HS 04

169 26 3
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na hud'u

K'ok'arin b'oye damuwarta tayi ta hanyar aro far'a da murmushi ta d'aura kan fuskarta sam bata son mahaifiyarta ta fuskanci wani abu, har ya sosa ranta,

Cikin sanyin murya tayi sallama tana tura k'ofar falon k'asa na b'angaren UMMA, Farha da gudu rungumeta, "Yaya Shatu ashe zaki zo, d'azu nacewa Umma a kaini gidan ki, tace ba zani ba", Murmushi tayi tana kama hannun Farha zuwa cikin falon, A zuciyarta ta ayyana ban da yarinta irin na Farha zuwa yanzu ya kamata ta fuskanci Umman ba zata tab'a bari taje gidan ba, tsawon shekaru hud'u da aurenta daga Umma har k'annenta babu wanda ya tab'a tako k'afa gidan ta, Sai dai ita tazo, Ta rasa dalilin Umman na yin haka wanda kowa ya shaideta da hak'uri had'i da kawaici, duk abunda zai sa tayi haka ba k'arami bane,

Umman na zaune k'asan carpet tana had'a atamfofin ta na siyarwa, Teema (itace babbar yarinyar da ta haifa a gidan Alhaji Inuwa) na gefe tana taya ta, "Umma ina wuni?", "Lafiya Lau Shatu" Ta amsa tana dubanta dan son tabbatar da babu wata damuwa a tare da ita, Tsakanin uwa da ya' sai Allah duk k'okarin ta na b'oyewa Umma ta hango zallar damuwa shimfid'e cikin k'wayar idon ta, Sai dai bata nuna ba sai kallonta da ta mayar kan atamfofin gabanta, K'assn zuciyarta tana jin wani yanayi na rashin dad'i, Bata da damuwa da ta wuce na SHATU kullum addu'arta Allah ya kawo sauyi a rayuwar ta, Tana matuk'ar bata tausayi a k'ananun shekarunta ta soma cin karo da k'alubale na rayuwar aure, Ta samu duk wata soyayya da kulawar miji amma ta rasa soyayyar ahalin sa akan wani laifi da ba nata ba,

"Teema ba magana" Cewar Shatu tana dubanta, "Kiyi hak'uri Yaya lissafi ne ya d'auke mun hankali", Murmushi tayi tace "Kema Umma ta koya miki kasuwanci"," "Ai shine mutuncin ka rik'e sana'a, kema nayi ta fama dake ki fara kin saka shiririta, komai kud'in gidan ku ko mijin ka gara kana sana'ar sai kaga kayi wasu hidinmimo ba tare da ka jira a baka ba", Umma ta fad'a, Shatu tace "In shaa Allah zan fara ba da jimawa", "Allah ya yarda yayi miki jagora", Ta amsa da "Amin",

"Yaya ni nayi first position wannan term d'in ma" Farha ta fad'a cikin murna, "Mashaa Allah K'anwata ba dai hazak'a ba", Dariya tayi cikin murna tace "Amma Khairy itace second to the last position, Hajiya ta mata dukan tsiya tace bata san ciwon kanta ba ta bari na wuce ta wai kar ta k'ara bari na fita", SHATU numfashi taja tace "Allah ya bata k'ok'ari itama", "Ita bata concentrating ne a class sai wasa da bacci, watarana ma tak'i zuwa school", "Je ki d'auko mun ruwa a fridge" Ta fad'a dan kawar da zancen, Ko ba'a fad'a ba tasan hassada ce ta saka Hajiya dukan Khairy yadda take son yaranta yana da matuk'ar wuya ta dake su, Ita dai tun tashin ta bata tab'a ganin mai irin halin Hajiya ba wacce k'yashi, hassada da bak'in ciki ya mata yawa,

Shatu ta jima wurin mahaifiyar nata suna hira cikin raha da k'annenta, Sam bata d'auko mata zancen alak'arta dasu Hajiya ba, bata son jin abunda zai hana mata bacci da natsuwar zuciya, SHATU tun aurenta bata tab'a kawowa Umma complain na komai ba, Tun kafin auren ta sanar da ita duk abunda yaje ya dawo bata son jin komai, Dan ita kanta bata so auren ba ganin k'iyayyar HAJIYA gare su tana gujewar yar' ta shiga uk'uba, sai dai ganin yadda Shatu ta nuna tsantsar k'aunar MU'AZZAM da kuma nagartar sa had'i da girma uwa uba k'imar Alhaji yasa ta bada goyon baya da sharad'in bata son jin komai da ya shafi rayuwar auren nasu matuk'ar ba alkhairi ba ne,

Wayarta dake hannun Farha ta mik'o mata tace "Yaya yana kira", Karb'a tayi ta danna receive, "Zan shigo gaishe da Umma sai mu wuce gida", Tace "Tohm" Ta kashe wayar, "Umma wai zai shigo", Duk da kasancewar Mu'azzam tamkar da' a wurinta matsayinsa na dan' mijinta hakan bai hana mata jin nauyin sa ba na surukin ta, Tun kan auren sa da Shatu dama ba wata sakewa ce tsakanin su ba, Gaisuwa ce daga ita ba k'ari,

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now