*ADM*
*S REZA...✍️*
*First Class writer's asso...*
*PAGE4️⃣8️⃣*
........ Lokacin da suka isa gidan suka tarar da Usha da Mahaifinsa tsaye a harabar gidan cikin shigar wasu sabbin jallabiyoyi farare haɗe da hulunansu. Wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Muhammad ya sake miƙa gidiyarsa ga Allah buwayi gagara misali mai aiwatar da komai cikin hikimarsa. Yana isa gurin ya ce "Salamu'alaikum? Ya faɗa yana sakin fara'a da murmushi duk a lokaci ɗaya! "Wa'alaikum salam warahamatulla wabarakatuhu". Bayan sun gama gaisawane mahaifin Usha wanda ya samu sabon sunan Musulunci Abubakar Sadiq ya ce "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda ya haɗamu da mutumin kirki irinka! Tabbas lokacin da Sadiya ta bani labarin ku da kuma abinda ya faru da kai sai naji gaba ɗaya halaiyarka sun bani sha'awa, shine ta ce min wai ai haka halaiyar duk wani musulmin kwarai take mutuƙar zaiyi koyi da ɗabi'un ma aiki Sallallahu alaihi Wasallama. To ina jin haka sai na je gurin wani malami na masa bayani akan ina son shiga musulunci. Muhammad kam farinciki kamar yayi tsalle.Daga haka suka shiga cikin gidan yana son yin tozali da yayan nasa. Zaune yake ya miƙe ƙafafunsa daga shi sai gajeran wando da senglet fara kansa babu hula ya kafe guri ɗaya da kallo kamar mai tuto wasu abubuwan. Da sauri Muhammd ya ƙarasa kusa dashi yana kiran sunan sa. "Yaya Daniel? Yaya! Yaya!!! Ganin ya kasa juyawa ya kallesane yasa Abukar cewa "Bazai iya maganaba muma munyi dashi amma daga kallon guri ɗaya sai zubar da hawaye. A lokacin ne Muhammad ya kai kallonsa ga ƙafafunsa sai yaga ɗaya ta kumfura sosai ɗayar kuma ta shanye, ya kalli hannayansa suma haka suke, ga kansa da yayi ƙato wuya kuma ya sirance. Cikin damuwa Muhammd ya ce "Mai ya faru dashi haka? Ban gane ba ina Eliza? Yana rufe baki sai gata tafito riƙe da cufi a hannu tana juya abunda ke cikin kofin da cokali.
Da sauri ya karaso gurin da take ya ce "Mai ya faru da yayanna? Eliza ta fashe da kuka itama kanta a birkice take, kamar ba itace wannan ma'abociyar kwalliyarnanba. Cikin kuka ta ce "Mutanan Ƙauyan ku ne( wato mutanan KATUNGU) Sune sukazo har gida suka ɗauki wandonsa guda ɗaya, suka ciri gashin kansa shima ziri ɗaya, to tun daga ranar ya fara rashin lafiya duk inda zamuje sai a ce bazza a iya karya a sirin ba, wai a she ƴan uwanan wannan mutanan da ya rufeku tarene suka masa a siri. Muhammad ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!. "Faɗamin abunda ya faru tun rabuwarku da mu?
Elixa ta fara cewa "Ya kai wata uku a ƙulle batare da kowa yabi ta kansa ba, bayan zuwan Captain ɗinsu sai ya naimi zama dashi, bayan an karanto laifukansa wanda ya yi a lokacin da ya samu ƙarin girma. Hatta ƙananan sujojin da suke ƙarƙashin sa suma kuka sukeyi dashi. Sannan bayan ku da ya ƙulle a she ya sa an kashe wasu da yawa musulmai sojoji idan an kawosu aiki ƙarƙashin sa, babban amininsa wanda suke aikata aikin tare shine ya sanar da cewar ya kashe a ƙalla sojoji kusan takwas ba tare da laifin komai ba kawai dan sun kasance Musulmai. Da farko ya fara yin musu amma ganin hujjojin da aminin nasa ya kawone yasa ya yarda. Ana cikin wannan sai a ka sake sakowa batun ku a kan ya kulkeku har sama da shekaru a shirin,kuma daga ƙarshe ya rufeku a ciki ya saka muku wuta. To bayan tabbatar da laifinne kuma a take a ka cere musu kayan jikinsu a ka fara hukuntasu da hukunci irin nasu na sojoji. Bayan kwana bakwai a ka fara bin komai da ya mallaka na gidan soja a ka kwace, sannan gidan da yasakawa wuta shima a kace sai an biya domin ba nasa bane. Sannan bayan an gama biya kuma za'a harbesu a cikin barikin sojojin dake cikin gari. Wannan shine hukuncin da za'a masa.
Bayan haka suka bamu wata biyu a kan mu biya tarar da a ka cimu, kuma kuɗaɗene masu yawa wanda gaba ɗaya nidashi bamuda koda rabunsu. Daga nan muka wuce gidan Abbana tare da sojoji guda biyu wanda duk inda zamuje suna tare damu har wata ukunnan su cika. A nan muka tattara komai da mukamsllaka amma ko rabin abunda a keso bai kaiba. Mun shiga tashin hankali sosai , muka naimi auro a gurin babanna amma yace baida shi, daga ƙarshe ya ce ko dai Daniyel ya bar masa gida kokuma mu tafi tare. A haka muka cinye wata guda babu komai sai wahala.
VOUS LISEZ
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
ActionThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3