Chptar 44

8 3 0
                                    

*ADM*


            *S REZA...✍️*

*First Class writer's asso...*

           *PAGE4️⃣4️⃣*
........Misalin ƙarfe tara na safiya suka isa gidan Shek Kabir kabuga, kana ganin Shek kasan yana cikin farinciki da zuwan wannan baƙon nasa. Kafin Hajiya Babba ta tafi saida tasa a ka kira yayan mahaifinta Malam Adamu. Tarɓa ta mutunci Muhammad da iyalansa suka samu daga gurin iyalan Shek. Sosai Shek da Muhammad suke cikin farincikin ganin junansu, kana ganin kabuga kasan a kwai magan-ganun a bakinsa. Itama dai Momy tana nunu nata farincikin daidai yanda zata iya. Bayan an kawo musu abubuwan da a ka tana dar domin sune kowa yaci abunda zai iya ci kafi a ka sake sabuwar gaisuwa tsakanin su. A taƙaice Muhammad ya basu labarin abunda ya faru da su tsawon wannan lokacin, kuma ya tabbatar musu da cewar ɗan uwansa ne ya masa. Da mamaki Momy taga Shek na kuka yana tausayawa Muhammad, shima kansa Muhammad ɗin yayi mamaki. Bayan ya gama ne ya fara masa nasihohi a kan wannan jarabtar da ta sameshi. Sosai Muhammad da su Samuel suka ƙara yarda da Addinin musulunci, yanda sukaji irin alkairin da Allah ya tanadar ga masu yafiya idan an cucesu, sosai son Addinin Musulunci ya ƙara shigarsu har suna ji cewar zasu iya komai cikin koyarwar Addinin Musuluncin.

Shek ya kalli Salis ya ce "Kardai ka ce min wannan shine mai sunan Alhaji har ya gyrma haka? Muhammad yayi murmushi ya ce "Eh fa shine har ya zama saurayi. Ya faɗa yana dariya dukkansu. Hajiya Babba ma saida abun ya bata dariya, itama Momy dariya tayi tana kallon Salis ɗin da ke sunne kai. Ganin shek na ta kallon su Sarah ne yasa Muhamd gyra zama ya ce....

"Wannan shine babban ɗana. Ya faɗa yana nuna Salis. Sai ya ƙara nuna laɗifa ya ce "Wannan itace auta Ladifato. Sai ya dawo da kallonsa izuwa gurin Samuel ya ce "Wannan kuma shine ɗan gidan yayan nawa, shine babba sai ƙanwarsa gata nan ya faɗa yana nuna Sarah. Sannan ya ɗora da cewa..."Sannan sune suka buƙaci shiga Addinin Musulunci da kansu. Momy da shek da su Maryam da sauran suka amsa da AllahuAkbar! Fuskokinsu cike da annuri jin cewar ADDININMU zai samu ƙarawa. Momy ta ce da Maryam ta je ɗaki ta taso Abdalha. Tayi maganar ne batare da kowa yajitaba. Maryam ta sanar mata da cewar ai tun jiya da sukawo daga asbiti bai fito wajeba, ya ce kar kowa ya dameshi, sannan Dr Musa ya ce a barshi ya samu barci sosai. Badan Momy tasoba ta bar maganar amma hankalinta naga ɗanta.

Shima shek ya gabatar da yaransa ga resu. Cikin tsokana Muhammad ya ce "To a cikin su ukun suwaye a maran da za'a aurar? Shek ya nuna Sadiya da Nusaiba. Duk da hakan dai ya ce "Banga magajin Malam ba? Abokin Salis... domin bana mantawa da tsiran sati ɗayane tsakanin su? Da sauri Hajiya Babba ta ce "Ai nasa yanzu ya zama magidanci? Da sauri Momy ta ce "Allah sarki ai bashi da lafiya yanzu haka ma yana ɗakinsa a kwace baisan halin da ya ke cikiba. Salis ya ce "Allah sarki ai ina jin sunansa amma bamu taɓa haduwaba, shine Abdllah Kabir kabuga ko? Yayi maganar ne bayan ganin hoton Abdalha da mahaifin nasa a palon.  Maryam ta amsa da eh shine.

Daga haka suka ranƙaya ɗakin da Abdalha ɗin ya ke. Sosai suka tausaya masa ganin yanda ya rame ya fita a haiyacinsa. Muhammad ya tambayi mai ke damunsa,? Mai yasa ba'a kai shi asibitiba? Shi kansa shek sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewar ciwon ɗan nasa na gaskene ba yanda yake tunaniba. "Ciwon nasa bana asbiti  bane na gidane! Cewar Momy cikin wata iriyar murya. Hajiya Babba da Muhammad har haɗa baki sukeyi na tambayar kamar ya? Ganin haka yasa Shek barin ɗakin yana jin wani irin abu na masa ciwo game da ciwon Abdalh ɗin.  Take Momy ta kwashe komai ta sanar musu da komai, tun farkon gabar dake tsakanin yaran har ta dawo soyayya. Salis yayi mamaki sosai jin cewar a kan soyayya Abdalh ya koma haka. Da sauri Muhammad ya fita izuwa gurin Shek. Hajiya Babba da Momy ma suka bi bayan sa. Bayan fitarsu Momy suma ƴan matan suka fita. Salis da Samuel kuma suka zauna a ɗakin suna jiran ya farka. Ai kuwa basu wani daɗe a ɗakinba ya tashi. Yana tashi zaune ya fara bin Salis da Samuel da ido. Salis ne ya matso kusa dashi ya ce "Shek Abdalha Kabir kabuga Sarkin soyayya? Ya faɗa da a lamar tsokana?

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMWo Geschichten leben. Entdecke jetzt