22

84 19 1
                                    

HALACCIN SO
NA ZEE YABOUR

ZEEYABOUR on wattpad
@HWA

*Free novel ne bana kud'i ba*

LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA
NANA FIDDAUSI MUHAMMAD SURAJO

Shafi na ashirin da biyu

Afuwan kun jini shiru tsawon kwanaki nayi tafiya ne ban samu natsuwar typing ba, amma yanzu In shaa Allah zaku cigaba da samun update

Cikin kulawa da soyayya Mu'azzam ya kama Shatu zuwa cikin asibitin, Har kunya yaso bata ganin irin rik'on da ya mata, daidai reception wanda ke d'auke da mutane tsirakun masu ganin likita, tayi k'ok'arin zame hannun ta, Kallon ta yayi ta masa alamar akwai mutane, Basarwa yayi tankar bai gane me take nufi ba, ya sake ma hannun nata kyakkyawan rik'o, Babu jan lokaci suka samu ganin k'wararren likita wato Dr Muhriz wanda ya gwanance kan aikin sa, Allah ya bashi baiwar iya kula da lafiya, Hannu Mu'azzan ya bashi suka gaisa cikin mutun ta juna, Suka zauna kan kujeru biyu masu kallon Dr, Mu'azzam ya masa bayanin dukkan abunda Shatu ke ji, Dr Muhriz ya jinjina kai tare da yin murmushi wanda murmushin nasa ya saka Mu'azzam jin wani sanyi a ransa, Da alama lokaci yazo da zai fara amsa sunan Baba, lokaci yayi da Shatu zata huta da gorin haihuwa, lokaci yayi da zai daina ganin hawaye kan fuskar ta, Nurse d'aya ya kira, Yace ta d'ibi jinin Shatu aje a mata test kala uku hadda na ciki,

SHATU tunda Nurse ta d'ibi jinin ta ta fita, zuciyarta ke faman dukawa sam ta kasa samun natsuwa, farin ciki da walwala data hango kan fuskar Mu'azzam tana fatan ta dawwama har abada, bata fatan ta yanke, Hakan yasa ta k'ara kwad'aituwa da son ace cikin take d'auke dashi,

Mintuna talatin da biyar ya d'auke Nurse d'in ta dawo da sakamakon test d'in ta mik'awa DR MUHRIZ cikin ladabi, Ya amsa yana d'aukar tsadadden medical glass d'insa cikin case ya goge ya saka, Mu'azzam da Shatu hankalinsu duka suka tattara kan sa,

"Test d'in ya nuna tana da malaria sai kuma peptic ulcer wacce ita ke sata tashin zuciya, jiri da kuma amai", Dr Muhriz ya fad'a, Shatu kallonta ta kai kan Mu'azzam ba abunda take ji kamar shi, idan itace mai sauk'i ne damuwar sa na matuk'ar d'aga hankalinta da jefata rashin natsuwar zuci, Idon su ya sark'e cikin na juna shima yanayin nata yake son gani, baya k'aunar ganin damuwa a tare da ita, Kowane murmushi ya sakarwa d'aya sai da hakan bai hanawa junansu hango damuwa tare da d'aya, Dr Muhriz ya katse su da cewa "Za'a mata treatment na malaria sosai dan ta mata kamu sosai, haka ulcer ta kiyaye cin abinci kuma ta rage shan yaji", Mu'azzam yayi nodding kai, gaba d'aya jikinsa ya sanyaye sam baya jin k'arfi sai sarewa a tare dashi, "Anya kuwa suna da rabon ganin jinin su a duniya" Zuciyar sa tayi saurin kwab'ar sa da nuna masa Bawa baya saurin cire rai ga rahamar ubangiji haka wani jinkirin alkhairi ne "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faqeer" Ya soma fad'a, Shatu ta rasa meke mata dad'i itama sarewa da karaya take ji a tare da ita sai dai bata fasa ambaton Allah ba,

Dr Muhriz ya rubuta musu allurai da maganganu, suka siya a pharmacy na asibitin, Aka mata allura da cewar zasu dawo sai anyi na kwana uku.

*******************************

Shiru ne ya ratsa motar na wasu mintuna sai sautin karatun qur'ani dake tashi, Hannun sa taji cikin nata, bata kalle sa ba idonta na kan titi, Murzawa yayi a hankali cikin murya mai sigar lallashi yace "Kada hakan ya dame ki ko yasa ki karaya, Allah yana sane damu In shaa Allahu zai bamu yara nagari a lokaci mafi dacewa", Kallon ta ta mayar kansa tace "Har kullum damuwar ka na sama da tawa, haka damuwata mai sauk'i ce a kan taka, babu abunda ke d'aga mun hankali kamar damuwar ka, farin cikin ka shine nawa Yaya Mu'azzam, ka daina tunanin hakan zai zama damuwa gareni matuk'ar bai zama gare ka ba", Hannun sa ya janye ya maida ta bayanta ya kwanto da ita kan kafad'ar sa, "Ba k'aramin dace nayi ba da samun mace ta gari irin ki, Allah ya barmu tare", "Kamar yadda nayi dacen da samun miji nagari irin ka", Shafa bayanta yayi a hankali, Yana cigaba da tuk'i da hannu d'aya.

HALACCIN SO(COMPLETED)✅Where stories live. Discover now