Chapter 24Tabbas solomon yasan wannan abubuwan da Uncle ya lissafo duk cikin al'adarsune, tabbas yasan wannan duk al'ada ce ba addininsu bane, amma shi bai taɓa tunanin cewar abun zai zagayo ta kansa ba! Kallon kawun nasu yayi cikin muryar kuka ya ce "Banida kuɗi banida komai bansan ya zanyi ba, yana kuka yana riƙe da hannun Titi wacce itama kukan takeyi. (duk wannan maganar cikin yaransu yakeyi wato yaren tibi) Kafin kowa ya sake magana sai sukaji anshigo gida cikin ihuu ana kuka haɗi da ƙara. Suna juyawa sukayi ido biyu da Daniyel wandake rusar kuka ko ganin gabansa bayayi. Da sauri Titi ta 'karaso gurinsa ta rike 'kafarsa tana kuka tana cewa "Yaya Daniel mama ta mutu please and please ka ce mata karta tafi ta barni!?". Cikin kuka shima Daniel ya kamota tsam ajikinsa yana rarrashinta, shima Solomon sai kawai ya fad'a jikinsu yana kuku abun tausayi. Suna cikin haka kawun su ya sake cewar "Kunsan fa tin cikin dare ta mutu saboda haka dolene ayi wannan allurar domin karta fara wari agari, kuma kar ta san'kare. Daniyel da baisan zancen me a keba ya kalli uncle din nasu ya ce "Kawu meya faru?
Tsaf uncle din nasu yasanar masa da duk abunda ake bu'kata kamar yanda ya sanarwa da Solomon. Cike da rauni Daniel ya ce "Uncl a samo mai siyan gonar mu sai kawai a siyar masa kaga ai sai musamu na kaita mutuware? Da sauri Solomon ya d'ago kai ya kalli yayan nasa cikin mamaki amma bai ce komai. Tabbas kam indai har ba gonar zasu siyarba to basu da wannan kuɗin da zasu iya biya, to amma gonar fa guda biyuce kawai, ɗayama daga ciki ta Solomon d'in ce da ya siya da kansa tunda sad'ewa.
Haka kuwa akayi suka samo wanda zaisiya, akayi cinikin gonar amma Solo ya ce banda kayan ciki wato doyarsa, domin kuwa doyar ta nuna harma an fara cira ana ci.
Bayan ansiyar ne solo ya samu yayansa ya ce "Yaya ina kuɗin shagon da aka siyar kace zamu kai ma..."kafin ya 'karasa ya ce "Ninasan dama baku damu daniba, wato na ɓata amma kai damuwar ka kud'iko? To 'barayine suka bini abaya, Ina tunanin sunga lokacin da kabani kuɗinne shine suka bini, amma dai basumin komaiba kud'in kawai suka 'kar'ba. Solo ya ce "kayi ha'kuri Allah ya kiyaye gaba ai ban sani bane. Ya amsa da amin sannan ya ce "yanzu zanje na nemo mai motar da zai d'aukemu zuwa cikin gari, idan yaso acen ɗin sai ayi mata allurar. Yana fad'a ya bar gurin yayinda solo ya bishi da kallo.
Sai wajan karfe sha biyu na rana kafin Daniel ya dawo da wani mai moto har cikin garin nasu. Wanda har mutane sun fara magana, ƴan gari sun fara surutu, dan gin ubansu kuma babu wanda ya taimaka da komai. Aikuwa solo da Daniel ne kad'ai suka d'auketa domin kuwa harta fara wari kasan cewar ba'a yi wannan allurar ba. Haka dai a ka kaita mutuware, wanda suma da ƙyar suka yarda suka 'kar'beta akan wai basu kawota da wuriba harta fara wari.
Kaman yanda kawunsu ya ce musu duk kwana 'daya dubu uku ne to tabbas hakane. Anan fa hankalin Daniel da solo ya tashi, sukace badamuwa zasu biya.
Bayan sun koma gidane, a ranar Daniel ya ce zai tafi gurin aikinsu domin a wannan lokacin har sun fara zuwa zana jarabawar neman aiki. Ya ce "zanje bayan kwana goma zai dawo sannan kuma zai dawo da kud'in da zasu 'kar'bo mamar tasu. Batare da sunce komaiba suka masa fatan dawowa lfy. Kafin ya fitane Titi ta ce "Yaya kafin mama ta mutu ta bamu sa'ko mu sanar maka? Ya ce "Ina jinku? AI kuwa nan suka kwashe komai suka sanar masa irin wasiyyar da ta basu. Nan shima ya 'kara musu nashi fa'dan akan addininnasu domin kuwa duk cikinsu yafi su kishin addinin nasu.
Yau kwanan Daniel goma sha huɗu bai dawo ba. Ganin haka yasa solo sayarda d'aya gonar yaje ya biya kud'in mutuwaren sannan yazo gida da mamar tasu.anan fa kamar dama jiran beriyan sukeyi, kasancewar dama gashi ƙauyen ƙaramine yasa duk wani abu da a keyi a ƙauyen sai kowa yasani. Da 'kyar yayi sa'a ya yanka musu kaji suma guda uku sai kuma kayan shaye-shaye. Aikuwa nan aka fara zage-zage da 'korafe-'korafe. Haka dai ya toshe kunnuwansa daga jin kowani irin zagi daga cikin la'umman garin.
Kasan cewar an ɗan sayi gonar da daraja yasa tun kafin yayi komai saida ya ware kuɗin akwatin da ake siya kafin ya ɗan ware wanda za'ayi sauran hididdimun. Cikin yardar Allah akayi beriyar mamarsu batare da ɗan uwansaba. Kamar yanda aladarsu take wajan bikin anayin kwana uku anayi, wasu huɗu wasu biyar kai wasuma har sati guda.
![](https://img.wattpad.com/cover/323716862-288-k147137.jpg)
ESTÁS LEYENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AcciónThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3