Chptar 45

9 1 0
                                    

Chapter 45

Hakan da Ziyada ta yi ne ya ƙara tabbatar musu da cewar tanada wanda takeso. Cikin hukuncin Allah komai ya tafi daidai da yanda Allah yaso ya kasance. Malam Adamu da kansa ya zaunar da Aliyu ya tsara masa komai yanda zai fahimcesa, ya tabbatar masa da cewar ya yi haƙuri domin ba zaiwa ƴarsa auran dole ba, da farkoma rashin fahimta ne yasa yaso ys aikata kuskure. Da mamaki yaga Aliyu na murmushi Malam ya tambayeshi dalili. Ya ce "Ai tun ba yauba na gano Ziyada tana son Abdalha, kuma nasan da cewar  auran biyayya zatayi...koda hakan  bai faruba to babu shekka ni da kaina inada niyar samunka muyi magana a kai...sai dai ina tsoron abunda zai biyo baya domin nasa ba kwajituwa da yaron da takeso din, sannan kuma Abdalh da kansa ya turo Isa a kan ya roƙeni na janye batun Aurena da Ziyada kuma na yarda Allah ya basu zaman lafiya sannan nima naji naɗin wannan haɗin kan naku. Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulmai baki ɗaya, Allah ya ƙarya duk wani abun da zai tarwatsa kan al'ummar musulmai. Malam Adamu ya kamo Aliyu yana hamdala yana amsawa da Amin amin. Haka Malam ya ce duk yarinyar da yaga ta masa a cikin dangi to yaje ya naimi soyayyarta shi kuma zai masa komai na aure. Aliyu yayi murna sosai a haka ya bar gidan yana jin son Ziyada amma zai daurewa zuciyarsa kamar yanda ya ce.

Kwana biyu da faruwar haka soyayya ta ɓarƙe tsakanin Ziyada da Abdalha, duk wata kafar sadarwa labarinne ke kai wa da komowa, al'ummar gari kowa mamakin wannan abun ya keyi, ai jama'a basu ƙara shiga mamaki ba saida sukaji soyayyar Maryam da Isa, nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa. Masu cewa dama ai tun farko rashin fahimta ce tasa kowa baya ganin kowa da ƙima. Wasu kuma suce ai dama ai Malamai sune masu jefa al'umma a cikin ruɗani domin sunsan gaskiya sai su taketa domin son zuciyarsu. Wasu kuma sai suyi addu'ar Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulmai mu zama addini kuda ɗaya, koda ma nawane to a zauna lafiya babu cinmutuncin juna da wulaƙanta jna da aibata juna.

Ranar juma'a a ka ɗaura auran Sadiya da angonta. Sai Nusaiba itama da nata angon. Sannan a ranar ne Sara da Samuel suka karɓi kalmar shahada. Kowa ya zaɓi sunan da yakeso. Samuel ya koma Ibrahim Sara kuma ta ce tana son sunan da taji Momynta tana kiran Hajiya Babba dashi wato Fatima. Manyan Malamaine suka halarci taron hakanne yasa Fatima da Ibarahim suka samu kyaututtukan bam'mamaki. Tabbas sunga yanda a ke karamci sannan sunsha wa'azi mai ratsa zuciya, har saida suka zubar da hawaye. A wannan lokacin ne kuma Fatima ta fara tinanin iyayenta tabbas tayi kewarsu tana son ganinsu.

Soyyaya ce mai tsafta da birgewa irin ta malamai Abdalh da Ziyada sukeyi. Shima Isa ba'a barshi a baya ba domin soyewa sukeyi da Maryam sosai. Duk inda kaga Abdalha to suna tare su huɗu. Salis Abdalh Ibrahim Isa. Suma  haka matan Laɗifa da Fatima da Maryam haka zasu tafi gurin Ziyada a zauna a ta hira, a nanne Maryam ta ke sanar wa Fatima cewar ai duk wata Fatima to zara sunanta to kawai yanzu sai a koma cemata Zara, kunga an cire S na Sara an sa Z na Zara. Cikin farinciki Ziyada ta tabbatar mu da hakane, ai kuwa a ka koma cemata Zara. Tabbas Zara da Ibrahim sun tabbatar da cewar suna tare da malamai, domin a ɗan kwana goma sha huɗun da sukayi sun san abubuwa sosai. Ibrahim kam ɗan gata ya zama domin kuwa dukkansu ukun ne suke ƙara masa a bubuwa game da addini. Abdalha ya dage da koya masa karatu cikin muryarsa mai tashin daɗi, wani lokacin idan Abdalh na zubawa Ibarahim karatu sai ya ta kallonsa yana jin Allah yasa shima ya iya karatun Alqur'ani maigirma kamar haka. Isa ma haka yake koya masa wasu littattafai na addini Salis ma ba'a barshi a baya ba. Itama Zara haka Maryam wacce dama ita duk cikin yaran shek Kabir babu kamar ta a mata indai ɓangaren karatun ne, haka take rerewa Zara karatu sosai. Haka Malam  Ziyada zasu kwashe lokaci suna koya mata karatu ga Mama ga Momy dukkansu suna koya mata, domin suɗin sunzama wasu taurari a cikin al'umma. Shek Kabir kabuga da Malam Adamu kam komai ya wuce, yanzu lokacin auran yaran nasu kawai suke jira. Mama da Momy da Hajiya Babba suma sun zama ƙawaye sosai suke zama su sha hira. A nanne Hajiya Babba take sanar musu da abunda ya faru da ita na auran AJ da tayi.

Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADMWhere stories live. Discover now