Chapter 10
Tin da suka shiga motar yake tinanin mokomarsa idan an ɗaura wannan auran. Tafiya sukeyi suna ɗan taɓa hira jifa-jifa, Hajiya Babba kuwa ruƙon Allah ta keyi a zuciyarta a kan aurannan ya ɗauru kar a samu wata matsala ko ɗaya. Ita dai tasan abunda zatayi ba haramun bane, addini bai haramtaba, sannan ta wani ɓangaran ma sunna zasu aikata, to amma shin AJ yasan nufinta a kan wannan auran!. Awani ɗan ƙaramin gida suka tsaya, Hajiya Babba ta ce "Wannan shine gidan malamin da zai ɗaura mana auran, na sanar dashi komai kaide abun da nakeso shine...duk abun da zaice maka kace eh. AJ ya ce "Angama hajjaju makkatu. Bayan malamin ya gama yiwa AJ duk wata tambaya ne sanan ya ce su jira har lokacin sallar a'zahar tayi idan sun idar sai a ɗaura.
Haka kuwa a kayi bayan sallar azahar al'ummar da suka gabatar da salla a wannan lokacin suka sheda auran Abdul jabaru da amaryarsa Aisha Salisu (Wato Hajiya Babba) a kan sadaki dubu ɗari ɗaya. Shedu suka sheda waliyai suka amince al'umma suka ƙarɓi goran ɗaurin aure suka tabbatar.
Bayan an ɗaurane mlm ya kira AJ ya tambayeshi akan cewa shin da amin cewarsa a ka ɗaura wannan auran? AJ ya ce "Eh da yardasa kuma da amin cewarsa. Shidai malam yana ganin abun kamar ba mai yuwa bane domin kuwa yasan Hajiya Babba tin mijinta na raye. Haka suka shiga mota izuwa hotel domin a can zasu kwana kafin gobe subar ƙasar a yanda Hajiya Babba ta shirya kuma sai sunyi wata biyu kafin su dawo.
Bayan sun kama ɗakine Hajiya Babba ta ce masa bari taje ta dawo. Tana fita ta wuce gurin masu sayarda kazar amarci, ta sayo guda biyu sannan ta sayo musu lemo da ayaba da dai sauran abubuwan da zasu buƙata a daran. AJ kuwa Hajiya Babba na fita ya shiga toilet ya watsa ruwa yana cewa "Kai jama'a yanzu dai da gaske na zama maikuɗi! Tinda nake ban taɓa shiga ɗakin hotel bama amma wai yanzu gashi ni kaɗai zan kwana a kan wannan makeken gadon. Yana faɗa yayi tsalle ya faɗa a kan gadon yana mai sakin wata dariya irin ta wanda suka samu sauyin rayuwa kamar sa. Yana cikin wannan hali tinanin Sara ya faɗo masa. Ya ce "Allah sarki Sara bazan manta da keba, idan burina ya cika kece ta farko da zan fara mallakawa mota. Yana faɗa ya saki dariya yana kallon kansa ganin daga shi sai tahul ne yasa ya tuna da cewa ashefa baida kayan sawa. Tini ya mayar da na jikin sa kafin ya tada sallar magariba domin kuwa har wani gurin anyi. Kasan cewar sun daɗe a gidan malam. (Baisan cewar zaman da sukayi a gidan mlm Hajiya Babba ta shirya kanta bane🤓)
Hajiya Babba. Da sallama ta shigo ɗakin riƙeda ledodi a hannunta har guda huɗu. Kallonsa tayi ganin yanda yayi da fuskarsa alamar damuwa. Ta ce "AJ angon hajiya lfy kuwa?
AJ yace "Ina kika sakamin layin wayana?
Hajiya ta ce "Ai sai mun koma gida zan baka saboda kar a damemu muna cin amarci"
Cikin AJ yabada wani sauti gooo. Ya ce "Ina son nayi waya da Innah ta da ƙanwata?
"Ok kabari Saida safe. Kafin yayi magana ta ce "Ga kazar amarci na siyo mana kazo muci domin shima yana cikin dokokinmu. Kasancewar dama yunwa ya keji sai ya ce "Ikon Allah yanzu cin kazarma a cikin doka yake? Hajiya tayi dariya sannan ta buɗe musu kazar suka fara ci yana mata surutu ita kuwa Allah-allha take taga sungama ta samu kanta, domin yanda takejin idan bata yi komai yauba to abubuwa zasu lalace mata.
Bayan sungama Hajiya Babba ta ce "Tom Sai mutashi mu gabatar da Sallah ta godiya ga Allah ko? AJ ya ce "Ai lokacin sallar isha baiyiba. Ta ce "Tuni anyi sallah ai. Ya ce to bari naje nayi. Hajiya da ta gama gano shi sai kawai ta ce
"Ok tom yanzu dai ga kayan barci kaje kasaka nikuma zanyi sallar magariba da isha kafin ka fito.
AJ ya ce "No ai ni da wannan kayan zan kwanta karki damu haka nake kwana ko da malum-malum ne ban da matsala. Hajiya Babba ta ce "Shima yana cikin dokokinmu. Ai kuwa da sauri ya ƙarɓa yana faɗawa toilet domin sakawa.

CZYTASZ
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AkcjaThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3