HS 46

118 19 2
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na Arba'in da Shida

Bashar ba k'aramin farin ciki yayi ba jin cewar Mu'azzam yace ya same sa, Yana jin sun soma hawa matakin farko na nasara, Ya kira Kawu Kabiru ya sanar dashi yadda aka yi, Ya nuna jin dad'in sa tare da tsara masa kalaman da zai yi amfani dasu wurin sake jawo ra'ayin shi, Bashar ya amsa da gamsuwa, kana ya shiga, Yusrah ya kalle dake gefen sa ta soma bacci tun dawowarta kanta ke ciwo, Sigari yaji yana son sha dan yau sam bai samu keb'ewa yasha ba, Mukullin motar sa ya d'auka yayi ajiyar kwali d'aya a bonnet na motar saboda uzuri irin wannan, D'auka yayi ya dawo ciki ya shige d'akin sa ya saka key, ya shiga band'aki guda biyu yasha ya jefa cikin masai yayi flushing, Yayi brush tare da kunna room freshner ya fito, Har ya koma d'akin Yusrah bacci take, shima kwanciya yayi tare da jawota jikin sa.

**************************

Umma tun rasuwar Alhaji kullum sai ta kai sadakar ruwa masallacin unguwar da niyyar Allah ya kai lada kabarin sa, haka tasa a gina masallaci shima da niyyar kai lada kabarin sa, Kullum addu'ar gafarar ubangiji take rok'o masa kuma tana sa su Teema su masa addu'a, Shiyasa ake so ka auri mace ta gari, ko bayan ran ka zaka bar mai maka addua a doron k'asa, haka yaran ka zasu samu tarbiya,

Yau ma buhun shinkafa da na sugar ta siya, ta rabawa ma'aikatan gidan har masu aikin Hajiya Hafsatu tace suyi wa Alhaji addu'a, A ganinta ta haka zata saka mishi irin alkhairin da ya rik'a mata, haka dukiyar da ya bari ta kud'urta nema masa da kanta aljanna dasu, yadda ya tafi ya barsu itama haka zata tafi, ba zata bari rud'in duniya yaja ta, Ma'aikatan Hajiya Hafsatu taji suna hira a kitchen, D'aya tace "Umma ba dai kyauta ba wallahi, ku duba tun bayan rasuwar Alhaji take k'ok'arin abubuwan da zasu kai masa lada kabari". Luba tace "Har masallaci take kai motar ruwa kullum haka ta siya butoci na alwala dasu qur'ani". "kai Allah ya biyata da aljanna shima Alhaji Allah ya jikan shi". "Toh munafukai ina jin ku, baku da aiki sai tsegumi". Tsit sukayi kowacce tasha jinin jikinta, sun san irin tsanar da Hajiya ke ma Umma akan haka sai ta kore su, "Idan na sake jin wata na maganarta a gidan nan wallahi bakin aikin ku, munafukan banza kawai". Ta wuce tana mita, Kowacce taja baki tayi shiru tana cigaba da aikin gaban ta,

Bata zarce ko'ina ba sai b'angaren Umma, kamar kullum counter na hannnun ta tana lazimi tana kallon tashar saudi yayin da take jin shauk'in zuwa umrah, Hajiya Hafsatu ta fad'o falon babu sallama, "Tsohuwar munafuka, Alhaji ya rasu amma baki daina makirci, har ma'aikatan gidan da nawa sai kin siye, wai ke ace miki ta kirki, duk wasu sadaka da kike na sani na makirci ne bayan ke kika kashe Alhajin dan ki mallake dukiya". "Ke Hafsatu tsawon shekaru ina shanye duk wani cin kashin ki da wulak'ancin ki ba wai tsoro bane sai neman zaman lafiya, daga yau na zama na k'arshe da zaki k'ara jefa ta da kalmar kisan Alhaji idan ba haka ba kotu zata rabamu wallahi". HAJIYA Hafsatu da mamaki galala take kallon Umma bata tab'a zaton tana da baki haka ba, Kai ta jinjina tace "Mu zuba ni dake". Ta fice sam bata so maganar ta kai kotu dan bata da wasu hujjoji na cewar ita tayi kisan, tasan kuma sha'anin kotu sai abun ya juye kanta, Ta fice tana kumfar baki, Umma hankalinta ta mayar kan tv, ta kai matakin da ba zata iya cigaba da jure cin kashin Hajiya Hafsatu ba.

*********************

Bashar fuska sake cike da k'arfin gwiwa yayi knocking k'ofar ofishin Mu'azzam, Ya masa iso, Yana gyara zaman sa, Bashar ya shigo ya basa hannu suka gaisa ya zauna, Mu'azzam ya numfasa yace "Naji sak'on ka". "Sak'o na kuma, ai ban aikowa kowa wurin ka ba". "To ai ni kuma bance sak'on ya dangance aiko wani wuri na ba, meyasa kayi saurin tunanin haka". Ya fad'a yana kafe sa da kallo, Son daburce yayi ya dake da cewa "To ai idan kaji ance sak'o yana nufin kayi aike". Mu'azzam guntun murmushi yayi yace "Meyasa baka sameni ka sanar dani matsalar da kake fuskata sai ta hanyar Yusrah". Bashar murmushi yayi yace "Nasan abubuwa sun maka yawa ba zan so k'ara maka da nawa ba, kuma Yusrah na sanar da ita ne a matsayinta na matata bansan zata same ka da maganar". Mu'azzan yaja nunfashi yace "Me kake gani ya kawo maka durk'ushewar kasuwancin da yanzu baka samun customers". "Gaskiya bazan ce ba, daidai gwargwado ina k'ok'ari kuma ina kawo kaya masu kyau sai dai ba'a siya". Mu'azzam ya jinjina kai yace "Abu na farko da zan baka shawara shine ka rik'e addu'a, kayi dogaro da Allah kasa a ranka shi ke badawa kuma shi ke hanawa, kada ka duba na sama da kai a kullum ka rik'a duba na k'asan ka, zan maka hanyar da zaka rik'a order kaya masu kyau daga china wanda ake samun alkhairi dasu sosai, kuma zan had'aka da wasu manyan yan' kasuwa wanda zaka ji dad'in mu'amala dasu". Bashar ransa yaji ya b'aci ko kad'an ba haka ya zata ba, A zahiri yace "Amma me zai hana ko sau d'aya ne muyi tare, daga baya sai ka ware mun nawa ka d'aura ni hanya, kaga idan mukayi tare zan k'ara samun experience". "Bana business na had'aka". Ya fad'a in a serious tone, "Ko meyasa?". "Tsarina ne haka". Bashar tamkar ya tashi ya zabgawa Mu'azzam mari tsabar takaici, A zahiri yace "Toh nagode". Mu'azzam yace "Ba damuwa, ka shirya na had'a ka dasu d'in". "Idan wasu kud'i na suka shigo will let you know". "Alright" Cewar Mu'azzam yana komawa kan aikin gaban sa, Bashar ya fita cikin takaici kai tsaye ya nufi wurin Kawu Kabiru.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now