HS 39

94 14 1
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad

LITTAFIN GABA D'AYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na talatin da tara

Juyi take kan gado, idonta runtse tana jiran bacci ya d'auke ta, sai dai sam babu alamar sa, baccin ta ya zama ragagge a kwanakin, bata san haka zafi, ciwo da rad'ad'in rabuwa da masoyi yake ba, sai a yanzu da ta rasa MU'AZZAM cikin duniyar ta, Tabbas so cuta ne kuma mugun dafi mai wahalar da zuci, kamar yadda zuciyata ke azabtuwa da soyayyar Mu'azzam, kwanaki tayi ba tare da taji muryar sa ko tozali da shi amma ji take tamkar shekaru sun shud'e, Kullum safiya da fatan cire soyayyar sa a ranta sai dai abun yaci tura, Wayarta ta jawo k'ark'ashin pillow ta duba lokaci uku da mintuna na dare, Tashi tayi zaune ta soma addu'o'i kasancewar bata sallah, Ta jima tana yi kafin bacci ya soma fisgarta abun ku da shaid'an.

*****************************

Kowane dare ya mayar dashi wurin raya sa da bautawa Allah ta hanyar k'iyamul laili yana kai masa matsalolin sa wanda yayi imani ta hanyar sa zai samu sauk'i da warwarewar lamuran sa, Ya d'auki awa yana salloli kana ya sallame da yin addu'o'i, Yabi lafiyar gado tare da saita alarm 5:40 ya tashi sallar asuba, Idon sa ya runtse cikin ikon Allah bacci ya d'auke sa ba tare da ya tsaya dogon tunani ba.

******************************

7:30 daidai na safe k'arar wayarta ya tashe ta, ta mutsittsika ido ta jawo wayar, Ganin masoyin nata ne Farouq yasa ta d'auka, "Hello Babe". Yayi maganar yana jan numfashi, "Lafiya naji muryarka wani iri". "Ciwon ciki ke damuna, ina ga ajalina yazo". "Ka daina magana irin haka pls, ciwo ai ba mutuwa ba". "Ni kad'ai nasan azabar da nake ciki". Ya fad'a da k'yar yana sake jan wani dogon numfashi, "Ka tashi kaje asibiti". "Da wane kud'i babe, kinsan bani da ko sisi". "Ina da kud'i wanda Mama ta bani na shirye shiryen biki, ka tura account number na saka maka". "Shiyasa nake son ki babe, ke kad'ai kike magance mun damuwata". "Ni dai fatana ka samu lafiya". "I love you". Ya fad'a a marairace, Tace "I love you too, ka turo mun". Ta kashe wayar, Farouq dariya ya bushe da ita, Cikin hanzari ya tura mata account number, Ba'a fi minti goma ba ta tura masa dubu hamsin, Yana ganin alert yace "Ke Ina sonki ko dan yadda kike cika mun aljihu". Ya mik'e ya fad'a band'aki yin wanka.

****************************

Shatu sai da rana da fito, kana ta fito falo, Saratu da Jummai ta gani a falo suna kallo, IYA ta d'auke musu zuwa talla dama tsabar son kud'i yake sawa take d'aura musu, "Ina kwana?". Suka gaisheta a tare, "Lafiya lau, ina IYA?". "Tana d'aki". Hanyar d'akin IYA ta nufa, sallama kusan uku tayi ba'a amsa ba, IYA naji tayi shiru bata son shigowar SHATU, hakan yasa tayi shiru tamkar bacci take, Jin shiru SHATU ta juya ta koma falo, Ta zauna tare dasu Saratu dan ragewa kanta damuwa, wnada suke jan ta hira, tana biye musu.

*************************

Mu'azzam sosai yake gudanar da kasuwanci har yafi lokacin da Alhaji na raye, haka riba bata wasa yake samu ba, Yau ma tun shigar sa kasuwa yake k'ok'arin order wasu kaya, Sam ya daina sakewa kowa, haka harkar kasuwancin baya shawara da kowa sai yaron sa d'aya Haruna, wanda tun Alhaji na raye shima ya yarda da yaron sosai,

Kawu Kabiru abun ya soma damun su, Yau ya samu su Rabi'u da maganar,

"Kuna ganin yadda ake shige da fice da kaya plaza nan ba tare da sanin mu ba, ko shawara damu". Lamido yace "Ni kaina mamakin yaron nan yake, yaushe aka haife sa da zai nuna mana k'warewa". Rabi'u ya nisa da cewa "Munyi sake da yawa wallahi". Kawu Kabiru ya jinjina kai yace "Ya zama dole mu sake shiri ta hanyar da' na masa tarko mai wuyar fita". Lamido da Rabi'u suka ce "K'warai". "A yadda naga kansa na rawa dole mu nuna masa yaro yaro ne bai isa ja da babba ba". Rabi'u yace "D'azu naji ana cewa sabon kaya zasu shigo kuma zasu samu karb'uwa sosai". lamido yace "Matuk'ar muka bari suka zo fad'uwa ne gare mu, ku duba yadda yanzu kwata kwata kayan mu sun rage tafiya sai wanda Mu'azzam ya kawo ake so, hatta manyan yan' kasuwar nan nashi suke d'auka". "ku bar komai hannu na" Cewar Kawu Kabiru yana cizon labb'an k'asa.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now