Chapter 22
Yana zaune agurin yana kallonta har Dr Musu ya dawo. Kallonsa yayi cikin mamaki ya ce "Har kadawo? Dr ya a'msa da cewa "No na kira ne daga asbintin ne ankawo min. Bayan ya dawo palon gidanne ya zauna Dr ya kalleshi ya ce "Wai shin Abdalha mena keji yana faruwa da batun yarinyar da akace kaine kasaceta?" Tabbas Dr Musu ya gyrmi Abdalh nesa ba kusaba amma kasancewar shi Allah ya ɗaukakashi fiye da Dr Musu ɗin, sai suka zama tamkar abokai. Abdalha ya ɗago kai babu alamar fargaba ya ce "Itace wannan". Yafaɗa babu alamar wasa. Dr Musa ya zauna daƙwas cikin tsananin mamaki ya ce "Kana nufin kace Ziyada ce wannan? Abdalha bai bashi amsaba ya ce "Idan ta farka kasa madam ɗinka ta taimaka mata tayi wanka kuma abata abinci sanan ka kirani. Yana gama faɗa ya bar gidan batare da ya tsaya amsa tambayoyin da Dr kesan masaba. Dakallo Dr yabishi cikin sabon salon mamakin lamarin Abdalha. Afili ya ce "kenann shine ya saceta! Sanin babu mai bashi amsa ne yasa ya koma ɗakin da Ziyada ɗin ke ciki da sauri har yana cin karo da kujera.
******
Hajiya BabbaKallon palon nata takeyi cikin tsananin mamaki da abun al'ajabi, ta ce "Ooo ni Allah me laɗifa takezon zamane!" Ta faɗa a ranta ganin abun da take yi. Ma'aikatan da ke sunkuye a cikin palorn da basu san da shigowar hajiyan ba suna nan a yanda ta shigo ta samesu. Da ƙarfi ta ƙwaɗawa laɗifa kira wanda yasa ma'aikatan ɗagowa daga sunkuyan da suke suka kalleta, nan take suka fara mata barka da dawowa. Daidai Lokacin laɗifa tana sauƙowa daga sama waya kare a kunnanta alamar waya takeyi.
Hajiya ta nuna gurin da ƴan aiki suke ta ce "Lafiya kuwa naga waɗannan a haka?" Cikin wani ihuu da tsan-tsar farin ciki tanufi uwar tata tana cewa "Oyoyo Hajiya Allah inace ba yau zakidawo ba duk na zaci wasa kikemin. Kafin Hajiya Babba tayi magana ta ce da ƴan aikin subar palorn yanzu nan kafin ta ƙirga uku. Haka kuwa suka shiga rige-rigen barin gurin cikin sauri. Hajiya ta dawo da kallonta zuwaga laɗifa ta ce "Me ya faru zaki sakasu irin wannan aikin? Ta ce "Wallhi Hajiya ƴan aikin nann duk ƴan raininn wayone, wai saboda bana gida sai kowacce ta ci wanka suka zauna suna hirarr wai kowacce son yaya Salis sukeyi harda shawarin yanda zasu mallakeshi, cikin mamaki Hajiya ta tsayar da su tana kallonsu kowacce tayi tsuru-tsuru ta ce "Wato kuna shawarin yanda zaku mallake min yaro ko? Kuna matsayin ƴan aiki amma kun iya tunanin cutar da ɗan gidako? To dan uwar kowacce daga cikin ku kuhaɗa kayanku duk na sallameku ƴan iska kawai. Hajiya ta ƙarasa maganar tana nuna musu hanyar waje. Yayinda kallo ɗaya zaka mata kagane tana cikin fushine.
Nan fa ƴan aikin kowacce ta shiga bada haƙuri a kan cewar Walhi Rabi ce ta zigasu( Rabi itace babbar ƴar aikin gidan) Hajaya da Laɗifa basu tsaya bin ta kansuba suka koresu. Yayinda laɗifa ta kira Iro mai gadi cikin isa da cewar ita ɗin itace ta ce "Walhi Iro idan har kabari yarannan suka ƙara shigowa gidannan to kaima a bakin aikinka.tana faɗa ta bar gurin. Shikuwa iro sanin cewar itace matar gidan yasa ya rufe gidan yana cewar in Sha Allah bazasu shigoba.
Laɗifa na shiga palor ta tararr da Hajiya na waya, amma tana zuwa ta kashe. "Tashi mutafu? Hajiya ta faɗa tana nufar ƙofar waje.
Laɗifa ta ce "Haba Hajiya ko hutawa bakiyiba? "Laɗifa bakida hankali bakisan waye wannan mutumin ba, Walhi zai iya kashe mutum mutuƙar ba addininsu ɗayaba, barinma ace mudulmine.
Laɗifa ta zaro ido waje ta ce "Wai Hajiya meyasa baya son musilmai ne? Kuma naga Daddy mudulmine?
"Cikin ɓacin rai ta ce "Shiga mota muje, wannan labarin bai shafekiba. Haka suka shiga mota laɗifa dai sai tunanin wannan lamarin takeyi. Batayi auneba sai ganin su tayi agidan su Samuel. Ta ce "Hajiya kekuma zamuyi anann? Hajiya ta ce "Walhi yau za'ayi ta taƙare fito mutafi. Tafaɗa dai-dai tayi fakin a bakin get ɗin ta waje, domin tasan bazata iya shiga gidan ba.
******
GIDAN SOJA
Umar ne zaune tare da wasu daga cikin abokan Daniyel mutum biyu wanda suka haɗa komai tare a kan sune zasu kawo kuɗin. Umar yayi wata irin shigar da bakowane zai iya ganeshiba, domin kuwa ɗinkin babbar riga yasha ga hula sai sheƙi ya keyi. Ɗaya daga cikin abokan Daniyel ɗinne ya ce "Sorry sir Samuel ba aron kuɗi ya bamuba kuma mu bawai munsan me yayi da ƙuɗin bane, kawai munji labarin abunda ya farune yasa muka haɗa kuɗi domin a sakeshi. Tabbas da kana kusa da Umar da sai kaji yanda cikin sa ke murɗawa, domin kuwa Daddy ya zuba masa ido kamar shine mai yin maganar, kokuma mai son gano wani abu.

KAMU SEDANG MEMBACA
Addidinmu Labarine da yashafi kowa da kowa. Labari Mai Fuska Uku, Labarin ADM
AksiThi book is a Normal book. Ya kasance ɗaya tamkar da ɗari. Labari mai fuska 3