SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU

380 68 2
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                    EWF
  
     *BILLY GALADANCHI*.

42.

Mahaufiyar Boɗɗo ka sa daurewa ta yi ta fashe da kuka sannan takalli Baffan ta ce, "Haba Malam, Haba Malam wannan irin cin amana ne, idan da wani aka aurawa yarinyar nan baa gida bane kazo kenan kanata faɗar maganganun, wato da kai da matarka har abada bazaku bari  Boɗɗo ta zauna lafiya ba? Wannan dukan da kake mata wani ta kashe maka? Kunya haukane da zaka kashemun yarinya ina kallo, har abada bazan manta ranar da ka ce idan na taimakae ta akan haihuwa abakin aurena ba, haka ka bari jinjirin ya mutu ka hana a binneshi, ita taje nabi sahu ta yi tono da faratan hannunta ta bizne yaron nan, akanta aka fara shege ta je ta yi shegen da saninta amma ku bakusan ƙaddara ba? Wlh na gaji, dole yarinya ta zauna zaman jinkiri da bayan jinkiri idan bazaka iya haƙuri ba ka tafi nika barni ka ɗebi matarka ku tafi ni inason yarinya ta" Waigowa ya yi ya ɗauke ta da mari saida taga wasu kyawawan taurari cikin faɗa ya ce, "Saboda kinga 'yan uwanki suna kusa, kina tsammani bazan iya nakasa ki ba ko a gaban waye? Inga uban da ya isa ya zo gidannan ya ce phatoum zata zauna zaman jira, saida ta yi jiran a lahira dan wlh kashe zanyi" Hajiya Umma ce ta jinjina kai sannan ta ce,

"Wato wannan shine dalilin da ya sa tun farko banso wannan auren naki da mutumin nan ba, kanada mantuwa malam, wlh kanada mantuwa mai girma, ka ke cewa duk faɗin garin nan itace ta yi shege amma ai ubanta ne ya farayin fyaɗe kafin fyaɗen azo a rama akan ƴarsa, shin kanada ilimin akan tabbacin cewar duk wanda ya yi zina da ƴar wani sai anyi da tashi? Kuma idan har ba'ayi da zuri'arshi ba sai anyi da koda bangon gidanshi ne, abinda kayiwa uwar Phatoum kafin ka aure ta shine akayiwa phatoum ɗin maganar Allah wasa ne? Da aka tashi baka kaji kalan zafin da namu mahaifin ya ji sanda kayiwa uwarta fyaɗe sai aka haɗa maka da ciki, yaro na ne yayiwa Fatima fyaɗe kuma shima na gaya masa saiya gani idan har bai tuba ban sannan ni da ya mata fyaɗen tsine masa nayi? Ire iren ku kune kuke ƙara gurɓata al'umma dan yanzu idan mijin bare ne saiya ce ya fasa idan kuwa ka bata wannan auren wanima idan ya zo haka zaka ɓata daga nan idan ta gaji sai shiga duniya, yarinyar nna ba laifinta ba ne ba, meyasa bazaku tausaya mata ba? Ƙara harzuƙa ya yi yanzu kam ya soma masifa, "Nawan ma ai ƙaddara ne, kuma  kunsani bazaki ɗaura alhakin abinda ya faru da ita akaina ba dan ita shege ta yi" Kawu Bala ne ya karɓe zancen da cewa, "Kaga Malam, ka yarda ko karka yarda ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙiya, daga yanzu babu kai babu rayuwar ta mu zamu zame mata gata, saidai fa ka sani wannan gidan namune? Da kai sauran matanka da yaranka ku fice tunda kai bazaka zauna da phatoum ba ita mukuma iyayenta muda mukeda gidan mun buƙaci ta zauna dan haka ko sa second bazamu kara maka ba, An haɗaka da Allah kaƙi do le ne mu bi ka ta hanyar da ka ke so mubi" Bori ya fara "Ba inda zamuje wlh, ai nan muka saba da shi ko? Akan mutum ɗaya sai a kori rai sama da ashirin dan ana taƙamar bamu da shi" Matsawa ku sa da shi kawu bala ya yi sannan ya ce, "Tun duniyar waccen data gabata nike ma uzuri, bakada hankali malam kuma bakasan kunya ba, anyi maka kara har an gaji mutanen da ake maka kara akansu yanzu basa raye sun mutu, idan baka mayarda hankalinka wlh wulaƙanta zanyi, yarinyar nan an sanar maka ga abinda ya faru idan ka yafe shikenan ta dawo ta yi zamanta kuma banda takura ba, idan baka yafe ba ku kwashe   kayanku ku bata wuri gidan uwarta ne ina?" Muzurai ya shiga yi saikuma ya sakko "To dama ai ni ba'a mun bayani bane na zata kuna faɗa ne kawai dan ku kare ta yanzu na fahimci nakomai, shine Allah ya mata albarka, a nemosu su sawo ɗin" Kallon nutsuwa kawu Bala ya masa sannan ya ce, "Ka tabbatar zaka mutunta mana yarinya komai ya wuce idan fa na samu saɓanin haka wlh zanyi tijara mafi muni a gidannan" Washe baki ya yi "Haba Bala? Ya zamu dawo nan kuma? Ai na wuce wurin har abada" Nan suka koma ciki akai masa bayani sosai sannan Hajiya ta kirawo Ali inda ya tabbatar mata sunje masauki ne, anan ta ce su dawo ba dan ya so ba ya dawo ɗin.

