🤷♂️ *ADDININMU* 🤷
( *BY S REZA*... ✍️)
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...**KAFAƊI ALKAIRI KO KAYI...! SHIRU🤫S REZA DAI BAI MA SAN KUNA YI BA.*
*ADDININMU*
*PAGE* 👉9️⃣.........Cikin sauri Daddy ya zauna a bakin gadon yana amsa waya. Cikin minti kaɗan ya shirya cikin kayansa na sojoji, baiko tsaya ya kalli abun da ke faruwa a ɗakin nasaba, haka ya fita yana mai gyara rigar sa haɗi da kiran Mommy da ƙarfi! "A'lexa! "A'liza! "Da sauri Mommy tazo haɗi da cewa "Lafiya kuwa? Cikin sauri Daddy ya jefa mata kyin ɗakin haɗi da cewa ta rufe masa ɗaki zasuje Abuja yanzu sun samu kiran gaggawa sai gobe zasu dawo...sannan ya ce idan Samuel ya dawo ta ce ya kirashi. Haka Mommy ta masa fatan dawowa lfy haɗi da kissin ɗinsa sannan ya fita har yana haɗawa da gudu. Mommy kuwa komawa ɗaki tayi batare da rufe ɗakinba.
Duk abun da Daddy ke faɗa yana sauraro amma tsabar tsoro ya hana ya fahimci komai, yana cikin hakane yaji alamar zai fita, ai kuwa yazo jikin ƙofar toilet ɗin yana leƙawa har yaga fitar Daddy ɗin, sannan ya sauke a jiyar zuciya yayi hanyar fita. SARAH kuwa lokacin da ihu ya kufce mata haɗi da fitsari sai tayi saurin rufe bakinta, amma fitsarin kuwa saida ya kufce. A kan idonta Samuel ya fito daga toilet har ya bar ɗakin kafin itama ta fito cikin tsoro ta nufi ɗakinta. Tana shiga ɗaki ta faɗa toilet tayi wanka kafin ta fito tana cewa "Walhi daga yau bazan sake satarwa Daddy kuɗiba irin wannan tashin hankali da nake shiga! Haka ta ƙirga kuɗin dubu arba'in da uku (43,000) sannan ta shiga neman kayan da zata saka.
*LAƊIFA. SALIS POV*
Tana shiga palorn ta tararr da Hajiya Babba sai sakin murmushi takeyi, harda wani lissafi da hannu. Tin daga ƙofar palorn take kiran Hajiya Babba Hajiya. "Wai Hajiya wani irin aiki kika baiwa wannan wawan yaronne!? Allah Hajiya na tsani yaron Please dan Allah a koreshi akawo wani. Cikin mama Hajiya ta ce "Wai wani yaro kike magana a kaine kinzo tin daga waje kina kirana kamar namiki laifi?
Cikin tsananin jin haushin AJ Laɗifa ta ce "Hajiya wannan yaron dayafita daga gidannan mana dashi nakeyi Please wani aiki kika bashi? Kafin Hajiya tayi magana saiga Salis ya shigo yana ƙoƙarin zama laɗifa ta ce "Bro please dan Allah ka fita a harkar yaronnan, kaga abunda yamin yanzu kuwa!? Zaginafa yayi harda cewa wai wai yafi ƙarfin yayi dani! Yana ɗan aiki to Walhi sai ya bar gidannan tinda ba gidan ubansa bane. Cikin kwantar da murya Salis ya ce "Haba my sister meye na ɗaukar zafi haka, Allah yaron baida wata damuwa kece dai kike son saka abun a ranki amma karki damu A.J mutumin kirkine.
Cikin fushi Hajiya ta ce "To naji zan koreshi tundade kince bakya sonsa, amma bari kiji na faɗa miki... wallhi nima zanyi aure ko kunaso ko bakwaso, tinda na fahimci saboda ina goyan bayankune shine kuke son Sai kun kasheni da raina ko!? To na gode.
Cikin mamaki Salis da Laɗifa suke kallon Hajiya domin jin abun da take faɗa. Cikin ƙarfin hali Salis ya ce "To yanzu Hajiya ina ruwan auranki da aikin AJ? Sannan ma meyakawo zancen zakiyi aure bayan muna magana a kan ɗan aikine? Sai a lokacin Hajiya Babba ta fahimci katoɓararr da takusa ta tafka. Ai kuwa cikin sauri da rikicewa ta gyara maganar ta da cewa "To ai nasan halinkune yanzu ina faɗa muku aikin da na ɗauke shi sai kuce ku bai mukuba kumani haka nakeso.
Da sauri suka haɗa baki da cewa "Faɗa mana mun yarda? Hajiya Babba cikin farin ciki ta ce "Zai dinga tuƙani duk lokacin da naso haka. Sannan zan dinga aikansa cefane dade sauransu, shikenan fa aikin, ma'ana dai yaron gidana. Da sauri Salis ya ce "To yanzu Hajiya a kan wannan shine kike cewa wai zamuce bamaso?...ai gaskiya ma Walhi daɗima naji kinga shima yaron yanzu sai ya ɗanji daɗi ,Allah ma dai yasa ya iya mota? Hajiya Babba ta ce in bai iyaba za'a koya masa. Ita dai laɗifa bataso AJ yasamu aiki a gidan nasu indai ba aikin gadi bane, amma ya zatayi haka zata haƙura, amma tayi alƙawarin shida kansa zaibar gidan saboda cin mutuncin da zata dinga masa. ( *NI KO S REZA NA CE UMM-UMM FA🤓)* Ta ce "Bro muje nazo da labari? Salis ya ce to muje ɗakina. Haka suka tafi suka bar Hajiya Babba cikin murna ganinn ta shawo kan yaran nata cikin sauƙi.
VOCÊ ESTÁ LENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AçãoThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3