Chptar 19

10 3 0
                                    

19

Kallonta yayi da kyu cikin wani sabon mamakin da tun da suka haɗu take bashi ya ce "Hajiya ban gane me kike nufiba? Hajiya Babba ta kalleshi itama cikeda sha'awar sa ta ce "Inaso muyi sati biyu a nan in yaso muna komawa 9j shikenan kaci kuɗinka. Ta faɗa tana dariya. "Kina nufin daga haka mun gama auran kenann? Hajiya ta ce " Eh haka nake nufi. Cikin tsananin mamaki da farin ciki AJ ya shiga tinanin abubuwan da zaiyi idan ya mallaki wannan kuɗaɗan a cikin kwana goma sha huɗu kacel. Hajiya ta ce "Bakace komai ba? Ya ce "Na amin ce, saura kwana goma kenan ko? Hajiya ta ce "A'a daga gobe kwana zai ƙare. Ya ce "Na amince". Tunda suka zo ƙasar Morocco Hajiya Babba bata ga farin ciki a fuskar angon nataba sai yanzu, domin kuwa ya dawo kamar ba AJ mai surutu da abun dariya da fara'a ba, tashi tayi ta kama hannun sa tana masa alama da ido. Kaman yanda suka saba kullum Hajiya saita buƙaci mijin nata sau huɗu a rana, wani lokaci ma har fiye da haka, shikuwa gogan naku tun bai saki jiki da itaba har ya ware shima yake ɓarzar abarsa, domin kuwa da yana tsoro kar wani abu ya faru idan yaran ta sun gane, amma da yaga ita ko a jikinta sai kawai ya fara abubuwan da takeso, dukda kuwa yana shan wahala domin kuwa wani lokacin har fita yakeyi a haiyacin sa.

Yauma abun da ya faru kenann domin AJ ya nunamata cewar yau fa yana cikin farinci, warewa yayi suka sha love da ƴar tsohuwar abokin nasa, amma fa saida ya gaji ya barta, saida taji ta gamsu kafin ta yayyafa masa ruwa ya farka.

******
SALISU
Yakira numbar AJ ya kai sau goma amma bata shiga, sai kawai ya nufi police station ɗin cikin sauri domin kuwa gabansa na faɗuwa. Da sauri ya shiga gurin yana kallon sabon ɗan sanda da ke tsaye a gurin ba wanda ya saba ganiba, kasan cewar police station ɗin tsohone babu wasu ma'aikata a guri sai ƴan kaɗan hakanne yasa gurin ko mai gadi babu. Ɗan sandan ne ya tareshi yana cewa "Lafiya daga ina me kake nema? Salis ya ce "Wasu mata da suke cikin gurinnan ɗazu sunake nema?".

Cikin mamaki ɗan sandan ya ce "Kaine AJ?" Salis ya mai-maita sunan kafin ya ce "Please ina police ɗin da ke gurin ɗazu?" Cikin ɓacin rai police ɗin ya ciro waya yana dannawa kafin a ɗaga ya ce "Police ɗin dake gurin nann kuma an koreshi a aiki, sukuma wanda kazo nema an sake musu guri.

Cak Salis ya tsaya yana kallon police ɗin cikin mamaki, Salis ya buɗe baki zaiyi magana ya ji ɗan sandan na cewa "Yes sir ga wanda yake kawo musu abincin yazo, ina tsammanin ma shine AJ ɗin. Police ɗin yayi shiru yana ƙamewa a gurin kamar wani gunki yana sauraron abunda a ke cewa daga cikin wayan. Saida ya gama jin abunda a kace sannan cikin tsantsar girmamawa ya ce "Yes sir an gama". Salis dai sai kallonsa yake cikin mamaki.  Yana gama wayar ya kira wasu ƴan sanda ai kuwa nan take suka maƙala masa onka, suka turashi a cikin sel ɗin da su Innah suka fita. Yana tambayarsu lafiya amma ina saida suka turashi.

Laɗifa kuwa Salis na fita daga gida itama ta shiga ɗaki ta shirya ta ɗauki ATM card ɗinta ta shiga kiran numbar Umar. Bayan Umar ya ɗaukane ta sanar dashi cewar yazo ya karɓi kuɗin ya kai. Cikin murna Umaru ya amsa kafin ta sanar masa da gurin da zasu haɗu. Shuru tayi tana tunani. Shin meyasa Salis yafi damuwa da matsalar su yarinyar da zai aura! Bayan ga matsalar da nakeciki, kuma yasan cewar ina sonsa. Wata zuciyar ta ce "Shima saboda yana sontane,  kamar wacce take zance da wani ta ce "Ok hakane shima sonta yakeyi ko, shine yasa ya manta da tawa matsalar ko, to Walhi nima saide duk abunda zaifaru yafaru, badai abunda yafaru a baya bane zai ƙara faruwa muda Daniyel to walhi muje zuwa. Tana kaiwa nann ta nufi gurinda zasu haɗu da Umar. Tana tafiya tana tunani abunda ya faru tsakanin Daddynsu da Daniyel, ita ai ta wani gurinnan abun ya mata daɗi, domin yanajin cewar ai ta samu Samuel ta gama, tinda ɗan gidan  Daniyel ne, dariya tayi tana godewa Allah da abun yazo mata cikin sauƙi.

Jiniyar motocin sojojine ya karaɗe ilahirin unguwar da babu wasu mutane a cikinta sai ƴan ƙalilan kasan cewar a bayan gari gurin yake. Babu mota ko ɗaya da ta samu damar shigowa gurin kasan cewar gurin baida girma kuma ga wata tsohuwar mota a gurin ita kadai ma ta cika gurin. Parking sukayi sannan sojoji suka fara durgowa daga cikin kowacce mota kamar wanda suka zo filin yaƙi. Babban sojan barinkin garin wanda a wannan watan yake cika shekaru biyu da samun ƙarin girma daga wani muƙamin zuwa wani, wanda a yanzu haka shine Comandar ɗin duk wani sojo dake wannan state ɗin. Kaman yanda kowa yasani mutumne mara imani ga tsan-tsar kishin addininsa wato addinin Christian, mutumne mai ƙiyayya ga duk wani wanda ba ɗan addinisuba, hakanne yasa ya samu matsala da manyan ƴan kasuwar dake garin Benue makordi wanda suke musulmai, domin ya hana su sakewy.

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang