Chapter 31
Da gudu ta bar gidan bata tsaya sauraron kiran da Kadija ke mata ba har tana cin karo da mamar Kadijan zata shigo ɗakin bata ko bi ta kan ta ba ta kwasa da gudu sai gida. Ta na shiga gida ta tarar da Innah a gurin da ta barta, da sauri ta faɗa jikin innar ta na kuka ta na toshe bakinta. Cikin tsorata da halinda Nana ta shigo gidan Innah ta ce "Nana me ke faruwa? Waye ya taɓaki? Me a ka miki? Cikin kuka Nana ta ce "Innah wallhi walhi yaya ya dawo kuma kuma kuma! Sai ta kasa ƙarasawa ta sake fashewa da wani kukan. Cikin jin haushen abubda take cewa Innah ta ce "Saboda ya dawo shine kika shigo min gida da kuka kamar wacce a ka daka? To saime idan ya dawo, ai dama ni nasan babu inda yaje yana cikin garinnan, kuma in sha Allah sai Allah ya saka mana akan abinda ya sa aka ai kata mana. Cikin rashin sanin abunyi Nana ke kuka tana tsoran sanar wa da Innah abunda taji kuma kar taje abun ya ɓata mata rai! Sai kawai ta ce "Wannan sojan ne ya zo ya kamashi, wai saboda ya dawone yasa aka sakemu. Innah ta ce "To wai dan ƙundun ubansa me ya ha ɗashi da arne? Ina ruwansa da marasa sallah da har zaije ya jawo mana irrin wannan azabar? Nana ta ce "Yanzu dai Innah zanje nemansa Kadija ta ce min tasan unguwarsu harma gidan sojan, saboda haka zamuje tare kinji? "To walhi idan kikasa ƙafa kika bar gidannan da niyar zuwa neman Abduljabaru to ina tabbatar miki cewar bazaki dawo ki sameni a gidannan ba, zan tattara kayana na barmuku gida na shiga duniya ƙila a cikin duniyar na samu waɗanda zasu iya zama dani, dama ai nasan ba gidana bane gidan ubanku ne saboda hk zan bar muku gidan. Da sauri Nana ta rugomo Innah ta na kuka tana bata haƙuri a kan cewar ta fasa zuwa, "Pls Innah ki daina irin wannan zancen bai da ceba samm! Cewar Nana ta na kuka. Innah ta tashi ta bar gurin izuwa ɗakinta tana tunano ma haifin su Nana ɗin. Ganin haka yasa itama Nana bin bayanta ta na kuka, ai kuwa ta na shiga sai ga kiran Dr. Tana ɗagawa ya ce "Ina wa je! Nana ta ce "Innah Dr ne yazo wai yana wa je? Innah ta ce "Tashi kije amma karki daɗe, kuma ban yarda da zuwa ko ina ba. Dr kuwa yau dai ya zo da ƙarfin sa domin baiyana abunda ke cikin zuciyarsa a gurin hasken rayuwarsa.
*******
GIDAN SOJAAddu'a suka duƙufa yi dukkansu domin Allah ya kuɓutar dasu daga hannun wannan ƙaton arnan, kowa ya manta da komai sai addu'a, wasu kuma suna karatun qur'ani. Muhammad da sauran ƴan uwan nasa wanda suma kaɗan daga cikin ƴan cikin ƙauyan Katungu ne da suka musulunta shine fa Daniyel ɗin ya haɗa dasu, sannan yaje ƙauyan ya sanar wa da iyayensu cewar ai dama idan mutum ya ƙarɓi musulimci kuɗi a ke yi da shi, saboda haka Solo yaje yayi kuɗi da yaransu. Hakanne yasa suka ƙara ƙiyayyar Addinin Musulunci, wanda har wasu da ɗan dama sun fara nuna buƙatarsu ta shiga addinin saboda yawan zuwan da Muhammad ɗin keyi cikin ƙauyan Katungun, amma yanzu duk sun ƙara jin sun tsani addinin da ma mutanan cikin ta. Hakanne yasa suka fara kashe duk wani ko wata Musulmi da ya shiga yankin nasu. Yanzu dai cikin ƙauyan Katungu babu dama wani musulmi ya shiga.
Muhammad, Umar, Usman, Salis, Hajiya Babba, Laɗifa, AJ. Sune a cikin ɗakin rai bakwai(7) kuma dukkansu musulmai. Kowa ƙoƙarin karanto duk addu'ar da tazo bakinsa ya keyi, banda Laɗifa wacce tun da ta shiga jikin mahaifin ta take ta kuka har yanzu, Hajiya Babba ma kam izuwa yanzu ta saddaƙar domin bata manta abunda ya ce mata ba, ga kuma ƙarar tashin motocin su da sukaji alamar sun tafi.
Gudu sukeyi sosai wanda yasa suka isa cikin garin Boko da wuri, dubada yanda jiniyar motocin nasu ke tashi a dukkan hanyar da suka biyo, kowani mai abun hawa ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Abun da ya ɗaure wa kowa kai ku wa shine...suna shigowa unguwar da yake ɗin suka ga al'umma a tsaye a bakin gidan, ga kuma hayaƙi da ke tashi. Koda suka ƙarasa sai sukayi gamo da abun mamaki. Gidan wani ɗan kasuwa ne ya kama da wuta hakan yasa ya laso na kusa dashi, shima ya kamo na kusa dashi, wanda kuma gidan Comandar Daniyel ne a tsakiyar su. Ko kafin ƴan agajin suzo har kowani gida ya gama cinye wa tass. Ganin sojoji yasa sauran al'ummar dake tsaye a gurin suna kallo kowa ya ɗau na kare. Cikin tashin hankali Elixa ta fara rusa ihu har ta manta da ita ɗin wacece, ihu ta kayi tana faɗin irin dukiyar da ta ajiye a cikin gidan, su kansu sojojin mamakin wannan abun sukeyi, domin ai ba wannan gidan bane ya kamata a ce ya ƙone. Shi kuwa Comandar tsabar ruɗewa bai san lokacin da ya tun kari wutar ba, duda cewar wutar ta gama cinye komai amma har yanzu tanada zafi.

ESTÁS LEYENDO
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AcciónThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3