri,idan naje ma sati kawai zanyi in dawo kinji, kawai ki kwantar da hankalinki kiyi addu'a kinji." Kukanta ta ƙarawa sauti hadda shesheƙa harga Allah tsoro ta keji, gani ta ke tamkar idan aka taɓa mata ido za'a birkita mata lissafi a ƙara dagulawa, shiru ya yi baisan dalilin dayasa Zuwairah ta kafe akan tafiyar su tare da yayarta ba, shida kanshi ya san bai dace subar wannan yarinyar da zallan ƴar aiki kawai ba, yanzu idan wani abu ya taso baya nan ya zai yi? Yama rasa dalilin da ya sa yanzu banda tausayi babu abinda take bashi.....

    "Me zai tashi hankalinki akan wata makauniya Zuwairah? Mijinki yana sonki ko makaho ya laluba zaiji hakan, har yanzu halin wannan baƙin kishin naki yana nan?" Nisawa ta yi sannan ta ce, "Ba haka bane ba, kawai yanayin yanda ya ke treating ɗinta ne ke bani mamaki, komai zatayi faɗa ne a gunshi saidai kuma ya dinga nacin magana ke nan akanta, kuma duk ranar daya hantare ta ko ya mata faɗa tofa zaki kula cewar baya bacci mai daɗi kuma, idan ya kwana 2 bai ganta ba ya dinga nacin tambayar yara ke nan akan ina take, yanzu dai haka na gaya miki akanta mukabi ta ƙasar nan, na tambaya ya ce cousine ɗin sa ce, suna kama ba shakka amma anty wlh niba yarinya ce alamomin so gaba ɗaya sun bayyana awurin Ali na yarinyar nan." Murmushi Yusrah ta yi, "Zuwairah ko dai kyawun nata da kike faɗa ne ya rikirkita ki haka, kinga duk yanda kika ruɗe wai." Ɓata fuska ta yi sannan ta ce, "Duk kyawun Baby da ake faɗa yarinyar ta ɗakko, wai ana zancen kyawun Ali to wlh baiko kama ƙafarta ba, kinsan Allah banama son kallon yarinyar nan tsabar ƙwarjinin datake mun, nifa shiya sa nakeso in tattare i nawa i nawa in tafi abuna nida mijina, wannan tsinannen idon idan ya warke saita ce bata san mu ba." Dariya sosai Yusrah ta yi sannan ta ce, "Tashi Muje in ganta nidai in masa sannu tunda kin nace saikin bimu dubai zamuje hutawa abinmu."  Jiki a sanyaye ta miƙe suka ɗunguma.

  Kukanta ya tsananta abinda ya soma rikirkita tunanin sa ke nan, matsawa ya yi daf da ita ya janyota jikin shi, "Haba mana Fatima, yanzu ke idan na gayawa Hajiya Umma kin tashi hankalinki kina ganin zataji daɗi?  Itafa bata burin daya wuce ki samu lafiya ki riƙa gani kamar kowa, yanzu lokaci ne daya da ce kiyi addu'a Allah ya sa a dace akan aikin nan" batace komai ba sai kukan data ragewa sauti,

"To yanzu ki bari zan saka a taho da Hajiya Umma jibi ranar da za'ayi aikin shikenan?" Da sauri ta ɗaga masa kanta, saidai bata daina kukan ba ragewa kukan sauti kawai ta yi, mayafin abayar dake kanta ya zame, sumar kanta ya bayyana, hannu yakai yana shafawa a hankali ta re da ci gaba da rarrashin ta, turo ƙofar da akayi ne ya sanyashi ɗagawa ya kalli ƙofar, da sauri ya zabura ganin Zuwaira da Yusrah, kuma duk sun kula da hakan, janye ta ya yi daga jikin sa, ya soma yaƙe, "Anty Yusrah sannun ku da zuwa" Da fara'ar ta ta amsa masa, sannan ta matsa kusa da mara lafiyar, ita kuwa Zuwairah ko taku ɗaya bata ƙara ba ta kafe shi da ido ranta a matuƙar ɓace!!

   Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora