SHAFI NA ARBA'IN

391 56 5
                                    

  *GINI DA YAƁE*. FREE BOOK

                    EWF
 
  *BILLY GALADANCHI*

    40.

Gaba ɗaya ruwa aka saka mata, na wannan daren sannan ta samu kanta, washe gari wuraren 7 Ali yana ɗakin dama anan ya kwana, sanda ta buɗi ido ta ganshi wani irin haushin sa ne ya kamata ta yi azamar ɗauke kanta daga dubanshi, hannun ta da babu kanula ajiki ya kamo sannan ya na shafa sumar kanta ya ce, "Fatima" Bata ko da kalleshi ba ta ƙara tamke fuska sannan kuma bata amsa mai ba, cikin tsananin rauni ya soma magana..."Teemah na dan Allah kiyi haƙuri, wlh ba wani abin nake nufiba da wannan sharekin kawai raina ne kika ɓata, yanzu idanda kin illata kanki a wancen lokacin ya kikeso in rayu ne ehm?" Nan ɗinma bata waigo ba, sunkuyawa ya yi kusa da ita sosai har suna jiyo bugun zuciyar juna sannan ya ce, "Fatima na ji nayi laifi ta kowace siga, na yarda tun daga farkon sakaki a ido da nayi kawo wannan lokacin duk laifina ne amma dan Allah kimun uzuri irinna zamtowar ɗan adam da ajizanci ki yafemun kinji?" Ƙamshin jikinsa ya soma tasiri ajikinta, ɗan musƙutawa ta yi zuwa rigingina ya kai hannunsa ya shafi cikinta zuwa mara, "Babyna kikaita nausa haryaji ciwo a hanci shiyasa nayi fushi, kuma na tabbatar wannan lallausar fatar taki ma saida ta yi rashes alamar duka, mesa zaki azabtar da kanki da babynmu amaimakon ni ki azabtar dnai tunda laifin nawane?" Nurse ce ta shigo hakan ya tilasta masa janye jikinsa ta cire kanula ɗin tare da gaya musu zasu iya zuwa gida an sallamesu.... Bayan sunje gida ma taƙi ta ci taci abinci saida Zuwairah ta mata faɗa sannan ta ci indomie da farfesun naman rago, saidai yunwar mai ciki ba wasa dan kuwa ta ci sosai fiye da ƙima.

    Da dare koda yazo kwanciya ta jwanta abinta ta juya masa baya, amma fitila a kunne saida ya kammala dukkan shirin sa sannan yaje parlor ya janyo wata kula ya buɗe tare da zaro abinda ke ciki, nan da nan ƙamshin tsiren ya baɗe ɗakin abinda ya tabbatar bazqta iya haƙura da shi, gefe ɗaya ga kilishi yasha yaji irin mai kitse ɗin nan abin sam barka, numfashi ta ja sannan ta kanne taƙi tasowa, ganin haka ya sanya ya ce, "Teemah na zoki ga tsire na saya miki karya huce nasan mai zafi kikeso" cikin haushi ta ce, "Na ƙoshi" jin hakan ya sanya ya tabbatar haƙarshi ta kusa cimma ruwa! Murmushi ya yi sannan ya ce, "Dame kika ƙoshi Tsiren wai?" Banza ta mai ya taso ya zo kusa da ita, "Fatima" ya kira sunanta, hannu ta kai ta toshe hancin ta sannan ta rufe idonta, bata ƙaunar shaƙar ƙamshin sa saboda zai bata ita, bata burin ta sauka daga dokin fushin data ɗauka da Ali, ganin abinda ta yi ya tabbatar masa wannan karon ma bazaici nasara ba, zuwa ya yi ya rufe naman ya mayar a kula dan idan ya huce bazata ci ba tabbas. Kusa da ita ya dawo ya durƙusa sannan yakai hanun shi ya soma shafar gefen kanta a hankali, cikin muryar sa dake barazanar razanar da ita dan kuwa daf yake da fashewa da kuka ya soma magana, "Fatima badan halina ba na tuba ki gafarce ni, dan Allah ki haɗa duk abinda na miki ina roƙon alfarmar afuwa daga gareki ina roƙonki daki yafemun duk abinda na miki wanda na sani da wanda ban sani ba, dabara ta ɓacemun Fatima, wannan fushin da kike dani ji nake tamkar zan mutu, banida sukuni Ko kaɗan, na ɗauki tsawon lokaci ina fargabar zuwan ranar da zaki gane nine mutumin da kike yiwa baƙar addu'a kowace safiya, nine sanadiyar rushewar jin daɗin rayuwar ki shekaru masu yawa, nine mutumin daya tilasta miki haihuwar ƙuruciya ke kaɗai tare da fuskantar barqzanar ƙiyayya takowa ne lokaci, nine mutumin dana haddasa miki rayuwar kaɗaici acikin rashin walwala, wlh Fatima da ace hukuncin kisa ba babban laifi ba ne wlh da wannan kunyar taki dake kaina dana kashe kaina na huta da wannan baƙin cikin, wlh da inada yanda zanyi in rayu wata duniyar da bazan ƙara haɗa ido dake ba dana aikata hakan, ina kallo kika zamar mun jinin jikina, inaji ina gani kika zama wani sashi acikin jikina da bazan rayuba idan har babu ke, Fatima wlh ina sonki fiye da yanda kike tunani, ina ƙaunar ki fiye da  yanda nike ƙaunar kaina, dan Allah ki yafemun? Dan Allah ki soni, dan Allah ki ƙaunace ni, dan Allah....  Hawan jini yana nema yamun illah Fatima, zuciya ta tana barazanar fash..... Saikuma ya yi shiru saboda yana neman bada maza, kukan so yana neman ya ƙwace masa da sauri ya miƙe ta re da juyawa ya fita a ɗakin na kusan mintuna goma, saida ya dadaita kansa sannan ya dawo ya ragewa fitilar ɗakin ƙarfi sannan ya kwanta a bayanta ta re da rungume ta ta bayanta, lafewa ta yi acikin hannun sa yakai bakinsa ya sumbaci bayan sumar ta sannan a hankali ya ce, "Kin yafemun Fatina?" Ita ɗinma a hankali ta gyaɗa masa kanta, cikin muryaan kuka ta ce, "Yaa Ali ka yi haƙuri na saka ka kuka, bazan ƙaraba kaji" Runtse idonsa ya yi tare da matse ta sosai ajikinsa yanajin wani sonta yana ratsa ilahirin jikin sa, cikin wani shauƙi ya ce, "Ke zan baiwa haƙuri Fatina, banida burin da ya wuce faranta miki" Shiru sukayi atare yaci gaba shasshafa jikinta cikeda so, har bacci ya kwashe su.

*Bayan wata biyu*
     A wannan lokacin cikin Fatima ya doshi watanni shida, danya fito ya yi girma, rana tsaka kawai saiga Hajiya Umma a gidan, kowa ya shiga taitayin shi, bayan ta yi kwana biyu ana haba haba da ita, dan kuwa saida ta ji tamkar ta mayar da Zuwairah aciki saboda tattali ta kira Ali da Fatima a ɗakin fatima, sannan ta kalli Ali ta ce da shi, "Yaro gobe zan koma Niger, kamar yanda na gaya maka shanaye sun girma sosai akwai na turawa aciki, kuma sunada tsada sosai a ko ina, gidan gonar da mukayi magana ya kammala, injinan dakace  kawai ake jira"

"Umma inshaa Allah wani watan zasu zo a tsakiyar sa, indai ba wata matsalar aka samu ba kuma bana fata" Jinjina kanta ta yi sannan ta ce, "To kuma kasan al'adunmu dana cen da banbanci saboda haka da Fatima zan tafi a ƙa'ida ma zata koma ne da zaran ta samu ciki to amma yanzu zata koma gida sai ta haihu yaro ya yi watanni shida sannan zata dawo" da sauri ya kalli Hajiya Umma sannan ya ce, "Hajiya maganar shekara ɗaya ake fa? Gaskiya dai hajiya ni wannan al'adar tunda ba addini ba ne bazan iyaba, ko wata ɗaya bazata yi batare da niba bare shekara ɗaya" Wani kallonta wurga masa wanda ya bashi tsoro sannan ta ce, "Ohh kanaso ke nan ka gayamun dai kai ga mai mata, ba inda zanje sa matarkanko?"Ɓata fuska ya yi, "Ba haka nake nufi amma Hajiya a duba wannan maganar, yarinyar nan bazata iya zama inda ba AC ba tanada jin zafi wallahi, bayan haka tana son cin shawarma da pizza kullum, gashashiyar kazar garin nan kullum dashintake breakfast ana mata warming, bayaga haka kuma..... Sai yayi shiru ya kasa ƙarasawa, cikin mamaki Hajiya Umma ta ce, "Ina ji bayaga haka sai me?" "A to Hajiya Itafa sam idan ba shaƙar ƙamshin turaren jikina ta yi ba bata iya bacci shiyasa ma gaba ɗaya Zuwairah take cewa saidai na kwana mata" Miƙewa Hajiya Umma ta yi kafin ta ce, "Duk wannan haukar surutun da rashin kunya a kanka zai ƙare yaro, ni banida lokacin ɓatawa anan, magana ɗaya dai yarinyar nan gobe ƙafata ƙafarta idan ta ce garin nasu ko ruwa karta sha harta dawo wannan ruwannta, marasa kunya kawai" Tana kaiwa nan ta yi gaba abinta, Ali a ruɗe ya kalli Fatima, "Queen teetee wai kinsan hajiya Umma kuwa? Wlh bata sauya maganar ta, idan ta tafi dake ya zakiyi da cimar da baki saba ba bayan haka ina zaki samu AC dakike so? Fatina ina zakiga shawarma ko anaci a ƙauyenku, bafa a agadaz zaki zauna ba ko maraɗi ko yamai ko? Ni ina zanyi rayuwar shekara bakya nan?" Idanta ya cika da ruwa sosai ta ce, "Na kwana biyu banje ƙauyenmu ba shekaru sama da bakwai rabona da ƙauyen bansan wanne ci gaba suka samu ba amma la shakka ko wutar nepa babu a ƙauyenmu, bazan iya mata musu ba kayi haƙuri" Miƙewa ya yi tsaye, "Kina hauka ne? Bayan duk abinda likita ya faɗa ya zan bari kije haihuwa a kauye?  Gaskia bazai yiyu ba.

   Washe gari tun takwas na safe Hajiya Umma ta fito kowa ya zo rakiya banda Fatima Ali ya hanata, kallon sa ta yi kowa ya yi cincirindo banda Zuwaurah da suka yi sallama ta fita tun wurin bakwai, "Ina Boɗɗon ta ke? Karmuyi dare a hanya" Fuskar sa nan da nan ta sauya ya ce, "Amma Hajiya Jiya aina miki bayani komai ko?" Wani kallo ta wurga masa ta re da cewa, "Wlh yau dai ƙafata ƙafar Boɗɗo baza'ayi abun kunya akai na ba, na bata mintuna talatin da tattaro duk wani abu mai muhimmanci nata ta fito mu tafi, kuma wlh ban yarda ka sake yin magana ba" Hannu ya ɗaura akansa nan da nan idanshi ya yi ja, masu aikin suka fara tserewa ganin ogansu na shirin fasa kuka kome yayi zafi oho... Haka ya tayata haɗa jaka suna yi suna kuka bamai rarrashin wani...

Ali kenan baban soyayya!!!

**MUNADA GIDAUNIYAR NEMAN TALLAFIN CIYARDA MARAYU DA MARASA ƘARFI A WANNAN LOKACI NA WATAN RAMADAN MAI GABATOWA, SADAKA BATADA YAWA BATA KUMAYIN KAƊAN, DAN ALLAH KU TAIMAKA DA ABINDA YA SAWWAƘA A WANNAN ASUSUN AJIYAR.*
0724155958
ACCESS BANK
BELKISU YUSUF G.

 

GINI DA YAƁEWhere stories live. Discover now