*🤷♂️ADDININMU🤷♂️*
*(By S. REZA)*
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
*ADDININMU*
*PAGE1️⃣2️⃣*.........Haka sojojinnan suka tasa ƙeyar Innah da Nana har bakin motar Police ɗin da suka iso gurin, al'ummar unguwar kowa yafito yana kallon ikon Allah, wasu daga cikinsu kuwa kuka sukeyi ganin yanda Innah tayi kamar wacce bata cikin haiyacinta. Nana kuka Innah kuwa ta kasa magana tsabar ruɗewa. Babu ko imani suka turasu a cikin motar sannan sukayi gaba. Ana zuwa police station babu wani bincike saboda ganin wanda ya kawosu, haka Daddy yasa aka turasu cikin sell sannan ya kalli police ɗin daya ƙarɓi ƙarar ya ce "Kar a sake a bada belinsu harsai yaron yazo gidana da kansa. Cikin sauri police ɗin ya ce "Yes sir. Daddy ya bar police station ɗin cikin ɓacin rai. Bai taɓa kawo cewar Sahra zata iya satar masa kuɗiba, dama yasan saide wani ya zigata wanin ma wai musulmi mai Sallah shine yake tura yarinyata tana satar min kuɗi!! Haka Daddy ya shiga mota yana tinanin idan ya kama A.J Allah ne kaɗai yasan abunda zai masa.
*SALIS. LAƊIFA. POV*
Bayan Hajiya Babba da A.J sun tafine Salis ya koma cikin gidan domin yin mgn da laɗifa, amma taƙi buɗe masa ƙofa, hakanne yasa ya kira Nana yace mata yana zuwa, dama sunyi a kan zasu haɗu idan AJ ya tafi. Aikuwa bai bar ƙofar gidan ba sai wajan ƙarfe biyu, sannan ya ce zai tafi, amma gobe da safe zai kawo mata kyutar bazata. Haka sukayi sallama ya tafi gida cikin farin ciki.
Laɗifa kuwa abubuwan ne suka haɗe mata biyu. Ga haushin A.J da takeji wanda batasan meyasaba, gakuma haushin hanata zuwa club ɗin da Salis yayi jiya, tabbas taso taje tasake haɗuwa da wannan gayan, kodan tasamu sukuni a zuciyarta . A kowani lokaci idan zatayi ƙoƙarin kawar da tinaninsa sai taji soyayyar sa na ƙaruwa a zuciyarta.
Tana cikin hakane wani tinani ya faɗomata, aikuwa afili tace "Tabbas shine Walhi shine, take ta shiga wanka domin kuwa gurinsa zataje, to amma ai tamasa rashin mutunci, take abunda ya faru tsakanin ta da Umar abokin Samuel ya shiga dawo mata a kanta.
Fitowarta keda wiya daga gidansu ƙawarta Yusra wacce ke unguwar su Umar ɗin ne ta hango wani saurayi shida wata budurwa a jikin motarta suna hira. Kallon gurin tayi cikin tsananin mamaki ta ce "Yusra kinga irin abubda yasa bana son zuwa unguwar ku ko? Yanzu-yanzu daga ajiye motar har wani wawa ƙazami zai ɓatamin Itaki? Ai kafin Yusra tayi magana har Laɗifa ta kai gurin da Umar ke tsaye.
Yana cikin hirarrsa irin ta mayaudara yaji muryarta tana cewa "Uban waye ya baka izinin tsayuwa a jikin motana?. Dagashi har yarinyar da ya tare yake zuba mata ƙarya akan cewar motar sace suka juyo suna kallon ta. Kafin suyi magana ta ci gaba da cewa...inbanda hauka da rashin tunani daga ganin mota sai kawai ka zoda wani ƙazamin kayanka ka jin gina ajiki, kalleka fa kamar wani ɗan almajiri wai kai saurayi har kana kawo budurwa jikin motana.
Cikin jin kunya Umar ya kalli yarinyar da ya gama shirya mata ƙarya, zaiyi magana taja wani dogon tsaki mtsiiiiiiii sannan ta bar gurin. Laɗifa ta ce Mlm kobazaka ma tsa bane? Umar kuwa ya kasa magana tsabar kunya haka ya bar gurin motar yana sosa kai ya kasa magana, amma abunda tamasa ya tsaya masa a'rai.
Laɗifa tace "Sune irin ƴan isakan samarin da suke zuwa wajan ƴan Mata da yaudara, kukuma kuna jin zancen su saikuyi sauri kuce kun amin ta dasu, daga baya kugane ashe matsiyata ne. Yusra ta ce "To mlm bansan iskanci ni kinga ina kula irinsune? Kuma wannan ma ai ɗan unguwar nann ne kinga gidansu can? Laɗifa ta ce "Au shi ƙaryar tashima har a unguwarsu yakeyi? Yusra ta ce "Tom kindai gani.
Ajiyar zuciya Laɗifa ta sauke tana tinanin cewar to idan taje gurinsa me zatace masa! Nan take ta kawar da wannan tunanin ta shirya domin zuwa gurin Umar. Tayi niyar zuwa a yau amma ta bari sai gobe.
ESTÁS LEYENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AcciónThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3