Chapter 28
Dr Musa ya meƙe tsaye da ga kujerar da ya ke zaune ya ce "Jiya muna kallo nida Madam naga wannan sanarwar shine abun ya bani mamaki kuma na ce sai na tambaye ku domin kaina ya ƙulle walahi, shin da gaske ne kai ne ka sace ta?" Ya ƙara sa maganar ya na kallon cikin idon Abdalh wanda shi kuma ya ke kallon Ziyada wacce har idonta ya cika da ruwan hawaye. Cikin kuka da ya kuffce ma ta ta ce "Ba shi ba ne ya sa ceni, ha salima saboda shi a ka sake ni, amma ni ban san dalilinsa na yin hakan ba" "Babu wani dalilina kawai nayi ne domin Allah da kuma wanke kaina a idon duniya domin kowa yana tunanin ni ne na sace ki. Dr Musa ya ce "Shek kabuga ni fa ban gane me kuke ce wa ba fa, dan Allah kusanar min da komai, amma to idan ba kai ba ne to su wa ye? Nan ta ke Abdalh ya kwashe komai ya sanar wa da Dr Musa, sannan ya ɗora da abunda ya faru lokacin da ya je gidan su yarinyar da mahaifinsa ya tura sa domin su ga juna. Da sauri Dr Musa da Ziyada suka kalleshi jin abun da ya ce. "To su yaran da su ka sace ta me ta musu?" Cewar Dr Musa cikin mamakin lamarin?
"Wai sabo da waƙar da ta yi ta buɗaɗdiyar wasiƙa. "To suɗin ƴan gidan uban waye da har zasu mata wannan jan aikin, Kai kuma ka barsu suka tafi baka sa police sun ka ma suba?"
Cikin kukan da ya fara fin ƙarfin ta ta ce "Dan Allah inaso na tafi gida ni ɗaya, domin nasan me zan ce wa Malam ya fahimce ni, kuma kaima zaka fita da ga zargin da al'umma su ke ma ka, amma dai ni ka ɗai zan je gida kuma yanzu. Ta ƙara sa ta na fashewa da wa ni sabon kukan. Abdalha ya ce "No tare zamu tafi domin nasan abun da zanyi ko mai ya yi daidai kamar yanda na ce a baya. Ziyada dai bata yarda ba har sai da Dr Musa yasa baki kafin ta yarda zasu tafi da Abdalha amma sai da daddare domin gudun idon mutane. Haka suka yanke akan zasu tafi ɗin.
Ɓangaran gidan su Abdalha ku wa kaman yanda ya amsa musu cewar shine ya sa ce Ziyada haka ko wa ya hau ya zauna daram, harda Momy wacce izuwa yanzu basu gama shirya wa da mai gidan nata ba tun abun da ya faru a kan Abdalh wancan lokacin. Suna zaune kamar yanda suka saba duk bayan sallar magariba ranar juma'a domin gabatar da karatun littatafan addini da Momy ke ƙara koya musu a duk yan macin ranar. Cikin sauri har yana ƙoƙarin zame wa ya shigo gidan cikin tsan-tsar ɓacin ran abun da ke tafe da shi ɗin, tin kafin ya ƙara so ya fara ce wa "Ina kike ke mai ɗaure wa wannan yaron, Yanzu me hakan ya haifar wannan wani irin abun kunya wannan yaron ya ɗauko mana, yanzu a ke sanar min da cewar wai Abdalh ya je gidan shek gurin yarinyar da na turashi wai yarinyar ta ce bazata auresa ba, saboda abun da ya aikata. Yanzu kuma gashi wai wannan malamin ƙar yar ne wai ya kai Abdalh kotu akan sai ya fito masa da yarinya. Yanzu dan Allah wannan wani irin abun kunya yaronnan ya je ya kwaso min, a ce wai ni Kabir kabuga ne ɗana zai je neman aure wani gidan amma a faɗi aibunsa! Sannan ga batun waccen uban yarinyar da ya sace musu wai ya kai ƙara kotu" Ya ƙarasa maganar ya na mai nuna Momy kamar ita ce Abdalha ɗin.
Cikin tsan-tsar tashin hankali Momy ta ce "Kotu fa ka ce Malama?" Ta faɗa ta na miƙewa tsaye. Cikin mamaki Maryam ke kallon Daddy jin wai yarinyar ta ce bata son Abdalh ga kuma batun kotu. Ita dai ta san Nana ta na son Abdalh sosai, kuma tasan irin addu'ar da takeyi a kan ta samu Abdalha amma yanzu a ce wai yarinyar ta ce ba ta son sa, Kai saidai ko an zugata kokuma dai a kwai wani abun a ƙasa bayan haka. Ta na cikin tunani ta ji Daddy na faɗin. "Ni dai Walhi ba zan je kotu na tsaya ni da wannan banzan dattijon ba, bansan komai ba sabo da haka shi da ya je ya taro abun sa shi ne zai jagoranci kayarsa, ha ka kawai yaro lokaci ɗaya ya zo ya zama wani iri, to wallhi zan mutuƙar saɓa masa in dai a kan ƴan bidi'ar nanne, bana sonsu bana ƙaunar ganinsu bare wai har na je na haɗu dasu a kan na sace musu yarinya, To idan na je na ce musu me? Na ce musu dan Allah suyi haƙuri?" Ha ka dai Daddy ya dinga sarfa masifa ta idan ya shiga ba ta nan ya ke fitaba, ƙarshe dai ya ƙare da kiran Abdalh amma no amsar, hakanne ya sa ransa ƙara ɓaci, domin yaso Abdalh ya zo ya sanar da shi gidan uban wa ya kai musu yarin ya domin shi dai Daddy bai yarda cewar ya sace ta ba, kawai ya masa haka ne domin ransa ya ɓaci. Ɓacin ran Daddy yau kam ya ɓaci, nan Momy ta ke sanar masa da cewar yau gaba ɗaya Abdullah bai zo gida ba.
![](https://img.wattpad.com/cover/323716862-288-k147137.jpg)
YOU ARE READING
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
ActionThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3