************
    Dukda akwai wuta a ƙauyen amma babu agidansu Boɗɗo dan haka Ali a wannan wunin ya tabbata anja wutar nepa dama su ta kuɗi ce, maganar ruwa kuma akwai dan haka bassuda matsala. Inna kuwa tamkar zata mutu ganin cewar Fatima ta samu jin daɗi, hadda ido yaushe ta fara gani? Yarinyar data watsawa ruwa kuma antabbatar mata indai wannan ruwan ya taɓa idonta bazasu ƙara ganin haske ba har abada? Kayan abincin ta da ƙwalam duk a ɗakin suka tare, Inna kuwa nan ta hau masifa akan ai 'yar fari ce ɗakinta zata sauka, anan mahaifiyar Fatima ta kalleta cikin mamaki ta ce, "Boɗɗon ce zata zauna a ɗakin ki? Sanda ta samu waccen cikin a shekarun baya daya akai ki zauna da ita a ɗakinki kikace mayya ce? Mayyar yanzu kike so ta zauna miki bakya tsoron ta cinyeki" Baki ta kama "Aa Lallai rashin kunyarki ta nunaa a fili, ya tabbata bakida kunya, yanzu ke Phatoum kike tarewa faɗa" Harara ta cilla mata a karo na farko tun zamansu sannan ta ja tsaki ta ce, "Kinga Inna idan bakida abinyi ni inada shi, yarinya dai ba inda zataje, wurin uwarta zata zauna" Boɗɗo sai binsu da ido take har Inna ta gaji ta juya.

*Bayan kwana ɗaya*

        Ali ya zo yiwa Fatima sallama amma ƙememe an hanashi ya ganta, wai idan yarinya ta zo wanka shikenan miji bazai ƙara ganinta ba sai ta haihu kuma, abin ya bashi mamaki danshi bai gama gaya mata abubuwan dayakeso ya gaya mata ba, anan ya matsa dole suka bashi aron matarsa, tana shiga motar kuwa ya figeta sai masaukin sa. A ɗakin Boɗɗo sai ƙin kallon sa ta ke dan sarai ta san ma'anar zuwansu anan wurin, hannun ta ya riƙo "Tee queen meye haka? Kinata shareni" Kallon sa ta yi "Kasan halin mutanen ƙauye, dan Allah ka mayar dani gida" Fuskarta ya shafa sannan yakai hannun sa har saman cikinta yana shafwa ya ce, "Gobe zan tafi Fatima, sabosa haka wannan ranar duk tawa ce, ni a wurina sai yau zan kaiki gida, zanyi  tsananin kewar ki" Murmushi ta sakar masa "Toni mezan maka?" Fuskarsu ya haɗe wuri ɗaya ya shiga goga hancinsu a tare yana murmushi sannan ya ce, "Na kwaso ruwa Fatima, kimun izinin in juye miki su tas a mara" Runtse idonta ta yi sannan ta ce "Har sai yaushe zaka fara jin kunya ta wai? Yana ƙyalƙyala dariya ya ce "Oho Allah masani" Nan suka afka sabuwar duniya, dukda sun ƙoshi amma tunanin kewar da zasu shiga ya hanasu rabuwa da juna haka sukaita abu ɗaya har la'asar. Daganan kuɗaɗen ƙasar ya bata masu yawa, sannan ya ce, "Munyi zagaye na samu wanda ya iya gashin kaza na biyashi kuɗin sa duk kullum zai aika mikingida biyu da dare, a booth akwai lemuka irin wanda nasan kinasha ance akwai yalwar ƙanƙara amma plss karki hayewa shan abu mai sanyi, kiyi haƙuri tare da kawar da kanki akan kome zakiji ko ki gani haka rayuwar take wani zubin, kiyiwa mahaifinki uzuri, akwai shinkafa, taliya, macaroni, wakenda dai indomie duk a booth, na sayo miki camp gas kuma anyi refilling nashi so idan ma ya ƙare ki bayar a saya miki, akwai ƙwai shima cr8 takwas idan ya kare akwai kuɗi a hannunki, eat healthy bake kaɗai kike ba, kinji"  Hawaye ne ya fara silalo mata a hankali ta fara rero godiya da addu'a sannan ta ce, "Inka tafi yaushe zaka dawo?" Shiru ya ɗanyi sannan ya ce, "Sai watan haihuwarki Fatima, akwai Surgery da za'a yiwa Honey a zuciya kuma lallai zai zamana ina tare da ita kema kinsan hakan, so zamu bar ƙasar atare, u makesure that kin mata yau ɗinnan kin mata sannu saboda batajin daɗin, ki mata nasiha ta saka tsoro aranta a kan aikin ko zata samu nutsuwa" Addu'a ta musu sannan suka shirya tafiya gida.......

Mom Nu'aiym.

GINI DA YAƁETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang