Chptar 43

10 1 0
                                    

*S REZA...✍️*

*ADM*

*First Class writer's asso...*

           *PAGE4️⃣3️⃣*
........Haka Salis ya bar ƙofar gidan cike da damu wa a ransa, baya son ya taƙura Mata, zai bata dan lokaci kafin komai yayi daidai. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta ko wani ɓangarori. AJ ya koma aikin sa na  tuƙa motar bredi wanda suɗinma da ƙyar suka ɗauke shi a kan suna da ma'aikata, yaci sa'ar dai ya taɓa aiki a gidan ne kuma lokacin da yayi aikin basu taɓa gamashi da wani laifi ba. Dubu goma za'a dinga biyansa duk wata ɗaya, haka ya nuna farin cikinsa sannan ya kama aikinsa ba wasa. Ita kuwa Nana kaman yanda Aj ya ce ta kama kanta ta riƙe maraicinta ta nutsu ta mai da hankalinta a kan karatun ta, hakan tayi domin bin maganar Yayan nata. Wayar hannunta  ya karɓa ya sayar, da kuɗin wayar ya sayo musu duk wani kayan buƙata domin   yace bazai kwaso nasu na da ba. Rayuwa ta yi musu tsanani sosai, hakan kuma baisa ya nunawa ko wa cewar yana cikin damuwaba, harta kawunsu baisan da haka ba,  wani lokaci abunda zasucima wahala yake musu, ɗan sauƙin abunma a kullum yana zuwa da bredi kida, daga ƙarshe ma Nana daina zuwa school ta yi, sai islamiyya, shiɗinma dai ana binsu bashin kuɗin wata. Duk da haka ya ce duk lokacin da Hajiya Babba zataje asbiti to baya buƙatar suyi amfani da komai nasu. Da farko Muhammad bai yardaba amma ya ga AJ ɗin kamar hakan yakeso, hakanne yasa komai idan za'a yi sai an sanar masa, albashin sa na farko ma a kan yaron ya tafi, hakan ma dan an rage masa kuɗin ne. Izuwa yanzu rashi da damuwa sun fara nunawa a jikinsu, duk da irin halin da suke ciki bai hana Kadija gabatar da kanta a gurinsa ba, amma ya mata kace kace ya ce idan a kan haka take zuwa gidansu to karta ƙara zuwa. Yanzu yana yawan zuwa gidan kawunsa kuma duk lokacin da zaije sai ya ruƙo musu bredi ya kai musu. Har Wannan lokacin bai manta da Sarah a ransa ba amma yasan babu komai yanzu a tsakanin su, yanzu itama ta daina kiransa , sai kawai yaji baiji daɗiba. Lokacin da abubuwa suka rincaɓe masa sai kawai ya siyar da wayarsa ya sayo ƙarama, kuɗin wayar kuma ya fara siyan kayan jinjiri, sannan ya biya wa Nana kuɗin school taci gaba.  (Wannan kenan)

*ABDALHA POV*

Kamar da wasa abubuwa sun chakuɗe masa, Duk gurin wanda yake ganin zai tayashi domin shawo kan mahaifinsa a kan lamarin auransa amma abun yaci tira. A kan wannan abun yasa iyayen nasa sun samu matsala, yanzu haka mahaifinsa ya cire hannunsa a kansa gaba ɗaya, yanzu haka ya dawo gidansu da zama kasan cewar bashi da lafiya, ciwon zuciya ya sa shi a gaba, Daddy yayi tunanin Abdullah yana yin hakane domin ya amince da auransa , baisan cewar ɗansa ya faɗa cikin kokin love ba. Wayarsa ya ciro yana daga kwancen ya nemo numbar Isa, kira ɗaya ya ɗaga yana sallama.

"Yauwa Isa ya kukayi da shi? Yayi tambayar cikin Muryar da kanaji kasan yana cikin wani hali.

"Isa yaja doguwar ajiyar zuciya ya ce "Wallhi kunyarsa nake ji, bansan da wani ido zan kalleshiba, bansa ma mai zance masa ba.

"Kwana nawa ya rage? Cewar Abdalha yana lumshe idonsa?

"Kwana takwas? Ya bashi amsa yana jin babu daɗi ga tausayin halinda Abdalha ke ciki.

Azuciyarsa ya furta "Takwas! Sai ya kashe wayar yana jin cewar dama haka a ke ji idan kana son mutu! Gani yake babu wanda ya taɓa jin irin abunda yakeji a kan Zainab, sam bai yarda da cewar wani ne zai aureta ba, yana mata son da zai iya ja da kowa domin mallakatarta, gani yake shi nashi salon son daban yake, duk lokacin da ya tuno da cewar auranta saura kwanaki kaɗan sai ciwonsa ya tashi. Numbar ta ya kira yana jin cewar zai samu mafita daga gareta.

*ZAINAB POV*

Mutuƙar wannan auran da zatayi zaisa mahaifinta farinciki kamar yanda ya ce, to tabbas zata auri Aliyu badan tana sonsaba, zatabi zaɓin mahaifinta kodan ganin yayi alfahari da ita kamar yanda ya ce, ta yarda da cewar tana son Abdalha kamar yanda  yake sonta amma wani ƙaramin abu ya shiga tsakani yayi baƙe-baƙe babu damar kaucewa. Hirar su da shi ta jiya ta tuno lokacin da ya ke ce mata "Kar zuciyarki ta raya miki cewar zaki auri wani baniba, domin haka bazai taɓa faruwa ba, kisa a ranki nine mijinki, bansan soba sai a kanki, haka zaluka bansan komai game da shiba na sa ƙafa ta a ciki, bansan komai ba ban saniba! Ya ƙara sa yana kallon wayar kamar ita zai gani. Kawar da idanunta ta yi itama daga kallon wayar tana jin cewar sonda take masa yafi wannan abun da ya lissafo kawai dai shi ya fito da nasa filine.

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMWhere stories live. Discover now